Ƙarin Bayani
d Babu shakka, Kalmar Allah tana ɗauke da wasu koyarwa da suke da ‘wuyar ganewa’ kuma wannan ya haɗa da rubutun da Bulus ya yi. Duk da haka, ruhu mai tsarki ne ya hure dukan mutanen da suka rubuta Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya taimaka wa Kiristoci a yau su fahimci “zurfafan al’amuran Allah,” wato koyarwar Littafi Mai Tsarki masu wuya.—2 Bit. 3:16, 17; 1 Kor. 2:10.