Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/15 pp. 7-11
  • Ka Ci Gaba Da Biɗan “Adalcinsa” Da Farko

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci Gaba Da Biɗan “Adalcinsa” Da Farko
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Haɗarin Zama Mai Adalcin Kai
  • Wani Haɗari Shi Ne “Cika Yin Adalci”
  • Ba Kowane Lokaci Ba Ne Muke da Cikakken Labarin
  • Wataƙila Ra’ayinmu ba Gaskiya Ba Ne Ko Kuma Yana da Iyaka
  • Ka Ci Gaba da Biɗan Adalcin Jehobah
  • Bayin Jehobah Suna Son Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ka Yi Murna Cikin Adalcin Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Yi Ƙaunar Adalci Da Dukan Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Biɗan Adalci Zai Kāre Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/15 pp. 7-11

Ka Ci Gaba Da Biɗan “Adalcinsa” Da Farko

“Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.”—MAT. 6:33.

1, 2. Mene ne adalcin Allah, kuma yana bisa ga mene ne?

“KU FARA biɗan mulkinsa.” (Mat. 6:33) Shaidun Jehobah a yau sun san wannan umurni da Yesu Kristi ya ba da a Huɗubarsa a kan Dutse sosai. A kowane fannoni na rayuwarmu, muna yin ƙoƙari mu nuna cewa muna ƙaunar wannan sarautar Mulkin kuma muna son mu yi aminci da ita. Amma dole ne mu lura da sashe na biyu na wannan furcin, wato, “da adalcinsa.” Mene ne adalcin Allah, kuma mene ne yake nufi a fara biɗansa?

2 Ana iya fassara kalaman yare na asali don ‘adalci’ zuwa “shari’a” ko kuma “aminci.” Saboda haka, adalcin Allah yin gaskiya ne bisa ga mizanansa da kuma ƙa’idodinsa. A matsayin Mahalicci, Jehobah yana da ikon kafa mizani don abin da ke da kyau da marar kyau da kuma abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. (R. Yoh. 4:11) Amma, adalcin Allah ba dogon jerin dokoki da ƙa’idodi masu wuya ba ne. Maimakon haka, yana bisa mutuntakar Jehobah da kuma halinsa na adalci, wanda ya haɗa da sauran halayensa na musamman kamar su ƙaunarsa, hikima, da iko. Adalcin Allah yana da alaƙa da nufinsa da kuma ƙudurinsa. Ya ƙunshi abin da yake bukata daga waɗanda suke son su bauta masa.

3. (a) Mene ne yake nufi a fara biɗan adalcin Allah? (b) Me ya sa za mu ɗaukaka mizanan adalci na Jehobah?

3 Mene ne yake nufi a fara biɗan adalcin Allah? Yana nufin a yi nufin Allah domin a faranta masa rai. Biɗan adalcinsa ya ƙunshi yin ƙoƙari mu yi rayuwa bisa ga ƙa’idodinsa da cikakken mizanansa amma ba namu ba. (Karanta Romawa 12:2.) Wannan hanyar rayuwa ta ƙunshi dangantakarmu da Jehobah. Ba batun yin biyayya ga dokokinsa don muna tsoron horo ba ne. Maimakon haka, ƙaunarmu ga Allah tana motsa mu mu yi ƙoƙari mu faranta masa rai ta wajen ɗaukaka mizanansa, ba kafa namu ba. Mun fahimci cewa abin da ya dace mu yi ne, wato, ainihin abin da aka halicce mu mu yi. Kamar Yesu Kristi, Sarkin Mulkin Allah, dole ne mu yi ƙaunar adalci.—Ibran. 1:8, 9.

4. Me ya sa yake da muhimmanci sosai mu biɗi adalcin Allah?

4 Yana da muhimmanci mu biɗi adalcin Jehobah kuwa? Ka yi la’akari da wannan gaskiyar: Gwaji na asali a lambun Adnin ya dangana ne ga ko Adamu da Hauwa’u za su amince da ikon Jehobah na kafa mizanansa ko kuma a’a. (Far. 2:17; 3:5) Rashin yin hakan ya kawo mana wahala da mutuwa a matsayin ’ya’yansu. (Rom. 5:12) A wani sassa kuma, Kalmar Allah ta ce: ‘Wanda ya bi adalci da jinƙai rai ya ke samu, da adalci, da girma.’ (Mis. 21:21) Hakika, fara biɗan mulkin Allah yana kawo dangantaka da Jehobah da zai sa mu samu ceto.—Rom. 3:23, 24.

Haɗarin Zama Mai Adalcin Kai

5. Wane haɗari ne muke bukatan mu guji?

5 Da yake rubuta zuwa ga Kiristoci a Roma, manzo Bulus ya nanata haɗarin da dukanmu muke bukata mu guji idan za mu yi nasara wajen fara biɗan adalcin Allah. Da yake magana game da ’yan’uwansa Yahudawa, Bulus ya ce: ‘Ina shaidassu suna da himma domin Allah, amma ba bisa ga sani ba. Gama yayinda suka rasa sanin adalcin Allah, suna kuwa biɗa su kafa na kansu, ba su yi biyayya da adalcin Allah ba.’ (Rom. 10:2, 3) In ji Bulus, waɗannan masu bauta ba su fahimci adalcin Allah ba domin sun shagala ainun don su kafa nasu adalcin.a

6. Wane hali ne ya kamata mu guji, kuma me ya sa?

6 Hanya ɗaya da za mu iya faɗa cikin wannan tarkon shi ne ta wajen ɗaukan hidimarmu ga Allah a matsayin gasa, muna gwada kanmu da wasu. Wannan halin zai iya sa mu kasance da yawan gaba gaɗi game da iyawarmu. Amma, idan muka aikata hakan nan, za mu mance da adalcin Jehobah. (Gal. 6:3, 4) Muradin da ya dace don yin abu mai kyau shi ne don ƙaunarmu ga Jehobah. Duk wani ƙoƙari da muka yi don mu nuna adalcinmu zai ƙaryata da’awarmu cewa muna ƙaunarsa.—Karanta Luka 16:15.

7. Me Yesu ya ce game da matsalar adalcin kai?

7 Yesu ya damu game da waɗanda “su ke amincewa da kansu masu-adalci ne, suna maida sauran mutane wofi.” Ya yi magana a kan matsalar adalcin kai ta wajen ba da wannan misalin: “Mutum biyu suka tafi cikin haikali garin yin addu’a; ɗaya Ba-farisi ne, ɗaya kuma mai-karɓan haraji. Shi Ba-farisin ya tsaya yana addu’a da kansa haka, Ya Allah, na gode maka ba kamar sauran mutane ni ke ba, azalumai, marasa-adalci, mazinata, ko irin wannan mai-karɓan haraji. Lahadi ɗaya ni kan yi azumi biyu, ina bada zakka daga cikin dukan abin da na samu. Amma shi mai-karɓan haraji, da ya ke tsaye daga nesa, ba ya yarda ya tada ko idanunsa sama ba, amma sai ya bugi ƙirjinsa, ya ce, Ya Allah, ka yi mani jinƙai, ni mai-zunubin.” Yesu ya kammala da cewa: “Ina ce maku, Wannan mutum ya tafi gidansa baratace ne bisa ga wancan: gama dukan wanda ya ɗaukaka kansa za shi ƙasƙanta; amma wanda ya ƙasƙantadda kansa za shi ɗaukaka.”—Luk 18:9-14.

Wani Haɗari Shi Ne “Cika Yin Adalci”

8, 9. Me yake nufi mu zama masu “cika yin adalci,” kuma mene ne hakan zai iya sa mu yi?

8 An kwatanta wani haɗari da za mu guji a littafin Mai Wa’azi 7:16: ‘Kada ka cika yin adalci; kada kuwa ka cika yin hikima; don me za ka hallaka kanka?’ Marubucin Littafi Mai Tsarki da aka hure ya ci gaba, kamar yadda aya ta 20 ta nuna, ya nuna mana dalilin guje wa irin wannan halin: “Lallai babu wani mai-adalci ko ɗaya cikin duniya, wanda yana aika nagarta, ba tare da zunubi ba.” Wanda ya zama mai “cika yin adalci” yana kafa mizanan kansa na adalci kuma ya shari’anta wasu da su. Hakika, ya mance cewa ta wajen yin haka yana ɗaukaka mizanan kansa fiye da na Allah kuma ta haka ya zama mai rashin adalci a gaban Allah.

9 Zama masu “cika yin adalci” zai iya sa mu yi shakkar yadda Jehobah yake bi da al’amuransa. Ya kamata mu tuna cewa, idan muka yi shakkar adalcin shawarwarin Jehobah, mun soma saka mizananmu na adalci gaba da mizanin Jehobah. Kamar muna shari’anta Jehobah da namu mizanan sanin nagarta da mugunta ne. Amma Jehobah ne yake da ikon kafa mizani na adalci, ba mu ba!—Rom. 14:10.

10. Kamar yadda yake a batun Ayuba, mene ne zai iya sa mu shari’anci Allah?

10 Ko da yake babu wanda zai so ya yi wa Allah shari’a da gangan, amma halinmu na ajizanci zai iya sa mu yi hakan. Wannan zai iya faruwa da sauƙi sa’ad da muka ga wani abu da muke ɗauka ba shi da kyau ko kuma idan mun sha wahala. Mutumi mai adalci Ayuba ma ya yi wannan kuskuren. Da farko, an kwatanta Ayuba kamar “kamili ne mai-adilci, yana tsoron Allah, yana kuwa bada baya ga mugunta.” (Ayu. 1:1) Duk da haka Ayuba ya sha masifu masu yawa da a ganinsa ba su dace ba. Wannan ya sa Ayuba, “ya maida kansa ya fi Allah gaskiya.” (Ayu. 32:1, 2) Ayuba yana bukata a daidaita ra’ayinsa. Saboda haka, bai kamata mu yi mamaki ba idan a wasu lokatai mun samu kanmu a irin wannan yanayin. Idan hakan ya faru, mene ne zai iya taimaka mana mu daidaita ra’ayinmu?

Ba Kowane Lokaci Ba Ne Muke da Cikakken Labarin

11, 12. (a) Idan muna ganin cewa akwai abin da bai dace ba, mene ne muke bukatan mu tuna? (b) Me ya sa wani zai ji cewa kwatancin Yesu na ma’aikata a garkar inabi ya nuna wani abu da ba daidai ba ne?

11 Abu na farko da za mu tuna shi ne cewa ba a kowane lokaci ba ne muke da cikakken labarin. Hakan yake a batun Ayuba. Bai san cewa mala’iku ’ya’yan Allah a sama sun yi taro inda Shaiɗan ya yi masa tuhumar ƙarya ba. (Ayu. 1:7-12; 2:1-6) Ayuba bai sani ba cewa Shaiɗan ne ainihin tushen matsalolinsa. A gaske, ba za mu kasance da tabbaci ba cewa Ayuba ya san ko wane ne Shaiɗan! Saboda haka, ya yi tsammani cewa Allah ne ya haddasa matsalolinsa. Hakika, yana da sauƙi mu yi kammalawa da ba daidai ba sa’ad da ba mu san cikakken labarin ba.

12 Alal misali, ka yi la’akari da kwatancin Yesu na ma’aikata a cikin garkar inabi. (Karanta Matta 20:8-16.) A nan Yesu ya kwatanta maigida wanda ya biya dukan waɗanda suke yi masa aiki yawan albashi ɗaya, ko sun yi aiki dukan rana ko kuma sa’a guda kawai. Yaya kake ji game da hakan? Hakan ya yi daidai ne? Wataƙila kana jin tausayin waɗanda suka yi aiki dukan yini a cikin rana mai zafi. Hakika sun cancanci a biya su fiye da sauran! Bisa wannan kammalawar, ana iya ɗaukan cewa maigidan marar ƙauna ne kuma ba mai gaskiya ba ne. Ana iya ɗaukan amsar da ya ba waɗannan ma’aikata masu yin gunaguni kamar yana ɓata ikonsa ne. Amma muna da cikakken labarin ne?

13. Wane ra’ayi ne kuma za mu iya kasance da shi game da kwatancin Yesu na ma’aikata a cikin gonar inabi?

13 Bari mu bincika wannan kwatanci daga wani ra’ayi. Babu shakka, maigida da ke cikin wannan kwatanci ya fahimci cewa dukan waɗannan maza suna bukatan su ciyar da iyalansu. A zamanin Yesu, ana biyan masu aiki a gona kowace rana. Iyalansu sun dogara ga kuɗin da ake biya kowace rana. Saboda haka, ka yi tunanin yanayin waɗanda maigidan ya same su a kusan ƙarshen ranar kuma don haka sun yi aiki na awa guda kawai. Wataƙila ba za su iya ciyar da iyalinsu ba da kuɗin awa guda; duk da haka, suna shirye su yi aiki kuma suna jira dukan rana don su samu aiki. (Mat. 20:1-7) Ba laifinsu ba ne da ba su yi aiki ba dukan rana. Babu abin da ya nuna cewa sun ƙi yin aiki da ganga ne. A ce ka jira dukan rana, ka san cewa wasu sun dangana ga kuɗin da za ka samu a wannan ranar. Za ka yi farin cikin samun wani aiki, kuma za ka yi mamakin samun isashen kuɗin ciyar da iyalinka!

14. Wane darasi mai kyau ne muka koya daga kwatanci na garkar inabi?

14 Yanzu bari mu sake yin la’akari da ayyukan maigidan. Bai biya wannan ma’aikacin fiye da wancan ba. Maimakon hakan, ya bi da dukansu a matsayin waɗanda suke da ikon samun kuɗin tallafa wa kansu da iyalansu. Duk da cewa akwai ma’aikata masu yawa, maigidan bai yi amfani da yanayin don ya biya su kuɗin da bai kai na yini ba. Dukan ma’aikatansa sun koma gida da isassun kuɗi don su ciyar da iyalansu. Yin la’akari da waɗannan ƙarin bayani zai iya canja ra’ayinmu game da ayyukansa. Shawararsa mai kyau ne ba ɓata ikonsa ba. Wane darasi ne za mu iya koya? Yin la’akari da wasu bayanan za su iya sa mu kammala yadda bai dace ba. Hakika, wannan almara ta nanata cewa adalcin Allah ya fi kyau, kuma hakan bai dangana kaɗai ga ƙa’idodi na doka ba da kuma abin da ’yan Adam suka cancanta.

Wataƙila Ra’ayinmu ba Gaskiya Ba Ne Ko Kuma Yana da Iyaka

15. Me ya sa ra’ayinmu game da adalci zai iya kasance ba gaskiya ba ko kuma yana da iyaka?

15 Abu na biyu da za mu tuna sa’ad da muka fuskanci yanayi da ya yi kamar ba daidai ba ne shi ne cewa wataƙila ra’ayinmu ba gaskiya ba ne ko kuma yana da iyaka. Mai yiwuwa ba gaskiya ba ne saboda ajizanci, wariya, ko kuma al’ada. Yana da iyaka kuma domin ba ma iya sanin muradi da kuma ainihin abin da ke cikin zuciyar mutane. Akasin hakan, Jehobah da Yesu ba su da irin wannan iyaka.—Mis. 24:12; Mat. 9:4; Luk 5:22.

16, 17. Me ya sa Jehobah bai tilasta bin dokarsa game da zina a lokacin da Dauda ya yi zina da Beth-sheba ba?

16 Bari mu bincika labarin zina da Dauda ya yi da Bath-sheba. (2 Sam. 11:2-5) Bisa Dokar Musa, sun cancanci a kashe su. (Lev. 20:10; K. Sha 22:22) Ko da yake Jehobah ya yi musu horo, amma bai tilasta bin dokarsa ba. Jehobah ya yi abin da bai dace ba ne? Ya nuna son kai ne ga Dauda kuma ya ɓata mizaninsa na adalci? Wasu masu karatun Littafi Mai Tsarki suna ganin ya yi hakan.

17 Amma, Jehobah ne ya ba da wannan doka game da zina ga alƙalai ajizai, waɗanda ba sa iya sanin zukata. Duk da kasawarsu, wannan dokar ta sa ya yiwu su ci gaba da yin hukuncinsu. A wata sassa kuma, Jehobah yana iya sanin zukata. (Far. 18:25; 1 Laba. 29:17) Saboda haka, bai kamata mu yi tsammani cewa Jehobah zai bi dokar da ya kafa don alƙalai ajizai ba. Idan ya yi hakan, ba zai zama kamar tilasta wa wani mai gani sosai ya saka tabarau da aka ƙera don a daidaita idanun waɗanda suke ciwon ido ba? Jehobah zai iya sanin zukatan Dauda da Bath-sheba kuma ya ga cewa sun tuba da gaske. Yin la’akari da wannan, ya yi musu shari’a da ya dace, bisa jin ƙai da ƙauna.

Ka Ci Gaba da Biɗan Adalcin Jehobah

18, 19. Mene ne zai taimaka mana kada mu taɓa shari’anta Jehobah da namu mizanan adalci?

18 Saboda haka, idan a wani lokaci mun ga wani abu da muke ji ba daidai ba da Jehobah ya yi, ko da mun karanta shi a cikin labarin Littafi Mai Tsarki ko kuma ya faru a rayuwarmu, kada mu shari’anta Allah da namu mizanai na adalci. Mu tuna cewa ba mu da cikakken labari kuma wataƙila ra’ayinmu ba gaskiya ba ne ko kuma yana da iyaka. Kada ka manta cewa “fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah.” (Yaƙ. 1:19, 20) Ta wannan hanyar, zuciyarmu ba za ta taɓa yin “gunaguni da Ubangiji” ba.—Mis. 19:3.

19 Kamar Yesu, bari a koyaushe mu fahimci cewa Jehobah ne kaɗai yake da ikon kafa mizani don abin da yake da adalci da kuma abin da yake da kyau. (Mar. 10:17, 18) Ka yi ƙoƙari ka samu cikakken “sani” na mizanansa. (Rom. 10:2; 2 Tim. 3:7) Ta wajen amincewa da wannan da kuma yin nufin Jehobah a rayuwarmu, za mu nuna cewa muna fara biɗan “adalcinsa.”—Mat. 6:33.

[Hasiya]

a Wani masani ya faɗa cewa, kalmar yare na asali da aka fassara “kafa” tana nufin ‘kafa abin tunawa.’ Saboda haka, waɗannan Yahudawan suna kafa abin tunawa na alama don yabon kansu ne ba na Allah ba.

Ka Tuna?

• Me ya sa yake da muhimmanci mu biɗi adalcin Jehobah?

• Waɗanne haɗarurruka biyu ne muke bukata mu guji?

• Ta yaya za mu fara biɗan adalcin Allah?

[Hoton da ke shafi na 9]

Wane darasi ne muka koya daga kwatancin Yesu na maza biyu da suka yi addu’a a cikin haikali?

[Hoton da ke shafi na 10]

Ya dace ne a biya ma’aikata da suka yi aiki na awa guda daidai da waɗanda suka yi aiki dukan rana?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba