Ƙarin Bayani
b Lamech ya ba ɗansa suna Nuhu, kuma mai yiwuwa ma’anar sunan shi ne “Hutu” ko kuma “Ta’aziya.” Lamech ya annabta cewa Nuhu zai aikata abin da sunansa yake nufi ta wajen kawo wa mutane hutu daga wahala da suke sha don an la’anta ƙasa. (Farawa 5:28, 29) Lamech ya mutu kafin annabcin nan ya cika.