Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/1 pp. 9-11
  • Yin Rayuwa Daidai Ƙarfinka Yadda Hakan Zai Yiwu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Rayuwa Daidai Ƙarfinka Yadda Hakan Zai Yiwu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mizanan Littafi Mai Tsarki da Za Su Taimaka
  • Ka Koya Daga Wasu
  • Za Ka Iya Yin Rayuwa Daidai Ƙarfinka
  • Matsalolin Kudi da Cin Bashi​—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimakawa Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Kashe Kuɗi Yadda Ya Kamata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ku Kashe Kuɗi a Hanyar da Ta Dace
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/1 pp. 9-11

Yin Rayuwa Daidai Ƙarfinka Yadda Hakan Zai Yiwu

A CE kana da duron da ke cike da ruwa kuma aikin ka shi ne ka tabbatar da cewa yana cike da ruwa a koyaushe. Mene ne za ka yi don ya kasance a cike da ruwa? Kana bukatar ka mai da ruwan da aka ɗebo daga cikin duron. Duron zai kasance a cike da ruwa idan ka zuba daidai ruwan da aka ɗiba daga ciki.

Abin da ake nufi da yin rayuwa daidai da ƙarfin mutum ke nan. Za a iya kwatanta kuɗin da kake samu da ruwan da kake zubawa cikin duro. Kuɗin da kake kashewa yana kama ne da ruwan da kake ɗiba daga cikin duron. Ƙalubalen shi ne kada ka ƙyale kuɗin da kake kashewa ya wuce wanda kake samu.

Ko da yake wannan bayanin yana da sauƙi, matsalar ita ce yin amfani da shawarar. Mutane za su iya guje wa faɗawa cikin matsalolin da suka shafi kuɗi idan za su ƙoƙarta su bi wannan muhimmiyar shawara. Ta yaya za a iya yin hakan? A ina ne za mu iya samun ja-goranci mai amfani? A cikin Littafi Mai Tsarki ne kawai za mu iya samun bayanan da za su taimaka mana a kan wannan batu. Bari mu ɗan duba abin da ya ce.

Mizanan Littafi Mai Tsarki da Za Su Taimaka

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da mizanai da dama masu amfani da za su iya taimaka maka ka yi amfani da kuɗaɗenka a hanya mai kyau. Za mu bincika kaɗan daga cikin su. Ka bincika ka gani ko ka amince cewa waɗannan mizanan za su iya taimaka maka ka yi rayuwa daidai da ƙarfinka.

Ka yi kasafin kuɗin da kake kashewa. Domin ka bi da kuɗi yadda ya kamata, kana bukatar sanin yawan kuɗin da ke shiga hannunka da kuma yadda kake kashe su. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka sami abin da zai ishe ka ba.” (Misalai 21:5, Littafi Mai Tsarki) Wasu suna yin amfani da ambulan don su tsara yadda suke kashe kuɗinsu. Kowane ambulan yana ƙunshe ne da abin da za a kashe kuɗi a kai, kamar “Abinci,” “Kuɗin haya,” ko “Sitira.” Ko da kana amfani ne da wannan tsarin ko wani, abin da ya fi muhimmanci shi ne sanin inda kuɗinka yake shiga, kuma a kowane lokaci, bukatunka su kasance kan gaba ba jin daɗi ba.

Ka guji ƙyashi. Mutane da yawa a ƙasashe masu tasowa suna sha’awar samun abubuwan da mutanen da ke ƙasashe masu arziki suke da su. Mutane da yawa suna iya yin sha’awar abubuwan da maƙwabtansu suke fahariya da su. Hakan zai iya zama tarko. Wataƙila maƙwabcin ya sayo waɗannan abubuwan ne da kuɗin aro. Me zai sa ka yi irin wautar da wani ya yi kuma ka faɗa cikin matsalar kuɗi? Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.”—Misalai 28:22, LMT.

Kada ka biɗi manyan abubuwa. Jehobah ya shawarci Baruch sakataren Irmiya ‘kada ya biɗar wa kansa manyan abubuwa.’ (Irmiya 45:5) Wani karin maganar Hausa ya ce “kwaɗayi mabuɗin wahala.” In ji wani rahoton da aka samu daga Asian Development Bank, kashi ɗaya cikin uku na mutanen da ke ƙasar Philippines da kuma fiye da rabin waɗanda suke zaune a Indiya ne suke rayuwa ƙasa da ainihin kuɗin da ake bukata don biyan bukatun yau da kullum a ƙasar Asiya, wato, dalar Amirka 1.35 a rana. Sa’ad da mutane suka samu irin wannan kuɗi ƙalilan, zai fi dacewa a mai da hankali ga bukatu. Ko a ƙasashe masu arziki, wannan mizanin zai iya taimaka wa mutane su guji faɗawa cikin matsalolin kuɗi.

Ka gamsu da ainihin abin da kake bukata. Wannan shawarar ta yi daidai da wadda ta ce ka guji biɗar manyan abubuwa. Littafi Mai Tsarki ya ba da wannan shawarar a 1 Timotawus 6:8: “Da ya ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.” Wasu daga cikin mutane mafi farin ciki a duniya ba su da kuɗi sosai; duk da haka, suna samun gamsuwa da abubuwan da suke da shi, waɗanda suka haɗa da nuna ƙauna ga iyali da abokai, ba dukiya ba.—Misalai 15:17.

Ka guji cin bashin da bai zama dole ba. Wannan furuci na Littafi Mai Tsarki gaskiya ne: “Mawadaci ya kan ci mulki bisa matalauci, mai-cin bashi kuma bawa ne ga mai-bada bashi”! (Misalai 22:7) Ko da yake akwai wasu yanayin da za su iya tilasta wa mutum ya ciwo bashi, waɗanda suka ci bashi kawai don su sayi wani abin da suke sha’awa za su faɗa cikin babban matsalar kuɗi.—2 Sarakuna 4:1; Matta 18:25.

Ka yi ajiyar kuɗi kafin ka soma sayayya. Ko da yake ana iya yi masa kallon tsohon yayi, yin ajiyar kuɗi kafin a soma sayayya yana ɗaya daga cikin hanyoyi mafi kyau da za su sa mutum ya guje wa matsalar kuɗi. Yin haka yana sa mutane da yawa su guji cin bashi da masifun da ke tattare da hakan, kamar su biyan ruwa mai yawa, wanda a ƙarshe yake ƙara yawan kuɗin dukan abubuwan da mutum ya saya. A cikin Littafi Mai Tsarki, an kwatanta tururuwa a matsayin abu mai “hikima” domin tana “tattara abincinta da kaka” saboda nan gaba.—Misalai 6:6-8; 30:24, 25.

Ka Koya Daga Wasu

Dukan shawarwarin nan na Littafi Mai Tsarki da muka tattauna suna da kyau, amma da gaske ne cewa suna taimaka wa mutane su yi rayuwa daidai da ƙarfinsu? Bari mu duba labaran wasu da suka bi shawarwarin nan kuma suka yi nasara wajen bi da matsalolin kuɗi.

Diosdado, wani mahaifi mai yara huɗu, ya ce gurguncewar tattalin arziki da ta auku a kwanan nan ya sa biyan bukatun iyalinsa ya yi masa wuya. Duk da haka, ya fahimci muhimmancin yin kasafin kuɗi. Ya ce: “Ina yin kasafin dukan kuɗin da nake samu. Ina lissafin abubuwa da zan kashe kuɗina a kai.” Danilo ma yana bin wannan mizanin. Kasuwancin da yake yi da matarsa ya faɗi. Amma, suna iya biyan bukatunsu ta wajen tsara kuɗin da suke samu. Ya ce: “Mun san yawan kuɗin da muke samu a kowane wata, kuma mun san yawan kuɗin da muke kashewa. Bisa ga hakan, muna tattaunawa dalla-dalla a kan yawan kuɗin da za mu iya kashewa.”

Domin su bi kasafin kuɗin da suka yi yadda ya kamata, wasu sun ga muhimmancin rage kuɗin da suke kashewa a kan wasu abubuwa. Myrna, wata gwauruwa da take rainon yara uku, ta ce: “Maimakon mu shiga motar haya domin mu halarci taron Kirista, ni da yarana muna takawa da ƙafa.” Myrna ta yi ƙoƙarin taimaka wa yaranta su koyi amfanin yin rayuwa mai sauƙi. Ta ce: “Na yi ƙoƙarin kafa misali mai kyau wajen yin amfani da mizanin da ke 1 Timotawus 6:8-10, wadda ta nuna cewa yana da muhimmanci mutum ya gamsu da abin ya mallaka.”

Gerald, wanda yake da yara biyu, ya yi makamancin haka. Ya ce: “Sa’ad da muke Bauta ta iyali, muna tattauna labaran Kiristoci da suka mai da hankalinsu ga abin da ya fi muhimmanci, wato, abubuwan da suka shafi dangantakarsu da Jehobah. Sakamakon yana da ban ƙarfafa domin yaranmu ba sa biɗar abubuwa marasa muhimmanci.”

Janet budurwa ce, wadda take hidima na cikakken lokaci na koyar da Littafi Mai Tsarki a ƙasar Philippines. Ta rasa aikinta kwanan nan, amma ta ci gaba da yin rayuwa daidai da ƙarfinta. Ta ce: “Ina cim ma hakan ta wajen horar da kaina da kuma tsara yadda zan yi amfani da abubuwan da nake da su yadda ya dace. Maimakon zuwa manyan shaguna masu tsada don yin sayayya, ina zuwa shagunan da suke da kaya masu araha. Me zai sa in biya kuɗi mai yawa a kan abin da zan iya saye a farashi mai rahusa? Ina kuma guje wa yin sayayya ba tare da tunani ba.” Janet ta ga amfanin yin ajiyar kuɗi tun da wuri. Ta ce: “Sa’ad da na samu kuɗi, ko da ɗan kaɗan ne, ina ajiye shi domin in samu abin rufin asiri sa’ad da wata bukata na ba zato ta taso.”

Za Ka Iya Yin Rayuwa Daidai Ƙarfinka

Babu shakka, mutane da yawa sun ga cewa ko da yake Littafi Mai Tsarki ya fi mai da hankali ne ga abubuwan da za su jawo mu kusa da Jehobah, yana kuma ba da ja-gorar da za ta amfane mu a hanyoyi na zahiri. (Misalai 2:6; Matta 6:25-34) Idan muka yi amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki da aka tattauna a wannan talifin kuma muka yi koyi da yadda wasu suka amfana daga bin waɗannan mizanan, kai ma za ka iya yin rayuwa daidai da ƙarfinka. Yin haka zai sa ka kauce wa masifu da alhini da miliyoyin mutane suke fama da su a yau.

[Bayanin da ke shafi na 10]

‘Muna tattaunawa dalla-dalla a kan yawan kuɗin da za mu iya kashewa’

[Bayanin da ke shafi na 11]

‘Maimakon mu shiga motar haya domin mu halarci taron Kirista, muna takawa da ƙafa’

[Bayanin da ke shafi na 11]

‘Ina guje wa yin sayayya ba tare da yin tunani ba’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba