Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Yau

Laraba, 15 ga Afrilu

Ku ƙaunaci juna.—Yoh. 15:12.

Bayin Jehobah suna son taimaka wa juna. (2 Kor. 8:4) Amma a wasu lokuta, yin hakan yana bukatar ƙarfin zuciya. Idan aka soma yaƙi, dattawa sun san cewa ꞌyanꞌuwa za su bukaci abubuwa da yawa. Alal misali, za su bukaci ƙarfafawa, da abubuwan biyan bukata, da kuma abubuwan da za su taimaka musu su ci-gaba da yin kusa da Jehobah. Da yake suna ƙaunar ꞌyanꞌuwan nan sosai, sukan tanada musu abubuwan nan duk da cewa yin hakan zai sa rayukansu cikin haɗari. Idan muna cikin haɗari, muna bukatar mu zama masu yin biyayya don bakinmu ya zama ɗaya. Mu bi umurni da muka samu daga reshen ofishinmu. (Ibran. 13:17) Ya kamata dattawa su riƙa bincika umurnai da aka bayar a kan yadda za su yi shiri don lokacin balaꞌi, da abin da ya kamata su yi idan balaꞌi ya auku. (1 Kor. 14:​33, 40) Ka yi ƙarfin zuciya, amma ka yi hattara. (K. Mag. 22:3) Kar ka sa ranka cikin haɗari, babu-gaira-babu-dalili. Ka dogara ga Jehobah. Da taimakonsa, za ka iya taimaka wa ꞌyanꞌuwanka ba tare da wani abu ya same ka ba. w24.07 4 sakin layi na 8; 5 sakin layi na 11

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026

Alhamis, 16 ga Afrilu

A cikin damuwata na yi kira ga Yahweh, . . . kukana kuma ya kai kunnensa.—Zab. 18:6.

Sarki Dauda ya san Jehobah kuma ya dogara gare Shi. Saꞌad da Sarki Shawulu da wasu mutane suke ƙoƙarin kashe Dauda, ya roƙi Jehobah ya taimaka masa. (Zab. 18:6) Da Jehobah ya cece shi, Dauda ya ce: “Yahweh mai rai ne!” Mene ne Dauda yake nufi da ya ce Allah mai rai ne? Wani littafi da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya ce Dauda yana nufin cewa Jehobah Allah ne na gaskiya da ke taimaka wa bayinsa a kullum. Abubuwan da suka faru a rayuwar Dauda sun tabbatar masa da cewa Allahnsa mai rai ne. Hakan ya sa ya ci-gaba da bauta ma Allah da kuma yabon sa. (Zab. 18:​28, 29, 49) Idan muna da tabbacin cewa Jehobah Allah ne mai rai, hakan zai taimaka mana mu ci-gaba da bauta masa da ƙwazo. Zai kuma ba mu ƙarfin jimre matsalolin da muke fuskanta kuma ya sa mu yi niyyar ci-gaba da bauta ma Jehobah da ƙwazo. Ƙari ga haka, ba za mu bar wani abu ya sa mu yi nisa da Jehobah ba. w24.06 20-21 sakin layi na 3-4

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026

Jummaꞌa, 17 ga Afrilu

Kada kowa ya ruɗe ku ko ta yaya.—2 Tas. 2:3.

Mene ne za mu iya koya daga abin da manzo Bulus ya gaya wa ꞌyanꞌuwa da ke Tasalonika? Idan muka ji wani abin da bai yi daidai da abin da muka koya a Littafi Mai Tsarki ba, ko muka ji wani labari mai ban mamaki, mu yi hankali. A Tarayyar Soviet ta dā, maƙiyanmu sun yaɗa wani saƙo ta wasiƙa da sunan hedkwatarmu. Wasiƙar ta ƙarfafa wasu ꞌyanꞌuwanmu su ƙafa tasu ƙungiya mai zaman kanta. Kuma an rubuta wasiƙar kamar daga hedkwatarmu ce. Amma ꞌyanꞌuwa masu aminci ba su yarda da wasiƙar ba, domin sun ga cewa abin da ta ce bai jitu da gaskiyar da suka koya ba. A yau ma, maƙiyanmu suna amfani da abubuwa kamar intane da dandalin sada zumunta don su raɓa kanmu ko su rikitar da mu. Maimako mu “jijjigu da sauri,” mu dakata mu yi tunani ko abin da muka ji, ko muka karanta, ya jitu da gaskiyar da muka riga muka koya. Hakan zai sa mu tsaya daram a kan gaskiya.—2 Tas. 2:2; 1 Yoh. 4:1. w24.07 12 sakin layi na 14-15

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba