DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 25-28
Ka Yi Ƙarfin Hali Kamar Irmiya
Irmiya ya yi gargaɗi cewa za a halaka Urushalima kamar yadda aka halaka Shiloh
26:6
Sanduƙin alkawari yana nuna cewa Jehobah na tare da Isra’ilawa, kuma a dā ana ajiye shi a Shiloh
Jehobah ya ƙyale Filistiyawa su kwace Sanduƙin Alkawarin kuma tun daga lokacin ba a sake ajiye shi a Shiloh ba
Firistoci da annabawa da kuma dukan mutanen sun yi barazanar kashe Irmiya
26:8, 9, 12, 13
Mutanen sun kama Irmiya don annabcin da ya yi game da Urushalima da kuma haikalin
Amma Irmiya bai karaya ba
Jehobah ya kāre Irmiya
26:16, 24
Irmiya ya ci gaba da kasancewa da gaba gaɗi kuma Jehobah bai yi watsi da shi ba
Allah ya sa Ahikam mai ƙarfin hali ya kāre Irmiya
Da taimakon Jehobah, Irmiya ya yi shekara 40 yana shelar saƙon hukunci