DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Kada Ku Yi Koyi da Elifaz Saꞌad da Kuke Taꞌazantar da Mutane
Elifaz ya gaya wa Ayuba cewa ꞌyan Adam ba za su iya taɓa faranta wa Allah rai ba (Ayu 15:14-16; w22.10 26 sakin layi na 10)
Elifaz yana nufin cewa Ayuba mugu ne, shi ya sa yake shan wahala (Ayu 15:20)
Abubuwan da Elifaz ya faɗa ba su taꞌazantar da Ayuba ba (Ayu 16:1, 2)
Abin da Elifaz ya gaya wa Ayuba ƙarya ne. Jehobah yana farin ciki da yadda muke ƙoƙarin bauta masa. (Za 149:4) Masu adalci ma za su fuskanci matsaloli.—Za 34:19.
DON BIMBINI: Ta yaya za mu iya “ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya”?—1Ta 5:14. w15 2/15 9 sakin layi na 16.