Ƙarin Bayani
a A yau, bayin Jehobah da yawa suna fama da tsufa da kuma rashin lafiya mai tsanani. Kuma a wasu lokuta, dukanmu muna gajiya. Saboda haka, za mu iya ganin cewa ba za mu iya yin tseren nan ba. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya jimrewa a wannan tseren rai, kuma mu sami ladan rai na har abada da manzo Bulus ya yi magana a kai.