Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Janairu p. 11
  • Ka Zaɓi Bauta wa Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Zaɓi Bauta wa Jehobah
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Za Ka Amfana Sosai Idan Ka Yi Baftisma!
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Baftisma Tana da Muhimmanci ga Kiristoci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Abin da Baftisma Take Nufi da Kuma Muhimmancin Yin Hakan
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Cika Farillan Baftisma Na Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Janairu p. 11
Wata hanya da ke nuna matakai da mutum zai dauka don ya bauta wa Jehobah. Alamar da ke kan hanyar tana nuna matakan yin nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taro da yin wa’azi da kuma baftisma.

Kana ɗaukan matakai don ka cancanci yin baftisma?

RAYUWAR KIRISTA

Ka Zaɓi Bauta wa Jehobah

Idan ba ka yi baftisma ba ko kuma kai ɗalibi ne da ke nazarin Littafi Mai Tsarki, shin za ka so ka yi baftisma? Me ya sa ya kamata ka yi baftisma? Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, hakan zai sa ka kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Za 91:1) Kuma yin hakan zai sa ka sami ceto. (1Bi 3:21) Waɗanne matakai ne za ka ɗauka don ka cancanci yin baftisma?

Ka yi nazari don ka gamsar da kanka cewa wannan ce gaskiya. Idan kana da tambayoyi, ka yi bincike da kanka don ka san amsarsu. (Ro 12:2) Ka bincika kanka don ka ga inda kake bukatar gyara kuma ka yi hakan saboda ƙaunar da kake yi wa Jehobah. (K. Ma 27:11; Afi 4:​23, 24) Ka riƙa neman taimakonsa. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya ƙarfafa da kuma taimaka maka. (1Bi 5:​10, 11) Ba za ka yi da-na-sanin yin hakan ba, domin bauta wa Jehobah ita ce abu mafi muhimmanci a rayuwa!​—Za 16:11.

KU KALLI BIDIYON NAN MATAKAN DA ZA KA ƊAUKA KAFIN YIN BAFTISMA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne wasu suka magance don su iya yin baftisma?

  • Ta yaya za ka iya sa bangaskiyarka ta yi ƙarfi don ka iya yi wa Jehobah alkawarin bauta masa?

  • Mene ne ya sa wasu suka ɗauki matakin yin baftisma?

  • Waɗanne albarku ne waɗanda suka zaɓi su bauta wa Jehobah za su samu?

  • Mene ne yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma suke nufi?

Bayan ɗan’uwan ya gama jawabin baftisma, sai ya gaya wa waɗanda za su yi baftisma su tashi tsaye kuma su amsa waɗannan tambayoyi guda biyu da babbar murya:

Kun tuba daga zunubanku, kun yi alkawarin bauta wa Jehobah, kuma kun gaskata da hanyar ceto da Allah ya yi ta wurin Yesu Kristi?

Kun fahimci cewa yin baftisma zai nuna cewa ku Shaidun Jehobah ne masu tarayya da ƙungiyarsa?

Idan waɗanda za su yi baftisma suka amsa e ga tambayoyin nan, hakan “shaida” ce cewa sun ba da gaskiya ga fansar Yesu kuma sun yi alkawari za su bauta wa Jehobah.​—Ro 10:​9, 10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba