Ƙarin Bayani
b Annabcin da aka rubuta a Ezekiyel 37:1-14 da kuma Ru’ya ta Yohanna 11:7-12 sun cika a shekara ta 1919. Annabcin da ke cikin littafin Ezekiyel 37:1-14 yana nufin yadda dukan mutanen Allah suka soma ibada ta gaskiya bayan zaman bauta da suka yi na tsawon lokaci. Amma annabcin da ke cikin littafin Ru’ya ta Yohanna 11:7-12 yana magana game da wani ƙaramin rukunin ‘yan’uwa shafaffu da suka soma ja-gorar mutanen Allah a shekara ta 1919 kamar yadda yake a ƙarni na farko. Waɗannan ‘yan’uwa ba su samu sun yi aiki da ƙwazo na ɗan wani lokaci ba.