Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/15 pp. 22-26
  • ‘Zan Ji Tsoron Wane Ne?’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Zan Ji Tsoron Wane Ne?’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “UBANGIJI NE HASKENA DA CETONA”
  • KA TUNA DA DUKAN LOKATAN DA JEHOBAH YA TAIMAKA MAKA
  • ƘAUNARMU GA BAUTA TA GASKIYA
  • KA DOGARA GA TAIMAKON ALLAH
  • “YA UBANGIJI, KA KOYA MINI TAFARKINKA”
  • BANGASKIYA DA BEGE SUNA DA MUHIMMANCI
  • Cikakkiyar Dogara Ga Jehobah Tana Sa Mu Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Jehobah—“Mai-ceto” Ne A Zamanin Da Aka Rubuta Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • “Masu Neman Sanin Jehobah Ba Za Su Rasa Abu Mai Kyau Ba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Tsoron Allah Hikima Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/15 pp. 22-26

‘Zan Ji Tsoron Wane Ne?’

“Ko da magabtana sun tasar mini, zan dogara ga Allah.”​—ZAB. 27:3, Littafi Mai Tsarki.

TA YAYA WAƊANNAN AYOYIN SUKE TAIMAKA MAKA KA KASANCE DA GABA GAƊI?

Zabura 27:1

Zabura 27:4

Zabura 27:11

1. Mene ne Zabura ta 27 za ta taimaka mana mu fahimta?

ME YA sa muke samun ƙaruwa a aikin wa’azinmu, ko da yake yanayin duniya yana daɗa lalacewa? Me ya sa muke farin cikin yin amfani da lokacinmu da kuma kuzarinmu don yin wa’azi duk da cewa tattalin arziki yana daɗa taɓarɓarewa? Yaya za mu iya ci gaba da kasancewa da gaba gaɗi duk da cewa mutane da yawa suna tsoron abin da zai iya faruwa gobe? Waƙar da Sarki Dauda ya rera, da ke littafin Zabura sura ta 27 ta ba da amsa ga waɗannan tambayoyin.

2. Yaya tsoro yake shafan mutum, kuma wane gaba gaɗi ne muke da shi?

2 Dauda ya soma wannan waƙar da waɗannan kalmomin: “Ubangiji ne haskena da cetona kuma; tsoron wa zan ji? Ubangiji shi ne ƙarfin raina; zan ji tsoron wanene?” (Zab. 27:1) Jin tsoro sosai zai iya naƙasa mutum har ba zai iya yin kome ba. Amma, mutumin da yake dogara ga Jehobah yana da gaba gaɗi kuma ba ya tsoron kome. (1 Bit. 3:14) Idan mun sa Jehobah ya zama ƙarfinmu, za mu “zauna lafiya, za [mu] zauna da rai a kwance, ba tsoron masifa.” (Mis. 1:33; 3:25) Me ya sa?

“UBANGIJI NE HASKENA DA CETONA”

3. Mene ne furucin nan, Jehobah ne haskena yake nufi, kuma mene ne ya wajaba mu yi?

3 Kalmar nan “Ubangiji ne haskena” yana nufin cewa Jehobah ne yake koya mana gaskiya. (Zab. 27:1) Haske na gaske yana haskaka hanyarmu don mu ga haɗarin da za mu guje wa, amma hasken ba ya cire haɗarin. Ya kamata mu guje wa haɗarin. Hakazalika, Jehobah yana bayyana mana haɗarin da ke wannan mugun yanayin da duniya take ciki. Ya tanadar mana da ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki da suke taimaka mana. Amma, wajibi ne mu yi amfani da su. Idan mun yi hakan, za mu kasance da hikima fiye da maƙiyanmu ko kuma malamanmu.—Zab. 119:98, 99, 130.

4. (a) Me ya sa Dauda ya ce Jehobah ne cetonsa? (b) A wane lokaci ne ainihi Jehobah zai zama cetonmu?

4 Kalaman Dauda a Zabura 27:1 sun nuna cewa babu shakka ya tuna yadda Jehobah ya cece shi sau da yawa. Alal misali, Jehobah ya cece shi “daga bakin zaki, da bakin bear kuma.” Jehobah ya kuma taimaka masa ya ci nasara a kan Goliyat. Daga baya, Sarki Saul ya yi ƙoƙari sau da yawa ya kashe Dauda da mashi, amma Jehobah ya cece shi. (1 Sam. 17:37, 49, 50; 18:11, 12; 19:10) Shi ya sa Dauda ya rera wannan waƙar cike da tabbaci: ‘Ubangiji ne cetona’! Jehobah zai kuma ceci bayinsa kamar yadda ya ceci Dauda. A wane lokaci ne zai yi hakan? A lokacin “babban tsananin.”—R. Yoh. 7:14; 2 Bit. 2:9.

KA TUNA DA DUKAN LOKATAN DA JEHOBAH YA TAIMAKA MAKA

5, 6. (a) Ta yaya yin tunani a kan abubuwan da suka taɓa faruwa da mu zai iya sa mu samu gaba gaɗi? (b) Me ya sa ya dace mu yi tunani a kan yadda Jehobah ya ceci bayinsa a dā?

5 Zabura 27:2, 3 tana ɗauke da wani abu mai muhimmanci da zai taimaka mana mu samu ƙarin gaba gaɗi. (Karanta.) Dauda ya tuna lokatan da Jehobah ya cece shi. (1 Sam. 17:34-37) Waɗannan abubuwan sun sa ya kasance da gaba gaɗi ya jimre da kowanne irin yanayin da zai fuskanta. Kai ma ka tuna yadda Jehobah ya taɓa taimaka maka? Alal misali, ka taɓa yin addu’a sosai game da wata matsala mai tsanani kuma ka shaida yadda Jehobah ya ba ka hikima ko kuma ƙarfi ka jimre da matsalar? Ko kuma, ka tuna yadda Jehobah ya taimaka maka ka magance wasu matsaloli da suka hana ka bauta masa da farin ciki? Ko ka tuna yadda ya sa ka samu sabon hanyoyin yi masa hidima? (1 Kor. 16:9) Ta yaya tuna da waɗannan abubuwan suke shafanka? Ya kamata waɗannan abubuwan su ci gaba da ba ka tabbaci cewa Jehobah zai iya taimaka maka ka magance ko kuma ka jimre da matsala da kuma yanayi mafi wuya.—Rom. 5:3-5.

6 Mene ne za ka yi idan wata gwamnati mai iko sosai tana son ta halaka Shaidun Jehobah gabaki ɗaya? Wasu mutane a zamaninmu sun nemi su yi hakan, amma sun kasa. Yin tunani a kan yadda Jehobah ya taimaki bayinsa a dā zai sa mu kasance da gaba gaɗi game da nan gaba.—Dan. 3:28.

ƘAUNARMU GA BAUTA TA GASKIYA

7, 8. (a) Kamar yadda littafin Zabura 27:4 ya nuna, mene ne Dauda ya roƙi Jehobah? (b) Mene ne haikalin Jehobah na alama, kuma yaya ake bauta a wurin?

7 Ƙaunarmu ga bauta ta gaskiya za ta kuma taimaka mana mu samu gaba gaɗi. (Karanta Zabura 27:4.) A zamanin Dauda, haikali ne “gidan Ubangiji.” Dauda ne ya shirya kome don ɗansa Sulemanu ya gina kyakkyawar haikali ga Jehobah. Shekaru da yawa bayan haka, Yesu ya bayyana cewa lokaci zai zo da mutane ba za su bukaci zuwa haikalin don bauta wa Jehobah ba. (Yoh. 4:21-23) A littafin Ibraniyawa sura ta 8 da 10, manzo Bulus ya ce wannan haikali na alama, ya wanzu sa’ad da Yesu ya yi baftisma a shekara ta 29 a zamanin Kristi, sa’ad da ya ba da kansa don yin nufin Jehobah. (Ibran. 10:10) Wannan haikali na alama yana nufin shirin da Jehobah ya yi don mu bauta masa idan mun yi imani ga hadayar fansa ta Kristi. Ta yaya muke bauta a wannan haikalin? Ta wajen yin addu’a “da zuciya mai-gaskiya da sakankancewar bangaskiya,” da kuma yi wa mutane wa’azi da gaba gaɗi. Da kuma sa’ad da muke halartar taron ikilisiya da kuma yin bauta ta iyali. (Ibran. 10:22-25) Ƙaunarmu ga bauta ta gaskiya za ta taimaka mana mu ci gaba da yin waɗannan abubuwan a waɗannan kwanaki na ƙarshe.

8 A dukan duniya, amintattun bayin Jehobah suna daɗa yin wa’azi sosai da ƙwazo, suna koyon sabon harsuna kuma sun ƙaura zuwa inda ake da bukatar masu wa’azi sosai. Suna kama da marubucin Zabura da ya roƙi abu ɗaya daga wurin Jehobah. Suna son su more jamalin Jehobah kuma su saka hannu a tsarkakkiyar hidima a kowane irin yanayi.—Karanta Zabura 27:6.

KA DOGARA GA TAIMAKON ALLAH

9, 10. Mene ne ma’anar tabbacin da ke Zabura 27:10?

9 Kalaman Dauda sun nuna yadda yake dogara ga Jehobah. Ya ce: “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni.” (Zab. 27:10) Littafin 1 Sama’ila sura ta 22 ta nuna cewa iyayen Dauda ba su yashe shi ba. Amma, wasu iyaye sun yashe ’ya’yansu a yau. Duk da haka, sun samu taimako da kuma kāriya daga Kiristoci masu ƙauna a cikin ikilisiya.

10 Jehobah yana a shirye ya kula da bayinsa ko da mutane sun yashe su. Kuma hakan ya tabbatar mana cewa zai kula da su sa’ad da suke fuskantar wasu matsaloli. Alal misali, idan muna tunanin yadda za mu kula da iyalinmu, ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana. (Ibran. 13:5, 6) Ya san yanayinmu da kuma abubuwan da muke bukata.

11. Idan mun dogara ga Jehobah, ta yaya hakan zai iya shafan mutane? Ka ba da misali.

11 Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata da ke nazarin Littafi Mai Tsarki a ƙasar Liberiya, mai suna Victoria. Mutumin da suke zama tare ya yashe ta da yaransu uku. Ko da yake ba ta da wurin kwana da aikin yi ba ta daina yin nazarin Littafi Mai Tsarki ba kuma daga baya ta yi baftisma. Wata rana, ’yarta mai shekara 13 ta tsinci wata jaka cike da kuɗi. Victoria da ’yarta sun ƙi ƙirga kuɗin don kada su soma sha’awar kuɗin da ba nasu ba ne. Sai suka nemi sojan da ya ɓatar da jakar nan da nan. Sa’ad da suka gan shi, sai ya ce idan kowa a duniya yana yin gaskiya kamar Shaidun Jehobah, duniya baki ɗaya za ta zama wuri mai kyau da kuma salama. Victoria ta yi amfani da Littafin Mai Tsarki don nuna wa sojan cewa Jehobah ya yi mana alkawarin sabuwar duniya. Imanin Victoria ya burge sojan sosai, kuma hakan ya motsa shi ya ba ta kyautar wasu kuɗaɗe. Mutane a dukan faɗin duniya sun san cewa Shaidun Jehobah suna da gaskiya. Domin suna dogara gabaki ɗaya ga Jehobah cewa zai kula da su.

12. Me ya sa muke ci gaba da bauta wa Jehobah duk da cewa za mu iya rasa aikinmu ko kuɗinmu? Ka ba da misali.

12 Ka kuma yi tunanin yadda Thomas, wani mai shela da bai yi baftisma ba a ƙasar Saliyo ya ji. Tun da ya soma aiki a wata makaranta kusan shekara ɗaya, ba a biya shi albashi ba. Sai Thomas ya je wajen shugaban makarantar don su tattauna game da kuɗin da yake binsu. Amma, shugaban firist ne, kuma ya gaya wa Thomas cewa ba a amince da koyarwar Shaidun Jehobah a makarantar ba. Ya ce idan Thomas yana son ya ci gaba da yin aiki a makarantar, dole ne ya yi tir da Shaidun Jehobah. Thomas ya bar aikin ko da yake ba a biya shi albashinsa ba. Daga baya, sai Thomas ya samu aikin gyaran rediyo da kuma wayar selula. Misalai da yawa sun nuna cewa idan mun dogara ga Jehobah, bai kamata mu ji tsoron cewa ba za mu iya biyan bukatunmu ba. Jehobah yana kula da mu domin shi ne ya halicci dukan abu kuma yana kāre bayinsa.

13. Me ya sa ’yan’uwan da suke zama a ƙasashen da ake talauci suke wa’azi da ƙwazo sosai?

13 ’Yan’uwan da suke zama a ƙasashen da akwai talauci sosai suna yin wa’azi sosai da ƙwazo. Me ya sa? Rahoto daga wani ofishin reshe ya ce: “Mutane da yawa da suka amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su ba su da aiki kuma hakan ya sa suna da lokaci sosai. ’Yan’uwa ma suna da lokacin yin wa’azi. Mutane suna saurin yarda cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe domin suna shaida hakan a yankinsu.” A wata ƙasa kuma masu shela da yawa suna gudanar da aƙalla nazari uku. Wani mai wa’azi a ƙasashen waje da ya yi shekara 12 a wurin ya ce: “Masu shela da yawa suna da lokacin yin wa’azi da gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki domin babu abubuwa da yawa da ke raba hankalinsu.”

14. A waɗanne hanyoyi ne taro mai girma za su iya more kāriyar Jehobah?

14 Jehobah ya yi alkawari cewa zai taimaki bayinsa da kāre su da kuma cece su a matsayin rukuni, kuma mun gaskata cewa zai yi hakan. (Zab. 37:28; 91:1-3) Taro mai yawan gaske za su tsira daga “babban tsananin.” (R. Yoh. 7:9, 14) Saboda haka, Allah zai kāre taro mai girma don kada kowa ya halaka su baki ɗaya a wannan kwanaki na ƙarshe. Jehobah zai ba su dukan abin da suke bukata don su jimre da gwaje-gwaje kuma su kiyaye dangantakarsu da shi. Kuma Jehobah zai ceci bayinsa a lokacin Armageddon.

“YA UBANGIJI, KA KOYA MINI TAFARKINKA”

15, 16. Ta yaya za mu amfana idan muka bi koyarwar Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.

15 Idan muna son mu ci gaba da kasancewa da gaba gaɗi, wajibi ne Allah ya ci gaba da koyar da mu. Dauda ya ce: “Ya Ubangiji, ka koya mini tafarkinka; ka bishe ni kuma a cikin hanya sosai saboda maƙiyana.” (Zab. 27:11) Idan mun yi biyayya ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da kuma ja-gorar da ƙungiyar Jehobah take mana, za mu nuna cewa Allah yana koyar da mu. Ya kuma kamata mu yi amfani da abin da muka koya. Alal misali, mutane da yawa sun bi shawarar da aka ba mu cewa mu sauƙaƙa salon rayuwarmu. Sun biya bashin da suke bi kuma sun sayar da abubuwan da ba sa bukata. Hakan ya sa ba sa yawan damuwa idan tattalin arziki ya taɓarɓare. Kuma yanzu ba sa aiki tuƙuru don su biya kuɗin abin da ba sa bukata. Kuma suna saka hannu sosai a hidima. Ya kamata dukanmu mu tambayi kanmu, ‘Ina hanzarin bin dukan abin da na karanta daga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da bawan nan mai aminci ya wallafa, ko da yin hakan yana da wuya?’—Mat. 24:45.

16 Idan mun ƙyale Jehobah ya koyar da mu kuma ya gaya mana yadda za mu yi rayuwa, ba za mu ji tsoron kome ba. Sa’ad da wani majagaba a ƙasar Amirka ya nemi ya rage sa’o’in da yake yi a wurin aiki don shi da iyalinsa su ci gaba da yin hidimar majagaba, shugaban aikinsa ya ce hakan ba zai yiwu ba domin bai je jami’a ba. Da a ce kai ne hakan ya faru wa, da za ka yi da-na-sani ne don ba ka je jami’a ba? Makonni biyu bayan haka, aka kori shugaban daga aikin sai sabon shugaban ya tambayi ɗan’uwan game da maƙasudinsa. Ɗan’uwan ya gaya wa shugaban cewa shi da matarsa majagaba ne na Shaidun Jehobah, kuma suna son su ci gaba da hidimar. Amma, kafin ɗan’uwan ya sake ce kome, sai shugaban ya ce: “Na san cewa akwai abin da ya bambanta ka da sauran mutane! Sa’ad da babana yake rashin lafiya kuma ya kusan mutuwa, ’yan’uwanku biyu sun zo wurinsa sun karanta masa wata aya a cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma na yi alkawari cewa idan na samu zarafi zan taimaki Shaidun Jehobah.” Washegari sai aka ba wannan ɗan’uwan wannan aikin da tsohon shugaban ya ƙi ba shi. Hakika, idan mun saka Mulkin Allah farko a rayuwarmu, Jehobah zai cika alkawarin da ya mana cewa zai ba mu dukan abin da muke bukata.—Mat. 6:33.

BANGASKIYA DA BEGE SUNA DA MUHIMMANCI

17. Me zai taimaka mana don kada mu ji tsoron abin da zai iya faruwa a nan gaba?

17 Dauda ya sa mu fahimci muhimmancin bangaskiya da kuma bege. Ya ce: “Da ba domin na gaskata zan ga alherin Ubangiji a cikin ƙasa ta masu-rai, da na suma.” (Zab. 27:13) Da a ce Allah bai ba mu bege ba kuma ba mu san abin da ke cikin littafin Zabura sura ta 27 ba, da yaya rayuwarmu za ta kasance? Saboda haka, ya kamata mu riƙa yin addu’a ga Jehobah a wannan kwanaki na ƙarshe don ya ba mu ƙarfi kuma ya cece mu daga yaƙin Armageddon.—Karanta Zabura 27:14.

[Hoto a shafi na 23]

Dauda ya samu gaba gaɗi sa’ad da ya tuna yadda Jehobah ya cece shi

[Hoto a shafi na 25]

Kana ɗaukan taɓarɓarewar tattalin arziki a matsayin dama na faɗaɗa hidimarka kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba