ABUBUWAN DA ZA KU IYA YIN NAZARI A KAI
Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Zai Cece Ka
Karanta Littafin Ƙidaya 13:25–14:4 don ka ga abin da ya nuna cewa Israꞌilawa ba su dogara ga Jehobah ba.
Ka bincika labarin sosai. Me ya sa ya kamata Israꞌilawa su kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cece su? (Zab. 78:12-16, 43-53) Me ya sa suka soma ganin kamar Jehobah ba zai cece su ba? (M. Sha. 1:26-28) Ta yaya Joshuwa da Kaleb suka nuna cewa sun dogara ga Jehobah?—L. Ƙid. 14:6-9.
Ka nemi ƙarin bayani. Me ya kamata Israꞌilawa su yi da zai sa su ƙara dogara ga Jehobah? (Zab. 9:10; 22:4; 78:11) Wace alaƙa ce ke tsakanin dogara ga Jehobah da kuma daraja shi?—L. Ƙid. 14:11.
Ka yi tunani a kan abubuwan da ka koya. Ka tambayi kanka:
‘Waɗanne yanayoyi ne za su iya sa ya yi mini wuya in dogara ga Jehobah da dukan zuciyata?’
‘Mene ne zan iya yi don in ƙara dogara ga Jehobah yanzu da kuma a nan gaba?’
‘Idan aka soma ƙunci mai girma, wane tabbaci ne ya kamata in kasance da shi?’—Luk. 21:25-28.