Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Yuni p. 8
  • Iyaye, Ku Koyar da Yaranku da Kyau Don Su Yi Nasara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Iyaye, Ku Koyar da Yaranku da Kyau Don Su Yi Nasara
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Yara “Gādo Ne Daga Wurin Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Iyaye, Ku Koyar Da ’Ya’yanku Cikin Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Yuni p. 8
Yusufu da Maryamu suna koya wa Yesu da sauran yaransu game da Jehobah a lokacin da suke cin abinci

RAYUWA Ta KIRISTA

Iyaye, Ku Koyar da Yaranku da Kyau Don Su Yi Nasara

Iyaye da suke ƙaunar Jehobah sukan yi marmarin ganin yaransu suna bauta ma Jehobah da aminci. Iyaye za su iya taimaka ma yaransu su yi hakan ta wurin koya musu Kalmar Allah tun suna jarirai. (M.Sh 6:7; K. Ma 22:6) Shin iyaye suna bukatar yin sadaukarwa kafin su iya cim ma hakan? Ƙwarai kuwa! Amma albarkar da za su samu tana da yawa sosai.​—3Yo 4.

Iyaye za su iya koyan darasi daga Maryamu da Yusufu. A “kowace shekara iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa,” duk da cewa hakan ba ƙaramin aiki ba ne kuma sukan kashe kuɗi sosai. (Lu 2:41) Abu mafi muhimmanci a wurin Yusufu da Maryamu shi ne iyalinsu su kusaci Jehobah. Kamar yadda Yusufu da Maryamu suka yi, ya kamata iyaye su taimaka ma yaransu su mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci ta wurin yin amfani da kowace dama don su koyar da yaransu kuma su kafa musu misali mai kyau.​—Za 127:​3-5.

KA SANI?

Duk da cewa iyalin Yesu suna bauta ma Jehobah, wasu ’yan’uwan Yesu ba su gaskata da shi da farko ba sai bayan mutuwarsa. (Yoh 7:5; A. M. 1:14) Daga baya, biyu daga cikinsu, wato Yakub da Yahuda sun rubuta littattafai da ke ɗauke da sunayensu.

KU KALLI BIDIYON NAN SUN YI AMFANI DA KOWACE DAMA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya Jon da Sharon Schiller suka ci gaba da bauta ma Jehobah a lokacin da suke renon yaransu?

  • Me ya sa iyaye suke bukatar su tarbiyyartar da yaransu bisa ga yanayin yaran?

  • Ta yaya iyaye za su taimaka ma yaransu tun da wuri don su iya jimrewa sa’ad da aka jarraba amincinsu?

  • A cikin littattafai da muke da su, wanne ka taɓa amfani da shi don ka taimaka wa yaronka ya zama aminin Jehobah?

Iyalin Schiller

Ku sa bauta wa Jehobah ya zama abu mafi muhimmanci a iyalinku

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba