Ƙarin Bayani
a A talifin da ya gabata, mun tattauna abubuwa da yawa da Allah ya ba mu da ake gani. A wannan talifin, za mu mai da hankali ga abubuwan da ba a gani da yadda za mu iya nuna godiya dominsu. Hakan kuma zai sa mu ƙara nuna godiya ga Jehobah da ya tanada mana abubuwan nan.