Ka Tsare Kanka Daga Miyagun Ruhohi
AN HAIFI James a can cikin tsibirin Malaita, a Solomon Islands. Tun yana yaro aka koya masa ya dinga ɗaukaka ruhohi. Ya ce: “Ban taɓa roƙon ruhohi su cuci wasu ba, amma ban yi tsammanin cewa zai yiwu mutum ya samu farin ciki ba tare da yin amfani da rarafono [wato, hanyoyin gargajiya da ake amfani da su a nemi taimako daga ruhohi] don tsaro daga lahani.”
Kamar mutane a wurare da yawa a duniya, mutanen Tsibiren Solomon sun gaskata cewa ruhohi suna iya taimaka masu ko kuma su cuce su. Hakika, yawancin Melanesiyawa suna ɗaukan waɗannan ruhohin da ƙauna, ba da tsoro ba.
Ana nuna imani ga ruhohi a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, sa’ad da James yake ƙarami, matan da ke ƙauyensu sukan ruga cikin gida da yaransu a duk lokacin da suka ji kukan wani tsuntsu mai suna korokoro, (wato koel). Me ya sa? Sun gaskata cewa kukan da tsuntsun yake yi alama ce da ke nuna cewa za a yi wa wani lahani.
Wasu ’yan ƙauyen suna ajiye wani farin dutse na musamman a saman ƙofar gidajensu. James ya yi hakan, domin ya yi imani cewa dutsen zai kāre shi daga miyagun ruhohi. Kuma sa’ad da James yake wajen aiki, yana kwashe dukan raguwar abincin da ya ci da rana kuma ya zuba shi a cikin jaka don ya zubar da shi. Dalilin yin hakan shi ne cewa boka zai iya ɗaukan raguwar abincin ya yi amfani da shi don ya yi masa tsafin da zai sa shi rashin lafiya.
Wataƙila irin waɗannan abubuwan ba sa faruwa a inda kuke da zama, amma kamar James, wataƙila ka taɓa jin kana bukatar bin al’adunku don ka sami kāriya daga mugayen ruhohi. Kana iya jin cewa bin waɗannan al’adun zai iya kāre ka daga lahani.
Idan kana daraja Littafi Mai Tsarki, babu shakka, za ka so ka san amsoshin da ya ba da game da tambayoyin da ke gaba: (1) Wane lahani ne miyagun ruhohi za su iya yi maka? (2) Bin wasu al’adu zai iya sa ka faɗa ƙarƙashin ikon aljanu ne? (3) Ta yaya za ka iya samun kāriya ta ainihi don miyagun ruhohi kuma ka yi farin ciki?
Yadda Miyagun Ruhohi Suke Yin Lahani
Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa miyagun ruhohi ba ruhohin matattu ba ne. “Masu-rai sun san za su mutu,” in ji Kalmar Allah, “amma matattu ba su san komi ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Gaskiyar ita ce, miyagun ruhohi su ne mala’ikun da suka yi tawaye tare da Shaiɗan don su yaudari mutane.—Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalla-dalla cewa muna bukatar kāriya domin miyagun ruhohi. Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci a Afisa: “Kokuwarmu ba da nama da jini ta ke ba, amma da . . . rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” Manzo Bitrus ya kwatanta mai mulkin dukan miyagun ruhohi, Shaiɗan Iblis, da “zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.”—Afisawa 6:12; 1 Bitrus 5:8.
Shaiɗan yana jawo lahani ta wajen yaudarar mutane, kuma ya ruɗe su su yi abin da zai ɓata wa Allah rai. Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan “ya kan mayarda kansa kamar mala’ika na haske.” (2 Korinthiyawa 11:14) Yana yin kamar shi ruhu ne da ke taimako, amma, nufinsa shi ne ya yi mugunta. Shaiɗan yana duhuntar da zuciyar mutane don kada su san shi, da kuma gaskiya game da Allah. (2 Korinthiyawa 4:4) Menene ya sa yake yaudarar mutane?
Shaiɗan yana sha’awar bauta kuma yana son mutane da saninsu ko cikin rashin sani su bauta masa. Sa’ad da Ɗan Allah, Yesu, yake duniya, Shaiɗan ya son ya ‘fāɗi, ya yi masa sujada.’ Yesu ya ce: “Rabu da nan, ya Shaiɗan: gama an rubuta, Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka.” (Matta 4:9, 10) Yesu ya ƙi yin duk wani abin da zai nuna cewa yana bauta wa Shaiɗan.
A cikin ruhohi, Jehobah ne mafi iko kuma ba zai bari a yi wa waɗanda suke yi masa biyayya lahani na dindindin ba. (Zabura 83:18; Romawa 16:20) Amma idan muna son mu faranta wa Jehobah Allah rai kamar yadda Yesu ya yi, muna bukatan mu guje wa duk wata hanyar bauta wa Shaiɗan ko aljanunsa. Saboda haka, muna bukatan mu san ayyuka na al’ada da suke sa a bauta wa mugayen ruhohi. Ta yaya za ka iya yin haka?
Ka San Al’adun da Ke Ɓata wa Allah Rai
Jehobah Allah ya yi wa mutanensa na dā, Isra’ilawa, gargaɗi game da yin koyi da al’adun al’ummai da ke kusa da su. Ya ce: “Daga cikinka ba za a iske wanda . . . ya ke yin istihara, ko mai-yin duba, ko mai-waibuwa, ko mai-sihiri.” Ga waɗanda suka bi waɗannan al’adu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya aika waɗannan al’amura duka abin ƙyama ne ga Ubangiji.”—Kubawar Shari’a 18:10-12.
Saboda haka, sa’ad da kake tunani game da al’adun da suka zama sanannu a yankinku, ka yi tunani a kan tambayoyin da ke gaba: Wannan al’adar tana ƙarfafa yin imani da duba? Tana cewa za a sami kāriya daga abubuwa marar rai? Ta ƙunshi yi ko samun kāriya daga sihiri? Za ta ƙunshi miƙa kai ga wani ruhu dabam da ba Jehobah ba ko wakilinsa da ya naɗa, Yesu?—Romawa 14:11; Filibiyawa 2:9, 10.
Yana da muhimmanci ka guje wa duk wata al’adar da ke ƙarfafa yin irin waɗannan ayyukan. Me ya sa? An hure manzo Bulus ya rubuta: “Ba ku da iko ku sha ƙoƙon Ubangiji duk da na aljanu ba.” Ya yi gargaɗi cewa waɗanda suke son su faranta wa Allah rai tare kuma da wasu ruhohi suna sa “Ubangiji shi ji kishi.” (1 Korintiyawa 10:20-22) Jehobah Allah ya bukaci mu bauta wa shi kaɗai kuma ya cancanci hakan.—Fitowa 20:4, 5.
Ka yi la’akari kuma da wannan tambayar: Al’adar tana ɗaukaka ra’ayin cewa mutum ba shi da hakki a kan abubuwan da shi ko ita ta ko ya aikata? Alal misali, a wurare da yawa an ƙi jinin yin kwartanci da kuma jima’i kafin aure, kuma Littafi Mai Tsarki ma ya haramta yin hakan. (1 Korintiyawa 6:9, 10) Amma dai, a wasu al’adu na Pasifik, ana amincewa da irin wannan al’adar idan yarinyar ta yi da’awar cewa an tilasta mata ne ta yi zina domin sihirin da aka yi mata.
Amma, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa, za mu ba da lissafin dukan abubuwan da muka aikata. (Romawa 14:12; Galatiyawa 6:7) Alal misali, mace ta farko, Hauwa’u, ta yi da’awar cewa Shaiɗan ne ya yaudare ta ta karya dokar Allah, tana cewa: “Macijin ya ruɗe ni.” Amma, Jehobah ya sami Hauwa’u da laifi bisa abubuwan da ta yi. (Farawa 3:13, 16, 19) Mu ma za mu ba shi lissafin abin da muka aikata.—Ibraniyawa 4:13.
Menene Ya Kamata Ka Yi?
Idan kana son ka faranta wa Allah rai kuma ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, kana bukatan ka ɗauki mataki yanzu. Masu zukatan kirki da suke zama a Afisa a ƙarni na farko sun kafa misali mai kyau game da wannan batun. Don su raba kansu daga tasirin miyagun ruhohi, sun tattara dukan littattafansu da ke ɗauke da sihiri kuma suka “ƙone su a gaban dukan mutane.”—Ayyukan Manzanni 19:19.
Kafin su ƙona littattafan, waɗannan mutanen “suka zo, suna faɗin laifinsu, suna bayana ayukansu.” (Ayyukan Manzanni 19:18) Abin da Bulus ya koya musu game da Kristi, ya motsa su su ƙona littattafansu na sihiri. Sun kuma canza ra’ayinsu game da al’adunsu.
Hakika, barin al’adu zai iya kasancewa da wuya. James da aka ambata ɗazu, ya fuskanci wannan ƙalubalen. Ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma yana jin daɗin abin da ya koya. Duk da haka, ya ci gaba da yin amfani da rarafono. Sa’ad da yake yin tunani a kan ra’ayinsa game da waɗannan al’adu, ya fahimci cewa ya gaskata da alkawuran Jehobah na nan gaba amma yana ganin cewa don samun kāriya a yanzu, yana bukatan ya dogara da al’adunsu.
Menene ya taimaka wa James ya canza tunaninsa? Ya ce: “Na yi addu’a ga Jehobah don na sami kāriyarsa da kuma taimakonsa don in dogara da shi. A lokacin kuma, na yi watsi da waɗannan batutuwa na al’adu.” Amma da akwai wani lahanin da ya same shi? “A’a,” in ji James. “Abin da ya faru shi ne na koyi na dogara ga Jehobah. Na ga yadda Jehobah zai iya kusantar mutum a matsayin aboki.” Fiye da shekaru bakwai da suka gabata, James yana hidima ta cikakken lokaci, yana taimaka wa mutane su koyi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.
Me ya sa ba za ka bi misalin James ba. Ka bincika al’adun da ake bi a wurin da kake zama, kuma ka yi amfani da ‘inganci tunaninka’ don ganin ko sun jitu da ‘nufin Allah.’ (Romawa 12:1, 2) Kuma ka sami gaba gaɗi don ka rabu da ayyukan sihiri. Idan ka yi hakan, ka tabbata cewa Jehobah zai ‘karɓe ka’ kuma zai kāre ka. (2 Korintiyawa 6:16-18) Kamar James, za ka ga gaskiyar alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki: “Sunan Ubangiji kagara ne mai-ƙarfi: Mai-adalci ya kan gudu ya shiga ciki, shi sami lafiya.”—Misalai 18:10.
[Hotunan da ke shafi na 15]
“Korokoro”
[Crecit Line]
Courtesy of Dr. Bakshi Jehangir
[Hotunan da ke shafi na 15]
Yarinya tana ƙwashe raguwar abinci don kada a yi amfani da shi a yi mata tsafi