Ƙarin Bayani
a Littafin nan Insight on the Scriptures ya yi bayani a kan ƙoƙarin da ’yan kimiyya suka yi don su gano dalilin da ya sa ake tsufa da kuma mutuwa, ya ce: “Sun manta cewa Mahalicci ne da kansa ya zartar wa iyayenmu na farko hukuncin mutuwa. Ƙari ga haka, Allah ya yi hakan a hanyar da mutane ba za su iya fahimtar lamarin gaba ɗaya ba.”—Littafi na 2, shafi na 247.