Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/15 pp. 13-17
  • Da Yake Ka “San Allah,” Me Ya Rage Yanzu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Da Yake Ka “San Allah,” Me Ya Rage Yanzu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MATAKAN DA MUKA ƊAUKA DON MU SAN ALLAH
  • WAƊANDA ALLAH YA SANI SUNA BUKATAR CI GABA
  • KA ƘARFAFA DANGANTAKARKA DA ALLAH
  • KANA BUKATAR JIMIRI DON KA KUSACI JEHOBAH
  • Matasa Ku Ci Gaba da Samun Ci Gaba Bayan Kun Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Yadda Za Ka Shirya Kanka don Yin Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • ‘Ku Tafi Fa, Ku Almajirtar, Kuna Yi Musu Baftisma’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/15 pp. 13-17

Da Yake Ka “San Allah,” Me Ya Rage Yanzu?

“Kun san Allah.”—GAL. 4:9.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa yake da kyau mu riƙa bincika matakan da muka ɗauka kafin mu yi baftisma?

  • Ko da mun riga mun manyanta, me ya sa yake da kyau mu riƙa samun ci gaba?

  • Me ya sa ya kamata mu riƙa yin tunani game da imaninmu da kuma keɓe kanmu?

1. Me ya sa ake bukatar matuƙin jirgin sama ya bincika jirgin kafin ya tashi?

A DUK lokacin da matuƙin jirgin sama yake son ya tashi, yana bincika jirgin sosai. Yana yin amfani da wata takarda don ya tabbata cewa ya bincika kome kafin ya tashi. Idan bai bincika jirgin ba, ba zai iya lura da wata matsalar da za ta iya jawo hatsari ba. Amma, ka san irin matuƙin jirgin da ainihi ake son ya cika wannan takardar a kowane lokaci? Wanda ya ƙware ne sosai. Matuƙin jirgin da ya ƙware sosai zai iya kasance da yawan gaba gaɗi, kuma ya ƙi bincika jirgin kafin ya tashi.

2. Mene ne muke bukatar mu bincika?

2 Kamar matuƙin jirgin sama, akwai binciken da ya kamata ka yi don ka tabbata cewa ba za ka daina bauta wa Jehobah a lokatai masu wuya. Kana bukatar ka ci gaba da bincika imaninka, ko da ka daɗe kana bauta wa Jehobah ko a’a. Idan muka ƙi yin hakan, wata matsala mai tsanani za ta iya sa mu ɓata dangantakarmu da Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa: “Domin wannan fa, wanda ya ke maida kansa yana tsaye, shi yi lura kada ya fāɗi.”—1 Kor. 10:12.

3. Mene ne Kiristoci da ke Galatiya suke bukatar su yi?

3 Hadayar fansa ta Yesu ta sa ya yiwu Kiristoci su koyi wani sabon abu game da Allah. Wato, za su iya zama ’ya’yan Allah! Amma, Kiristoci da ke Galatiya suna bukatar su ci gaba da bincika imaninsu. (Gal. 4:9) Wasu a cikin ikilisiyar sun nace cewa sai Kiristoci sun bi dokar da aka bayar ta hannun Musa ne Allah zai amince da su. Amma, Allah ya daina yin amfani da wannan dokar kuma ’yan Al’umma ba su taɓa bin dokar ba. Yahudawa da kuma ’yan Al’umma da ke cikin ikilisiyar suna bukatar su daɗa koyon gaskiya. Suna bukatar su san cewa Allah ba ya son mutane su bi dokar da ya bayar ta hannun Musa ba.

MATAKAN DA MUKA ƊAUKA DON MU SAN ALLAH

4, 5. Wane gargaɗi ne Bulus ya yi wa Galatiyawa, kuma yaya hakan yake da amfani a gare mu?

4 Wasiƙar da Allah ya hure manzo Bulus ya rubuta wa Galatiyawa tana tuna wa dukan Kiristoci cewa ba zai dace su yi watsi da gaskiyar da suka koya daga cikin Littafi Mai Tsarki ba. Bai kamata su koma gidan jiya ba. Wannan wasiƙar za ta iya ƙarfafa dukanmu mu kasance da aminci ga Jehobah.

5 Dukanmu na bukatar mu tuna sa’ad da muka zaɓa mu bauta wa Jehobah. Kuma, waɗannan tambayoyi biyu za su taimaka mana mu yi hakan: Ka tuna da matakan da ka ɗauka don ka cancanci yin baftisma? Ka tuna da yadda ka ji sa’ad da ka san Allah kuma shi ma ya san ka?

6. Waɗanne jerin abubuwa ne za mu koya game da su?

6 Akwai matakai guda tara da dukanmu muka ɗauka don mu bauta wa Allah. Waɗannan matakan na cikin akwatin nan “Matakan da Ka Ɗauka Kafin Baftisma Za Su Sa Ka Samu Ci Gaba.” Suna kama da jerin abubuwa da muke bukatar mu riƙa bincikawa don mu ƙarfafa imaninmu kuma kada mu koma gidan jiya. Kamar yadda matuƙin jirgin sama yake bukatar ya bincika jirgin kafin ya tashi, mu ma ya kamata mu ci gaba da bincika waɗannan abubuwan.

WAƊANDA ALLAH YA SANI SUNA BUKATAR CI GABA

7. Wane tafarki ne ya kamata mu bi, kuma me ya sa?

7 Kamar yadda matuƙin jirgin sama ke bukatar ya yi bincike duk sa’ad da zai tashi, mu ma muna iya bincika ci gabar da muke yi tun bayan da muka yi baftisma. Manzo Bulus ya ce wa Timotawus: “Ka kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi waɗanda ka ji daga gareni, cikin bangaskiya da ƙauna wadda ke cikin Kristi Yesu.” (2 Tim. 1:13) Waɗannan “sahihiyan kalmomi” suna cikin Kalmar Allah. (1 Tim. 6:3) Kamar yadda zanen gida zai iya sa mu san yadda ainihin ginin zai zama, haka nan ma “sahihiyan kalmomi” suna taimaka mana mu fahimci dukan abin da Jehobah yake son mu yi. Yanzu, bari mu tattauna matakan da muka ɗauka kafin mu yi baftisma, don mu ga ko har ila muna bin tafarkin koyarwa ta gaskiya da kyau.

8, 9. (a) Me ya sa za mu riƙa inganta iliminmu da imaninmu? (b) Me ya sa aka kwatanta ci gabanmu da yadda itace yake girma, kuma yaya hakan yake da muhimmanci?

8 Mataki na farko da muka ɗauka shi ne koyon gaskiya, kuma hakan ya sa muka yi imani da Allah. Amma muna bukatar mu ci gaba da koyon gaskiya da kuma ƙarfafa imaninmu. (2 Tas. 1:3) Muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah bayan mun yi baftisma.

9 Wannan ci gaba yana kama da yadda itace ke yin girma. Itace yakan yi girma sosai idan jijiyoyinsa sun riƙe ƙasa kuma suka yi ƙarfi sosai. Alal misali, wasu itatuwan Lebanon suna iya girma sosai, har su kai tsawon bene mai hawa goma sha biyu. Kuma sai an yi amfani da igiya mai tsawon kafa 40 kafin a kewaya guda. (W. Waƙ. 5:15) Itace yana girma da sauri sa’ad da aka shuka shi. Sa’ad da jijiyoyin suke shiga ƙasa kuma suke faɗaɗawa, sai itacen ya ƙara tsayi da kuma ƙauri. Amma, bayan shekaru da yawa, zai yi wuya a lura da yadda itacen yake girma. Hakan ya yi daidai da yadda Kiristoci suke samun ci gaba. Sa’ad da ake yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mu, muna iya yin canje-canje a salon rayuwarmu nan da nan kuma bayan hakan mu yi baftisma. Kuma hakan yana sa ’yan’uwa a cikin ikilisiya farin ciki. Muna iya zama majagaba ko kuma mu sami wani gata a cikin ikilisiya. Bayan hakan, ba za a iya lura da dukan ci gaba da muke yi kuma ba. Amma, muna bukatar mu ci gaba da inganta imani da kuma sanin gaskiya da muke da shi, har sai mun zama “cikakken mutum,” wato Kirista da ya manyanta. (Afis. 4:13) Saboda haka, idan muna samun ci gaba a matsayin Kiristoci, muna kama da ɗan tsiro da ya zama itace mai girma.

10. Me ya sa Kiristoci da suka manyanta ma suke bukatar su samu ci gaba?

10 Amma, bai kamata ci gabanmu ya tsaya a nan ba. Kamar jijiyoyin itace, iliminmu da imaninmu suna bukatar su yi zurfi da kuma ƙarfi, kuma su ci gaba da yin hakan. (Mis. 12:3) Akwai ’yan’uwa da yawa da suke samun irin wannan ci gaba. Wani ɗan’uwa da dattijo ne fiye da shekara 30 yanzu da har ila yana kan samun ci gaba, ya ce: “Yanzu ina ɗaukan Littafi Mai Tsarki da tamani fiye da dā. Na ci gaba da koyon yadda zan yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don tsai da shawara a hanyoyi dabam-dabam, kuma ina daɗa jin daɗin hidimata.”

KA ƘARFAFA DANGANTAKARKA DA ALLAH

11. Ta yaya za mu ci gaba da kyautata abokantakarmu da Jehobah?

11 Idan muna son mu ci gaba da manyanta a matsayin Kiristoci, wajibi ne mu riƙa kusantar Jehobah. Yana so mu san cewa yana ƙaunarmu kuma zai kāre mu a matsayin Abokinmu da kuma Ubanmu. Hakan zai sa mu ji kamar jariri a hannun iyayensa ko kuma yadda muke ji sa’ad da muke tare da amininmu. Ba zai yiwu mu kasance da dangantaka na kud da kud da Jehobah dare ɗaya ba. Muna bukatar lokaci da kuma ƙoƙari sosai don yin hakan. Saboda haka, ka tabbata ka keɓe lokaci don karatun Littafi Mai Tsarki kullum. Kuma ka karanta kowace fitowar mujalla ko ƙasida ko kuma littafi da ƙungiyar Jehobah ta wallafa. Hakan zai taimaka maka ka san Jehobah kuma ka kyautata abokantakarka da shi.

12. Mene ne muke bukatar mu yi don mu kyautata abokantakarmu da Jehobah?

12 Addu’a da kuma tarayya mai kyau da abokan Allah, zai taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. (Karanta Malakai 3:16.) Jehobah yana ‘jin roƙonmu.’ (1 Bit. 3:12) Jehobah yana kamar uba mai ƙauna domin yana jin addu’o’inmu. Saboda haka, ya kamata mu “lizima cikin addu’a.” (Rom. 12:12) Abokantakarmu da Jehobah za ta yi tsami, idan bai taimaka mana ba. Matsalolin zamanin nan sun fi ƙarfinmu. Idan muka daina yin addu’a ga Jehobah, ba za mu samu ƙarfin jimrewa da su ba. Kana yin addu’a ga Jehobah kamar yadda kake magana da amininka kuwa? Ko kuwa kana bukatar ka kyautata addu’o’inka?—Irm. 16:19.

13. Ta yaya halartar taro zai sa mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah?

13 Jehobah yana farin ciki da waɗanda suke “sa danganarsu gareshi.” Shi ya sa muke bukatar mu ci gaba da yin tarayya da abokansa da ke cikin ikilisiya. (Nah. 1:7) Muna bukatar mu riƙa yin tarayya da ’yan’uwanmu domin wannan duniyar ta lalace. Mene ne amfanin wannan tarayyar? A cikin ikilisiya, za ka samu ’yan’uwa da za su ƙarfafa ka, su taimaka maka ka ƙaunaci mutane kuma ka yi “nagargarun ayyuka.” (Ibran. 10:24, 25) Domin mu bi wannan shawarar, muna bukatar mu ba da lokaci don yin tarayya da kuma cuɗanya a cikin ikilisiya. Ka tabbata kana halartar kowane taro kuma kana yin kalami.

14. Me ya sa muke bukatar mu riƙa yin canje-canje kuma mu tuba idan muka yi kuskure?

14 Sa’ad da muka zama Kiristoci, wajibi ne mu tuba kuma mu yi tir da zunuban da muke yi a dā. Amma, muna bukatar mu kasance a shirye mu tuba kuma mu yi gyara a salon rayuwarmu. Yana da sauƙi mu yi zunubi domin har ila mu ajizai ne. Zunubi yana kamar maciji da ke a shirye ya sare mu idan ya samu dama. (Rom. 3:9, 10; 6:12-14) Shi ya sa bai kamata mu ruɗi kanmu ba cewa ba mu da kasawa. Abin farin ciki ne cewa Jehobah yana haƙuri da mu sa’ad da muke ƙoƙarin shawo kan kasawarmu da kuma yin gyara. (Filib. 2:12; 2 Bit. 3:9) Ka yi amfani da lokacinka da kuma kuzarinka a hidimar Jehobah, maimakon ɓad da su a biɗar abubuwan mallaka. Wata ’yar’uwa ta ce: “Iyayena Shaidu ne, amma sa’ad da na girma, sai na soma ji cewa Jehobah abin tsoro ne kuma ba zai yiwu in faranta ransa ba.” Sai ta soma sanyi a dangantakarta da shi kuma ta yi kurakurai. Ta daɗa: “Ba wai ba na ƙaunar Jehobah ba, amma matsalata ita ce rashin saninsa sosai. Amma, na roƙi Jehobah kuma ya taimaka mini in yi canje-canje. Na lura cewa Jehobah ya bi da ni kamar yaro, ya nuna mini abin da zan yi don in shawo kan matsalolina.”

15. Mene ne Yesu da kuma Jehobah suke lura da shi?

15 Bayan mala’ikan Allah ya fitar da Bitrus da kuma sauran manzanni daga kurkuku, sai ya ce su ci gaba da“faɗa” wa mutane bishara. (A. M. 5:19-21) Idan muna son mu kasance da imani sosai, ya kamata mu bincika ko muna yin wa’azi kowane mako. Yesu da Jehobah suna lura da bangaskiyarmu da kuma ƙoƙarin da muke yi a aikin wa’azi. (R. Yoh. 2:19) Dattijon da aka ambata ɗazun ya ce: “Ya kamata wa’azi ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu.”

16. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tuna cewa mun keɓe kanmu ga Jehobah?

16 Ka riƙa tuna cewa ka keɓe kanka ga Jehobah. Babu abin da muke da shi da ya fi dangantakarmu da Jehobah. Ya san dukan mutanensa. (Karanta Ishaya 44:5.) Ka bincika ka ga ko har ila kana da dangantaka na kud da kud da Jehobah, kuma ka roƙe shi ya taimaka maka ka ci gaba da yin hakan. Ka tuna da baftismarka da kuma ranar da ka yi hakan. Baftismarka ta nuna wa mutane cewa ka keɓe kanka ga Jehobah, kuma wannan ne zaɓi mafi muhimmanci da ka taɓa yi.

KANA BUKATAR JIMIRI DON KA KUSACI JEHOBAH

17. Me ya sa muke bukatar mu jimre idan muna son mu kasance kusa da Jehobah?

17 Bulus ya gaya wa Galatiyawa cewa kada su yi kasala. (Gal. 6:9) Ya kamata Kiristoci a yau ma su ci gaba da jimrewa. Za ka fuskanci matsaloli da yawa, amma Jehobah zai taimake ka. Ka ci gaba da roƙonsa ya ba ka ruhu mai tsarki. Hakan zai sa ka samu kwanciyar rai kuma ka yi farin ciki. (Mat. 7:7-11) Ka yi la’akari da wannan: Idan har Jehobah yana kula da tsuntsaye, me zai hana shi kula da kai da ke ƙaunarsa kuma ka keɓe kanka don yin nufinsa? (Mat. 10:29-31) Ko da kana fuskantar matsaloli, kada ka yi kasala ko kuma ka daina bauta masa. Muna moran albarka da yawa domin Jehobah ya san mu.

18. Da yake ka san Allah yanzu, mene ne ya kamata ka yi?

18 Saboda haka, idan bai daɗe da ka yi baftisma ba, me ya rage yanzu? Ka ci gaba da sanin Jehobah da kyau kuma ka manyanta sosai. Idan ya daɗe da ka yi baftisma kuma fa? Kada ka ji kamar ka gama sanin Allah kuma ba ka bukatar ka kyautata dangantakarka da shi. Maimakon haka, ka riƙa bincika kanka a kai a kai. Hakan zai sa ka ci gaba da kasancewa kusa da Jehobah, wanda shi ne Ubanmu mai ƙauna da Abokinmu da kuma Allahnmu.—Karanta 2 Korintiyawa 13:5, 6.

MATAKAN DA KA ƊAUKA KAFIN BAFTISMA ZA SU SA KA SAMUN CI GABA

  1. Abu na farko da muka yi shi ne koyo game da Jehobah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi.—Yoh. 17:3

  2. Yayin da muka daɗa samun ilimin Littafi Mai Tsarki, sai bangaskiyarmu ta ƙaru.—Yoh. 3:16

  3. Mun yi addu’a ga Jehobah a kai a kai.—A. M. 2:21

  4. Mun soma tarayya da ’yan’uwa a cikin ikilisiya.—Ibran. 10:24, 25

  5. Mun tuba daga zunubanmu.—A. M. 17:30

  6. Mun daina yin munanan ayyuka.—A. M. 3:19

  7. Bangaskiyarmu ta motsa mu mu yi wa’azi.—2 Kor. 4:13

  8. Mun keɓe kanmu ga Jehobah domin mu samu bin Yesu a hanyar da ta dace.—1 Bit. 4:2

  9. Mun nuna cewa mun keɓe kanmu ta wajen yin baftisma.—1 Bit. 3:21

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba