Tambayoyi Daga Masu Karatu
A wane lokaci ne aka jefo Shaiɗan daga sama?—R. Yoh. 12:1-9.
Ko da yake Littafin Ru’ya ta Yohanna bai faɗi ainihin lokacin da aka kori Shaiɗan daga sama ba, ya ambata aukuwa dabam-dabam da za su taimake mu mu ƙiyasta lokacin da aka kore shi daga sama. Na farko shi ne Mulkin Almasihu da aka kafa. Bayan wannan, “aka yi yaƙi cikin sama,” wanda ya kai ga faɗuwar Shaiɗan kuma aka kore shi daga sama.
Nassosi sun nuna dalla-dalla cewa shekara ta 1914 ce “zamanan Al’ummai” ya cika kuma aka kafa Mulkin.a (Luk 21:24) Bayan hakan, wane lokaci ne aka yi yaƙi a sama da ya sa aka jefar da Shaiɗan?
Ru’ya ta Yohanna 12:4 ta ce: “Dragon [Shaiɗan] kuwa yana tsaye a gaban mace wadda tana bakin haifuwa, domin sa’anda ta haifu shi cinye ɗanta.” Hakan ya nuna cewa Shaiɗan yana son ya kawar da sabon Mulkin da sauri, da zarar an kafa shi idan zai yiwu. Ko da yake Jehobah ya hana Shaiɗan ya cim ma mugun nufinsa, Shaiɗan ya nace kuma ya ci gaba da ƙoƙari don ya halaka sabon Mulkin da aka kafa. Shi ya sa “Mika’ilu da nasa mala’iku” ba su ɓata lokaci ba wajen ɗaukan mataki don su kawar da ‘dragon da nasa mala’iku’ daga sama don kada su yi wa Mulkin ɓarna. Hakan ya nuna cewa cin nasara a kan Shaiɗan da kuma jefar da shi daga sama ya faru ba da daɗewa ba da kafa Mulkin a shekara ta 1914.
Wani abu kuma da za a yi la’akari da shi shi ne tashin matattu na Kiristoci shafaffu, wanda ya soma kamar yadda Nassi ya nuna, ba da baɗewa ba da kafa Mulkin.b (R. Yoh. 20:6) Tun da yake ba a ambata cewa akwai wani cikin ’yan’uwan Kristi da suka bi shi wajen yaƙi da Shaiɗan da mala’ikunsa, hakan ya nuna cewa an riga an kammala yaƙi a sama da kuma jefar da Shaiɗan sa’ad da aka soma ta da ’yan’uwan Kristi daga matattu.
Saboda haka, Littafi Mai Tsarki bai faɗi ainihin lokacin da aka jefar da Shaiɗan da aljanunsa daga sama ba. Duk da haka, a bayyane yake cewa hakan ya faru ne bayan da aka naɗa Yesu Kristi sarki a sama a shekara ta 1914.
[Hasiya]
b Ka duba Hasumiyar Tsaro, ta 1 ga Janairu, 2007, shafuffuka 29-30, sakin layi na 9-13.