Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwbq talifi na 60
  • Me Zai Taimaka Mini Na Daina Tsoron Mutuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Zai Taimaka Mini Na Daina Tsoron Mutuwa?
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Amsar Littafi Mai Tsarki
  • Ka Koyar Da Zuciyarka Ta Ji Tsoron Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Bincika Wasu Ƙage-Ƙage Game da Mutuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Ji Tsoron Jehovah Ka Kiyaye Dokokinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
ijwbq talifi na 60

Me Zai Taimaka Mini Na Daina Tsoron Mutuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Ba laifi ba ne mu ji tsoron mutuwa kuma muna iyakacin kokarinmu a tsare kanmu daga haka. (1 Korintiyawa 15:26) Amma irin banzan tsoro na razana da ake yi domin karya ko kuma camfi yana jefa mutane cikin “bauta muddar ransu.” (Ibraniyawa 2:​15) Sanin gaskiya zai ’yantar da kai daga banzan tsoron mutuwa, irin tsoron da ke hana mutum sukuni a rayuwa.​—Yohanna 8:​32.

Gaskiya game da mutuwa

  • Matattu ba su san kome ba. (Zabura 146:4) Kada ka yi tunani azaba ko ciwo bayan ka mutu, domin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mutuwa da barci.​—Zabura 13:3; Yohanna 11:11-​14.

  • Matattu ba za su iya mana wani barna ba. Ko magabta a dā ma sun “mutu.” (Misalai 21:16) Littafi Mai Tsarki ya ce “kiyayyarsu, da kishinsu, yanzu sun kare.”​—Mai-Wa’azi 9:6.

  • Mutuwa ba ita ce karshen rayuwarmu ba sam sam. Allah za ya dawo da mutane da suka mutu ta wurin ta da su zuwa rai.​—Yohanna 5:​28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15.

  • Allah ya yi alkawarin lokacin da “mutuwa kuwa ba za ta kara kasancewa ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Game da ranar nan, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-adalci za su gāji kasan, su zauna a cikinta har abada,” ba za a kara jin tsoron mutuwa kuma ba.​—Zabura 37:29.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba