Ƙarin Bayani
a Idan muna jin tausayin mutane, hakan zai sa mu riƙa farin ciki, ban da haka, za mu sami sakamako mai kyau a wa’azinmu. Me ya sa? A wannan talifin, za mu tattauna darussa da za mu iya koya daga misalin Yesu da kuma hanyoyi huɗu da za mu nuna muna jin tausayin waɗanda muka haɗu da su sa’ad da muke wa’azi.