Ƙarin Bayani
h BAYANI A KAN HOTO: A watan Fabrairu 2019, Ɗan’uwa Gerrit Lösch memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya fitar da sabon juyin New World Translation a Jamusanci. A yau, masu shela a Jamus suna farin cikin yin amfani da wannan Littafi Mai Tsarki a wa’azi kamar yadda waɗannan ’yan’uwa mata biyu suke yi.