TARIHI
Na Amfana Domin Na Dogara ga Jehobah
Ba za mu iya sanin ainihin abin da zai faru a rayuwarmu ba. A wasu lokatai, yanayi zai iya yin wuya sosai. Amma Jehobah yana wa mutanen da suke dogara gare shi albarka. Abin da ni da kuma matata muka koya ke nan a rayuwarmu mai ma’ana. Ku ɗan dakata ku sha labari.
MAHAIFINA da mahaifiyata sun haɗu a taron ƙasashe na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da aka yi a mashaƙatar Cedar Point, jihar Ohio, Amirka a shekara ta 1919. Kuma a wannan shekarar ce suka yi aure. An haife ni a shekara ta 1922 kuma an haifi ɗan’uwana Paul shekaru biyu bayan ni. An haifi matata Grace a shekara ta 1930. Kakanninta da iyayenta Roy da Ruth Howell Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ne kuma kakanninta ɗin abokan Ɗan’uwa Charles Taze Russell ne.
Na haɗu da Grace a shekara ta 1947 kuma mun yi aure a ranar 16 ga Yuli, shekara ta 1949. Kafin mu yi aure, mun tattauna yadda muke son rayuwarmu ta kasance. Mun tsai da shawarar yin hidima ta cikakken lokaci tare kuma mun ce ba za mu haihu ba. Mun soma hidimar majagaba a shekara ta 1950, kuma a shekara ta 1952, aka gayyace mu yin hidimar mai kula da da’ira.
HIDIMAR MAI KULA MAI ZIYARA DA KUMA MAKARANTAR GILEAD
Mun ji cewa muna bukatar taimako don mu yi nasara a sabon gatan da aka danƙa mana. Na koyi darasi daga ’yan’uwan da suka manyanta kuma na so a koyar da matata sosai. Sai na tattauna batun da wani abokinmu mai suna Marvin Holien da wani mai kula mai ziyara da ya manyanta kuma na tambaye su: “Grace matashiya ce kuma ba ta ƙware ba. Don Allah za ku iya gaya mini wata da za ta so ta riƙa fita wa’azi tare da matata don ta ƙware?” Sai ya ce Edna Winkle majagaba ce da ta ƙware kuma za ta iya taimaka mata sosai. Daga baya, Grace ta ce Edna ta taimaka mata ta kwantar da hankalinta sa’ad da take tattauna da mutane a wa’azi. Ta kuma koya mata abin da za ta ce sa’ad da wani bai yarda da abin da ta ce ba, kuma ta koya mata yadda za ta riƙa sauraron mutane da kuma ba da amsa. Grace kuma ta ce: “Edna ainihin abin da nake bukata ce!”
Ni da matata mun yi hidima a da’irori biyu a jihar Iowa. Da’irorin sun kuma ƙunshi sashen jihar Minnesota da Dakota na Kudu. Bayan haka, aka tura mu Da’ira ta 1 a birnin New York, wadda ta ƙunshi sashen Brooklyn da Queens. Na tuna yadda na ji tsoro sa’ad da aka ba ni wannan aikin. Da’irar ta ƙunshi ikilisiyar Brooklyn Heights wadda ke yin taro a Majami’ar Mulkin da ke Bethel. Akwai ’yan’uwa masu hidima a Bethel da yawa da suka ƙware a wannan ikilisiyar. Bayan na kammala jawabin hidima na farko, sai Ɗan’uwa Nathan Knorr ya zo wuri na ya ce: “Malcolm, ka gaya mana inda muke bukatar gyara, kuma hakan ya dace. Kada ka manta cewa idan ba ka taimaka mana ta wajen gargaɗar da mu ba, to lallai ba ka da amfani a ƙungiyar Jehobah. Kada ka karaya.” Bayan taron, na gaya wa matata abin da ya faru. Sai muka koma masaukin da muka zauna a makon a cikin Bethel. Mun gaji tikis har muka soma kuka.
“Idan ba ka taimaka mana ta wajen gargaɗar da mu ba, to lallai ba ka da amfani a ƙungiyar Jehobah. Kada ka karaya”
Bayan ’yan watanni, aka aika mana wata wasiƙa. Ka san abin da ke cikin wasiƙar? Gayyata ce zuwa aji na 24 na Makarantar Gilead, kuma za a sauke karatu a watan Fabrairu na shekara ta 1955. Kafin mu je makarantar, an gaya mana cewa wataƙila ba za a tura mu yin hidima a wata ƙasa ba. Maimakon haka, koyarwar za ta taimaka mana a hidimar mai kula mai ziyara. Mun ji daɗin makarantar sosai kuma mun koyi kasancewa da tawali’u.
Bayan mun sauke karatu, sai aka tura mu yin hidimar mai kula da gunduma. Da’irarmu ta ƙunshi jihohin Indiana da Michigan da kuma Ohio. Mun yi mamaki sosai a watan Disamba na shekara ta 1955, sa’ad da muka karɓi wata wasiƙa daga Ɗan’uwa Knorr. Ya ce: “Ka gaya mini gaskiya. Kana so ka zo hidima a Bethel . . . ko kana so a tura ka yin hidima a wata ƙasa ko kuma hidimar mai kula da da’ira?” Ka san abin da muka ce masa? Mun ce za mu so mu yi hidima a duk inda aka tura mu. Nan da nan, aka ce mana mu zo Bethel!
NA JI DAƊIN YIN HIDIMA A BETHEL
A waɗannan shekarun da na yi hidima a Bethel, an tura ni wurare da yawa a ƙasar Amirka don na ba da jawabai a ikilisiyoyi da kuma manyan taro. Na taimaka wajen koyar da ’yan’uwa maza da yawa da za su samu gata da yawa a ƙungiyar Jehobah. Daga baya, na zama sakataren Ɗan’uwa Knorr a ofishin da ke tsara aikin wa’azi a faɗin duniya.
Na ji daɗin shekarun da na yi ina aiki a Sashen Hidima. Na yi hidima tare da Ɗan’uwa T. J. (Bud) Sullivan. Ya kwashi shekaru da yawa yana kula da wannan sashen. Amma akwai ’yan’uwa da yawa da na koyi darasi daga wurinsu. Alal misali, na koyi darasi sosai daga Ɗan’uwa Fred Rusk wanda aka ce ya koyar da ni. Na tuna ranar da na tambaye shi dalilin da ya sa yake yawan gyare-gyare a wasiƙun da na rubuta. Sai ya yi dariya ya ce: “Malcolm, sa’ad da ka furta kalmomi, za ka iya yin ƙarin bayani, amma idan ka rubuta abu, musamman idan daga nan ne, wajibi ne ka yi ƙoƙari don kada ka yi ko kuskure guda.” Sai ya gaya mini: “Kada ka yi fargaba. Kana ƙoƙari kuma da sannu-sannu, za ka saba da aikin.”
Sa’ad da muke Bethel, matata ta yi ayyuka dabam-dabam haɗe da aikin share ɗakuna. Ta ji daɗin wannan aikin sosai. Har yau, idan muka haɗu da wasu ’yan’uwa da matasa ne sa’ad da muke Bethel, suna yawan ce wa matata cikin fara’a, “Lallai, kin koya mini yadda ake gyara gado, kuma hakan ya sa mahaifiyata farin ciki.” Matata ta kuma ji daɗin yin aiki a Sashen Mujallu da Rubuta Wasiƙu da Sauti. Waɗannan ayyukan da ta yi sun taimaka mata ta san cewa ko da wane irin aiki muke yi ko kuma inda muke, yi wa ƙungiyar Jehobah hidima babban gata ne da kuma albarka. Kuma wannan ra’ayinta bai canja ba har yanzu.
CANJE-CANJEN DA MUKA YI
Gab da shekara ta 1975, mun ankara cewa iyayenmu son soma tsufa kuma suna bukatar taimako. A sakamako, muka yanke wata shawara mai wuya sosai. Ba mu so mu bar Bethel da kuma ’yan’uwan da muke ƙauna sosai. Amma duk da haka, na san cewa hakki na ne na kula da iyayenmu. Saboda haka, muka bar Bethel daga baya, amma mun so mu sake dawowa idan yanayinmu ya canja.
Domin mu sami abin biyan bukata, sai na soma sayar da inshora. Ba zan taɓa mance abin da wani manaja ya ce mini ba sa’ad da yake koyar da ni. Ya ce: “Wannan aikin ya ƙunshi zuwa gidajen mutane da yamma. Lokacin da za ka yi ciniki ke nan. Yana da muhimmanci sosai ka riƙa zuwa gidajen mutane kullum da yamma.” Sai na gaya masa cewa na san ya ƙware a aikin sosai, amma abin da ya fi muhimmanci a wuri na shi ne bauta wa Allah kuma ba zan iya canja hakan ba. Na yarda cewa zan riƙa zuwa gidajen mutane da yamma, amma ban da ranar Talata da Alhamis domin ina zuwa taro mai muhimmanci a waɗannan ranakun. Jehobah ya albarkace ni sosai domin ban ƙyale aiki ya hana ni halartar taro ba.
Muna tare da mahaifiyata sa’ad da ta rasu a watan Yuli na shekara ta 1987. Bayan ta rasu, sai nas da ke kula da ita ta ce wa matata: “Malama Allen, ki koma gida ki ɗan huta. Kowa ya san cewa kina kasancewa a nan kullum don ki kula da surukar ki. Ki ƙwantar da hankalinki.”
A watan Disamba na shekara ta 1987, mun sake cika afilkeshan don yin hidima a wurin da muke sha’awa sosai, wato Bethel. Amma bayan kwana biyu, sai muka gano cewa matata tana da ciwon daji na mazawari. Bayan an yi mata aiki kuma ta samu sauƙi, sai aka gaya mana cewa ta warke. Jim kaɗan bayan haka, sai muka karɓi wasiƙa daga Bethel cewa mu ci gaba da hidima a ikilisiyarmu. Mun duƙufa mu ci gaba da yin ƙwazo a hidimar Jehobah.
Daga baya, sai na samu aiki a jihar Texas. Mun yanke shawarar ƙaura zuwa wurin domin yanayin garin yana da zafi kuma mun ji daɗin garin sosai. Mun yi shekara 25 yanzu a wannan jihar kuma mun yi abokai maza da mata masu ƙauna sosai.
DARUSSAN DA MUKA KOYA
A cikin shekarun da suka shige, matata ta yi fama da ciwon daji na mazawari da maƙogwaro da kuma mama, amma ba ta taɓa gunaguni ba. Tana goyon baya na sosai kuma tana yi mini ladabi a matsayin shugaban iyalin. Mutane suna yawan tambayarta sirrin nasara da kuma farin cikin da muke yi a aurenmu. Ta ce mu aminai ne, muna tattaunawa kullum, muna kasancewa tare a kowace lokaci kuma ba ma barci muna fushi da juna. Ko da yake muna ɓata wa juna rai a wasu lokatai, amma muna gafarta wa juna kuma hakan yana taimaka mana sosai.
“Ka riƙa dogara ga Jehobah kuma ka haƙura da abin da ya ƙyale ya faru”
Mun koyi darussa da yawa a duk gwaje-gwajen da muka fuskanta:
Kada ka taɓa jingina ga naka fahimi.—Mis. 3:5, 6; Irm. 17:7.
Yin biyayya ga Jehobah da kuma dokokinsa yana da muhimmanci. Wajibi ne mu yi zaɓi guda, wato ko mu yi biyayya ko a’a.—Rom. 6:16; Ibran. 4:12.
Ka saka abin da Jehobah yake so a kan gaba a rayuwarka ba kuɗi ba.—Mis. 28:20; M. Wa. 7:1; Mat. 6:33, 34.
Ka yi tunani a kan abin da za ka iya yi, ba abin da ba za ka iya yi ba.—Mat. 22:37; 2 Tim. 4:2.
Mun kusan shekara 65 da yin aure, kuma kowannenmu ya bauta wa Jehobah fiye da shekara 75. Mun ji daɗin bauta wa Jehobah cikin shekaru da yawa. Muna fata da kuma addu’a cewa dukan ’yan’uwanmu maza da mata za su shaida irin farin cikin da ake shaidawa sa’ad da aka dogara ga Jehobah.