Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Yuli p. 13
  • Wa’azi na Musamman don Soma Nazari da Mutane a Satumba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wa’azi na Musamman don Soma Nazari da Mutane a Satumba
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za A Yi Amfani da Sabuwar Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah!
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Waꞌazi na Musamman a Watan Satumba don A Yi Shelar Mulkin Allah!
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Sabuwar Mujalla da Za a Ba Da!
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Kana Yin Amfani da Waɗannan Ƙasidun?
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Yuli p. 13
Hotuna: Iyalin da ke talifin nan “Ku Kafa Makasudai Don Sabuwar Shekara Ta Hidima​—Hidimar Majagaba” suna wa’azi. 1. Matashiyar da mahaifiyarta suna tattauna kasidar “Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!” da wata mata a kofar gidanta. 2. Kakar matashiyar tana amfani da kasidar “Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!” don ta yi nazari da wata a waya. 3. Mahaifinta da mahaifiyarta suna wa’azi da amalanke da aka nuna kasidar “Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!” da kuma yadda ake nazari da mutane.

RAYUWAR KIRISTA

Wa’azi na Musamman don Soma Nazari da Mutane a Satumba

A watan Satumba, za mu yi ƙoƙari sosai don mu nuna wa kowa yadda muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Masu shela za su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci kuma su ba da awa 30. Ta yaya za mu iya yin wannan wa’azi na musamman?

  • A Haɗuwa ta Fari: Ka yi amfani da bayanin da ke bayan ƙasidar don ka sa mutumin ya so wa’azinmu. Kuma ka nuna masa yadda muke nazari da mutane. Ka tuna kuma ka je wurin waɗanda suka so saƙonmu a dā, har da waɗanda ka koma ziyara a wurinsu. Ko da sun ƙi a soma nazari da su a dā, suna iya son yadda muke nazari yanzu da ƙasidar. Kada a bar ƙasidar a gidajen mutanen da ba sa gida, ko a saka a cikin wasiƙa zuwa ga waɗanda ba su taɓa nuna suna son saƙonmu ba. ’Yan’uwa da ke Kwamitin Hidima na Ikilisiya za su iya shirya wasu taron fita wa’azi a watan ban da waɗanda aka saba yi.

  • Wasu Hanyoyin Yin Wa’azin: Idan ana amfani da amalanken yin wa’azi a ikilisiyarku, a saka ƙasidar Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! a amalanken. Ka gaya wa wanda ya karɓi ƙasidar cewa za a iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kyauta. Ka ɗan nuna masa yadda ake nazarin a wurin ko ku shirya lokacin za ka nuna masa. Mai kula da hidima zai iya shirya wasu masu shela da suka ƙware, su je wuraren kasuwanci su nuna wa mutane yadda muke nazarin Littafi Mai Tsarki. Za ka iya nuna wa abokan aikinka yadda muke nazari da mutane, ko waɗanda ka haɗu da su sa’ad da kake harkokinka na yau da kullum.

Yesu ya ba mu umurni cewa, mu je mu sa mutane su ‘zama almajiransa’ kuma mu koyar da su. (Mt 28:​19, 20) Bari wannan wa’azi na musamman ya taimaka mana mu cim ma hakan ta wajen amfani da Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba