Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/12 p. 1
  • Abubuwa Uku da Za Su Inganta Koyarwarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abubuwa Uku da Za Su Inganta Koyarwarka
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Koyi Da Babban Malami
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Misalai Masu Amfani
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • “Ba Ya Faɗa Musu Kome Ba Sai Game Da Misali”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Mai Da Hankali Ga ‘Iyawarka Ta Koyarwa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 4/12 p. 1

Abubuwa Uku da Za Su Inganta Koyarwarka

1. Me ya sa ya kamata mu nemi hanyoyin inganta koyarwarmu?

1 Dukan masu shela malamai ne. Ko da muna yin wa’azi ne a gida-gida, ko kuma muna koma ziyara, ko gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki, koyarwa ce muke yi. Kuma abin da muke koyarwa yana da muhimmanci sosai. Muna ba da ƙarin haske ne a kan “littattafai masu-tsarki,” waɗanda ke sa mutane su zama masu ‘hikima don samun ceto.’ (2 Tim. 3:15) Hakika, wannan gata ne na musamman! Ga abubuwa uku da za su taimaka mana mu inganta yadda muke koyarwa.

2. Ta yaya za mu iya koyarwa a hanya mai sauƙin ganewa?

2 Sauƙin Ganewa: Idan mun fahimci batun da muke tattaunawa sosai, muna iya manta cewa mai yiwuwa batu ne mai wuya ga wanda bai sani ba. Saboda haka, sa’ad da kake gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki, kada ka yi bayanai da yawa da ba a bukata. A maimakon haka, ka faɗi muhimman batutuwa kawai. Ba yawan magana ba ne koyarwa mai kyau. (Mis. 10:19) Zai fi dacewa ka karanta ainihin nassin da ke da nasaba da batun da kake tattaunawa. Bayan ka karanta nassi, ka mai da hankali ga batun da kuke tattaunawa. Huɗuba a kan Dutse, wadda aka rubuta a Matta sura 5 zuwa 7, tana ɗauke da gaskiya mai zurfi, duk da haka Yesu ya bayyana gaskiyar a hanya mai sauƙin ganewa kuma bai yi amfani da kalmomi masu yawa ba.

3. Mene ne amfanin misalai, kuma waɗanne irin misalai ne suka fi dacewa?

3 Misalai: Misalai suna sa tunani, suna sosa rai, kuma suna sa a tuna batu da wuri. Kada ka ɗauka cewa kana bukatar ka zama wanda ya iya ba da labari kafin ka ba da misalai masu kyau. Sau da yawa, Yesu ya yi amfani da taƙaitattun misalai waɗanda ba su da wuyar fahimta. (Mat. 7:3-5; 18:2-4) Hotuna masu sauƙin ganewa waɗanda aka zana a kan takarda za su iya taimakawa sosai. Shiri mai kyau zai taimaka maka ka yi tunanin misalai masu kyau da za ka yi amfani da su.

4. Ta yaya za mu yi amfani da tambayoyi yadda mutane za su amfana?

4 Tambayoyi: Tambayoyi za su sa ɗalibinka ya yi tunani. Saboda haka, ka yi haƙuri da shi sa’ad da ka yi tambaya. Idan ka yi saurin amsa tambayar da kanka, ba za ka sani ba ko ya fahimci batun ko a’a. Idan amsar da ya ba da ba daidai ba ne, zai dace ka yi masa ƙarin tambayoyin da za su sa ya amsa tambayar da kyau maimakon ka yi masa gyara kawai. (Mat. 17:24-27) Hakika, babu wani kamiltaccen malami a cikin mu. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu riƙa mai da hankali sosai ga yadda muke koyarwa. Idan muka yi haka, za mu amfana har abada tare da waɗanda suke sauraronmu.—1 Tim. 4:16.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba