SHAWARA A KAN YIN NAZARI
Abubuwan da Za Su Taimaka Maka Ka Riƙa Karanta Littafi Mai Tsarki Kowace Rana
Shin, yana maka wuya ka karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana? (Yosh. 1:8) Da yake muna da ayyuka da yawa, karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana zai iya yi mana wuya. Idan hakan yana faruwa da kai, ka gwada ɗaya daga cikin shawarwarin da aka ambata a gaba:
Ka sa ƙararrawa. Ka sa ƙararrawa a wayarka yadda za ta riƙa tuna maka cewa lokacin karanta Littafi Mai Tsarki ya yi.
Ka ajiye Littafi Mai Tsarkinka inda za ka riƙa ganin sa. Idan kana amfani da Littafi Mai Tsarki da aka buga, ka ajiye shi inda za ka riƙa ganin sa kowace rana.—M. Sha. 11:18.
Ka saurari karatun. Ka saurari karatun Littafi Mai Tsarki da aka ɗauka yayin da kake ayyukanka na yau da kullum. Wata ꞌyarꞌuwa majagaba mai suna Tara da take da yara uku kuma tana aiki da dare, ta ce: “Saurarar karatun Littafi Mai Tsarki saꞌad da nake ayyukana na yau da kullum yana taimaka mini in riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana.”
Kada ka gaji. Idan wasu abubuwa suka hana ka karanta Littafi Mai Tsarki lokacin da ka tsara, ka yi ƙoƙari ka karanta ko da ayoyi kaɗan ne kafin ka kwanta. Za ka amfana sosai ko da kaɗan ne ka karanta.—1 Bit. 2:2.