TALIFIN NAZARI NA 24
WAƘA TA 98 Nassosi Hurarre Ne Daga Allah
Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Annabcin Yakubu—Kashi na 1
“Ku tattaru wurina in faɗa muku abin da zai same ku a kwanaki masu zuwa.”—FAR. 49:1.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abin da za mu koya daga annabcin da Yakubu ya yi kafin ya mutu game da Ruben, da Simeyon, da Lawi, da kuma Yahuda.
1-2. Mene ne Yakubu ya yi kafin ya mutu, kuma me ya sa? (Ka kuma duba hoton.)
A LOKACIN da Yakubu ya tsufa sosai, shi da iyalinsa sun ƙaura zuwa ƙasar Masar daga Kanꞌana. Ya yi shekaru 17 a wurin yana bauta wa Jehobah da aminci. (Far. 47:28) Yakubu ya yi farin ciki sosai da ya sake ganin Yusuf, domin ya ɗauka cewa ya riga ya mutu. Yanzu shi da dukan yaransa maza suna zama tare a Masar. Amma Yakubu ya san cewa lokacin mutuwarsa ya yi kusa. Sai ya kira dukan yaransa maza don ya gaya musu wani abu mai muhimmanci.—Far. 49:28.
2 A zamaninsu, idan mahaifi ya ga cewa ya kusan mutuwa, yakan kira iyalinsa ya ba su umurni kafin ya mutu. (Isha. 38:1) Kuma a wannan lokacin zai iya ambata wanda zai zama shugaban iyalin bayan ya mutu.
Yakubu yana gaya wa ꞌyaꞌyansa maza guda 12 abubuwan da za su faru da su da zuriyarsu kafin ya mutu (Ka duba sakin layi na 1-2)
3. Bisa ga Farawa 49:1, 2, me ya sa abubuwan da Yakubu ya faɗa wa yaransa suke da muhimmanci sosai?
3 Karanta Farawa 49:1, 2. Amma abubuwan da Yakubu ya gaya wa iyalinsa ya yi dabam da waɗanda aka saba ji. Domin Yakubu ya faɗi abubuwan da za su faru a nan gaba. Da taimakon Jehobah, Yakubu ya gaya wa yaransa abubuwan da za su faru da su da zuriyarsu a nan gaba. Saboda haka, abubuwan da Yakubu ya gaya wa yaransa annabci ne.
4. Wane annabci ne Yakubu ya yi, kuma mene ne za mu iya koya daga abin da ya faɗa? (Ka kuma duba akwatin nan “Iyalin Yakubu.”)
4 A wannan talifin, za mu tattauna abin da Yakubu ya faɗa wa ꞌyaꞌyansa maza huɗu, wato: Ruben da Simeyon da Lawi da kuma Yahuda. A talifi na gaba, za mu tattauna abin da Yakubu ya gaya wa sauran ꞌyaꞌyansa maza takwas. Kamar yadda za mu gani, Yakubu ya yi annabci ne game da abin da zai faru da ꞌyaꞌyansa maza da kuma zuriyarsu. Daga baya, zuriyarsu ne za su zama alꞌummar Israꞌila. Idan muka bincika abin da ya faru da alꞌummar Israꞌila a dā, za mu ga yadda annabcin da Yakubu ya yi ya cika. Kuma yayin da muke bincika abubuwan da Yakubu ya faɗa, za mu ga darussa masu muhimmanci da za su taimaka mana mu faranta wa Jehobah rai.
RUBEN
5. Waɗanne abubuwa ne Ruben ya yi tsammani zai samu daga wurin mahaifinsu?
5 Yakubu ya fara magana da ɗansa Ruben ne, kuma ya gaya masa cewa: “Kai ne ɗan farina.” (Far. 49:3) Da yake shi ne ɗan fari, ya yi tsammani cewa zai gaji abubuwa fiye da sauran ꞌyanꞌuwansa. Mai yiwuwa, ya ɗauka cewa shi ne zai zama wanda zai yi wa iyalinsu ja-goranci bayan mutuwar mahaifinsu, kuma zuriyarsa za ta ci gaba da yin ja-goranci.
6. Me ya sa Ruben bai sami gādon da ake ba wa ɗan fari ba? (Farawa 49:3, 4)
6 Amma Ruben bai sami gādon da ake ba wa ɗan fari ba. (1 Tar. 5:1) Me ya sa? Domin bayan mutuwar Rahila, Ruben ya kwana da Bilhah baiwar Rahila. Rahila ta ba wa Yakubu Bilhah ta zama matarsa. To, me ya sa Ruben ya kwana da ita? Shi ɗan Laiꞌatu ne, ꞌyarꞌuwar Rahila. Saboda haka, mai yiwuwa ya kwana da Bilhah ne domin Yakubu ya ƙi jininta kuma ya ƙaunaci mahaifiyarsa fiye da sauran matan. Ko kuma ya yi hakan ne domin yana shaꞌawarta kuma ya gagara kame kansa. Ko da mene ne dalilinsa, abin da ya yi ya ɓata wa Jehobah rai da kuma mahaifinsu.—Karanta Farawa 49:3, 4.
7. Mene ne ya faru da Ruben da kuma zuriyarsa? (Ka kuma duba akwatin nan “Annabcin da Yakubu Ya Yi Kafin Ya Mutu.”)
7 Yakubu ya gaya wa Ruben cewa: “Ba za ka ƙara zama na farko ba.” Kuma abin da ya faru ke nan. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana cewa wani daga cikin zuriyar Ruben ya zama sarki, ko firist, ko annabi ba. Amma duk da haka, Yakubu ya ba wa Ruben gādo, kuma Ruben ya zama ɗaya daga cikin zuriyar Israꞌila. (Yosh. 12:6) Ruben ya ci gaba da nuna halaye masu kyau, kuma kamar bai ƙara yin lalata ba.—Far. 37:20-22; 42:37.
8. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga labarin Ruben?
8 Mene ne za mu iya koya? Wajibi ne mu guje wa shaꞌawoyin banza, kuma mu ƙudiri niyyar cewa ba za mu yi lalata ba. Idan muka fuskanci jarabar yin zunubi, mu ɗan dakata mu yi tunani a kan yadda hakan zai shafi dangantakarmu da Jehobah, da iyalinmu, da kuma wasu. Mu kuma tuna cewa “duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.” (Gal. 6:7) Ƙari ga haka, abin da ya faru da Ruben ya tuna mana cewa Jehobah mai jinƙai ne. Ko da yake Jehobah ba zai kāre mu daga sakamakon kuskuren da muka yi ba, zai albarkace mu idan muka tuba kuma muka yi iya ƙoƙarinmu wajen yin abubuwan da suka dace.
SIMEYON DA LAWI
9. Mene ne Simeyon da Lawi suka yi da ya sa Yakubu bai ji daɗi ba? (Farawa 49:5-7)
9 Karanta Farawa 49:5-7. Bayan Ruben, sai Yakubu ya yi wa Simeyon da Lawi magana, amma abin da ya gaya musu ya nuna cewa bai ji daɗin abin da suka yi ba. Shekaru kafin wannan lokacin, wani mutumin Kanꞌana mai suna Shekem ya yi wa ꞌyar Yakubu mai suna Dina fyaɗe. Abin da ya faru ya ɓata wa dukan yaran Yakubu rai sosai, amma Simeyon da Lawi ba su iya kame kansu ba. Sun yi wa Shekem da mutanensa ƙarya cewa idan dukansu sun yi kaciya, za su zauna lafiya da su. Shekem da mutanensa sun amince kuma suka yi kaciya. Tun suna kan fama da zafin ciwo, Simeyon da Lawi “suka ɗauki takubansu, suka fāɗa wa garin ba tsammani. Suka kakkashe dukan mazan.”—Far. 34:25-29.
10. Ta yaya annabcin da Yakubu ya yi game da Simeyon da Lawi ya cika? (Ka kuma duba akwatin nan “Annabcin da Yakubu Ya Yi Kafin Ya Mutu.”)
10 Yakubu ya yi fushi sosai don wannan abin da Simeyon da Lawi suka yi. Ya annabta cewa za a warwatsar da zuriyarsu a ƙasar Israꞌila. Abin da ya faɗa ya cika ne shekaru 200 bayan da ya yi annabcin, lokacin da Israꞌilawa suka shiga Ƙasar Alkawari. A lokacin, zuriyar Simeyon ta sami gādonta a birane dabam-dabam a cikin yankin gādon da Yahuda ya samu. (Yosh. 19:1) Zuriyar Lawi kuma ta gaji birane 48 a wurare dabam-dabam a cikin Israꞌila.—Yosh. 21:41.
11. Waɗanne abubuwa masu kyau ne zuriyar Simeyon da Lawi suka yi?
11 Zuriyar Simeyon da Lawi ba su sake kuskuren da kakanninsu suka yi ba. Lawiyawa da yawa sun bauta wa Jehobah da aminci. A lokacin da Musa ya hau kan Tudun Sinai don ya karɓi Doka daga wurin Jehobah, Israꞌilawa da yawa sun bauta wa gunki, amma Lawiyawa ba su yi hakan ba. A maimakon haka, sun taimaka wa Musa wajen halakar da waɗanda suka bauta wa gunkin. (Fit. 32:26-29) Jehobah ya ba wa Lawiyawa babban gatan zama firistoci a ƙasar Israꞌila. (Fit. 40:12-15; L. Ƙid. 3:11, 12) Kuma daga baya, zuriyar Simeyon sun taimaka wa zuriyar Yahuda su yaƙi Kanꞌaniyawa da ke yankinsu a Ƙasar Alkawari.—Alƙa. 1:3, 17.
12. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga labarin Simeyon da Lawi?
12 Mene ne za mu iya koya? Wajibi ne mu kame kanmu a lokacin da muke fushi. Idan aka yi maka, ko wani na kusa da kai rashin adalci, babu shakka za ka yi fushi. (Zab. 4:4) Amma zai dace mu tuna cewa Jehobah ba zai ji daɗi ba idan muka faɗi ko muka yi wani abu don mu rama abin da aka yi mana. (Yak. 1:20) Idan wani ya yi mana rashin adalci, ko da yana bauta wa Jehobah ko aꞌa, zai dace mu bi da yanayin a hanyar da zai faranta wa Jehobah rai. Don haka, ba za mu faɗi ko mu yi wani abin da zai jawo wa wani ila ba. (Rom. 12:17, 19; 1 Bit. 3:9) Ko da iyayenka suna yin abin da Jehobah ba ya so, ka tuna cewa ba dole ne ka bi halinsu marar kyau ba. Kada ka ɗauka cewa ba za ka iya sa Jehobah farin ciki ba. Jehobah zai taimaka maka ka yi abin da ya dace, kuma zai albarkace ka idan ka yi hakan.
YAHUDA
13. Me ya sa mai yiwuwa Yahuda ya damu a lokacin da mahaifinsa zai yi masa magana?
13 Bayan Simeyon da Lawi, sai Yakubu ya yi magana da Yahuda. Mai yiwuwa Yahuda ya damu sosai da ya ji abubuwan da babansu ya faɗa wa ꞌyanꞌuwansa, da yake shi ma ya yi kurakure da dama. Bayan da Simeyon da Lawi suka kashe mutanen Shekem, Yahuda tare da sauran ꞌyanꞌuwansa sun kwashi kayan mutanen. (Far. 34:27) Shi da ꞌyanꞌuwansa sun haɗa baki sun sayar da Yusuf, kuma suka yi wa mahaifinsu ƙarya. (Far. 37:31-33) Daga baya ya kwana da Tamar, matar ɗansa da ya mutu don ya ɗauka cewa ita karuwa ce.—Far. 38:15-18.
14. Waɗanne abubuwan alheri ne Yahuda ya yi? (Farawa 49:8, 9)
14 Amma Yakubu ya yaba wa Yahuda, kuma ya yi masa alkawari cewa abubuwa masu kyau za su faru da shi da zuriyarsa. (Karanta Farawa 49:8, 9.) Mai yiwuwa abubuwan alherin da Yahuda ya yi ne ya sa hakan ya faru. Alal misali, Yahuda ya nuna cewa ya damu sosai da yadda mahaifinsu yake ji. Kuma akwai lokacin da ya tausaya wa ƙaninsu, Benyamin.—Far. 44:18, 30-34.
15. A waɗanne hanyoyi ne albarkar da aka yi wa Yahuda suka cika?
15 Yakubu ya annabta cewa Yahuda ne zai zama mai mulki bisa ꞌyanꞌuwansa. Amma shekaru 200 sun wuce kafin annabcin ya soma cika. Bayan da Israꞌilawa suka bar Masar zuwa Ƙasar Alkawari, zuriyar Yahuda ne suka yi gaba, saꞌan nan sauran suka bi su a baya. (L. Ƙid. 10:14) Shekaru da yawa bayan hakan, Jehobah ya sa zuriyar Yahuda su fara yaƙan mutanen Kanꞌana don su kwace Ƙasar Alkawari. (Alƙa. 1:1, 2) Kuma Dauda ne sarki na farko a cikin sarakuna da yawa da suka yi mulki daga zuriyar Yahuda. Amma annabcin bai ƙare a nan ba.
16. Ta yaya annabcin da ke Farawa 49:10 ya cika? (Ka kuma duba akwatin nan “Annabcin da Yakubu Ya Yi Kafin Ya Mutu.”)
16 Yakubu ya ce wani daga zuriyar Yahuda ne zai yi sarautar dukan duniya, kuma zai yi hakan har abada. (Karanta Farawa 49:10, Littafi Mai Tsarki.)a Sarkin Yesu Kristi ne, kuma Yakubu ya kira shi Shilo. Wani malaꞌika ya ce game da Yesu: “Ubangiji Allah zai ba shi kujerar mulkin kakansa Dawuda.” (Luk. 1:32, 33) Ƙari ga haka, an kira Yesu “Zakin nan daga zuriyar Yahuda.”—R. Yar. 5:5.
17. Ta yaya za mu yi koyi da Jehobah a yadda muke ɗaukan mutane?
17 Mene ne za mu iya koya? Jehobah ya yi wa Yahuda albarka duk da cewa ya yi kurakure da yawa. Mai yiwuwa ꞌyanꞌuwansa sun kasa gane dalilin da ya sa Jehobah ya albarkace shi haka. Duk da cewa ba mu san tunanin da ꞌyanꞌuwansa suka yi ba, Jehobah ya ga abubuwa masu kyau a wurin Yahuda kuma ya albarkace shi. Ta yaya za mu yi koyi da Jehobah? Idan aka ba wa wani ɗanꞌuwa aiki na musamman, mai yiwuwa ba za mu fahimci abin da ya sa aka ba shi aikin ba, musamman idan mun san wasu kurakuren da ya yi. Amma zai dace mu tuna cewa Jehobah ya ga abubuwa masu kyau da mutumin yake yi, kuma yana mai da hankali ga halaye masu kyau na masu bauta masa. Abin da ya kamata kowannenmu ya riƙa yi ke nan.
18. Me ya sa ya kamata mu zama masu haƙuri?
18 Wani abu kuma da muka koya daga labarin Yahuda shi ne mu zama masu haƙuri. Jehobah yana cika alkawuransa kowane lokaci, amma dole ne mu jira har lokacin da Jehobah zai yi hakan, kuma zai iya yin hakan a hanyar da ba mu yi tsammani ba. Alal misali, waɗanda suka soma shugabanci a ƙasar Israꞌila ba su fito daga zuriyar Yahuda ba. Amma zuriyar Yahuda ta ba su goyon baya da haɗin kai. Sun goyi bayan Musa daga zuriyar Lawi, da Joshua daga zuriyar Ifrayim, da Sarki Shawulu da ya fito daga zuriyar Benyamin. Bari mu ma mu goyi bayan duk wanda Jehobah ya zaɓa ya yi mana ja-goranci a yau.—Ibran. 6:12.
19. Mene ne muka koya game da Jehobah daga talifin nan?
19 Mene ne muka koya daga abin da Yakubu ya gaya wa ꞌyaꞌyansa maza huɗu? Mun ga cewa “yadda Yahweh yake gani ba haka mutum yake gani ba.” (1 Sam. 16:7) Jehobah yana da haƙuri sosai kuma shi mai gafartawa ne. Duk da cewa ba ya jin daɗi idan muka yi abin da bai dace ba, ya san cewa bayinsa ba za su iya bauta masa babu kuskure ba. Yakan albarkaci waɗanda suka yi kurakurai a dā kuma suka tuɓa suka soma yin abin da ya dace. A talifi na gaba, za mu tattauna abin da Yakubu ya gaya wa sauran ꞌyaꞌyansa maza takwas.
WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci
a Farawa 49:10: “Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jamaꞌoꞌi.”