DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 6-7
Ku Saka Mulkin Allah Farko a Rayuwarku
A cikin addu’ar da Yesu ya koyar, ya nuna cewa abubuwan da ya kamata mu fi mai da hankali a kai su ne Mulkin Allah da kuma abubuwan da suka jitu da nufinsa.
Sunan Allah
Mulkin Allah
Nufin Allah
Abincin yini
Gafarar zunubai
Kāriya daga jarraba
Wasu abubuwan da suka jitu da Mulkin da zan iya yin addu’a a kai:
Ci gaba da wa’azin Mulkin
Ruhun Allah ya taimaka ma waɗanda ake tsananta musu
Allah ya albarkaci aikin gine-gine da kuma kamfen na wa’azi
Allah ya ba wa waɗanda suke ja-goranci ƙarfi da kuma hikima
Wasu