a Yesu bai faɗa ko ƙarar da aka kawo game da bawan gaskiya ce ko a’a ba. Amma kalmar Helenanci da aka fassara zuwa furucin nan “kai ƙararsa” a Luka 16:1 yana iya nufin cewa sharri aka yi masa. Kuma Yesu ya mai da hankali a kan yadda bawan ya kasance da hikima ne, ba abin da ya sa aka kore shi ba.