Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 72 p. 170-p. 171 par. 2
  • Sa’ad da Yesu Yake Karami

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sa’ad da Yesu Yake Karami
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Kāre, Ya Tanadar Kuma Ya Jimre
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Yesu Ya Koyi Yin Biyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Saurayi Yesu A Haikali
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yesu Ya Yi Biyayya a Kowane Lokaci
    Ku Koyar da Yaranku
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 72 p. 170-p. 171 par. 2
Yesu dan shekara goma sha biyu ya zauna a tsakiyar malamai a cikin haikali

DARASI NA 72

Sa’ad da Yesu Yake Ƙarami

Yusufu da Maryamu suna zama a birnin Nazarat tare da Yesu da sauran ’yan’uwansa. Yusufu kafinta ne kuma yana aiki sosai don ya biya bukatun iyalinsa da kuma koya masu Dokar Jehobah. Suna zuwa majami’a a kai a kai don yin ibada kuma suna zuwa Urushalima kowace shekara don su yi Idin Ƙetarewa.

Sa’ad da Yesu yake ɗan shekara 12, iyalinsa ta yi wata tafiya mai nisa zuwa Urushalima kamar yadda suka saba yi. Birnin yana cike da mutanen da suka zo Idin Ƙetarewa. Sa’ad da Yusufu da Maryamu suke komawa gida, sun ɗauka cewa Yesu yana cikin jama’ar da suke tafiyar tare. Amma sai suka neme shi suka rasa.

Sai suka sake komawa Urushalima, kuma sun yi kwana uku suna neman sa. A ƙarshe, suka je haikalin. Yesu yana zaune tare da malamai kuma yana sauraran su da kuma yi musu tambayoyi. Hakan ya burge malaman da har suka soma yi wa Yesu tambayoyi. Sun yi mamakin abubuwan da Yesu yake faɗa, kuma sun ga cewa ya san Dokar Jehobah sosai.

Yusufu da Maryamu sun damu sosai. Sai Maryamu ta ce: ‘Ɗana, ina ka je? Mun yi ta neman ka a ko’ina!’ Sai Yesu ya ce: ‘Ba ki san cewa dole ne in kasance a gidan Ubana ba?’

Yesu ya koma Nazarat tare da iyayensa. Yusufu ya koya wa Yesu aikin kafinta. A ganin ka, Yesu wane irin mutum ne sa’ad da yake ƙarami? Yayin da Yesu yake girma, hikimarsa ta ci gaba da ƙaruwa kuma Allah da mutane suna son shi sosai.

Yusufu da Maryamu sun zauna tare da Yesu da kuma ’yan’uwansa maza da mata

“Murna nake yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.”​—Zabura 40:8

Tambayoyi: A wane wuri ne Yusufu da Maryamu suka ga Yesu? Me ya sa ya je wurin?

Matta 13:​55, 56; Markus 6:3; Luka 2:​40-52; 4:16; Kubawar Shari’a 16:​15, 16

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba