Sa’ad da Aka Yi Maka Laifi
YAWANCIN mutane sukan ce wai ramuwa yana da daɗi. Hakan na faruwa ne domin dole ne mu yi fushi sa’ad da aka yi mana laifi ko kuma aka cuce mu a wata hanya. Azancinmu da aka haife mu da shi ya nuna mana cewa ya dace a daidaita rashin gaskiyar. Tambayar ita ce, ta yaya?
Babu shakka, da akwai, laifofi iri-iri, kamar mari, bangaje, ko kuma zagi, zalunci, fashi, da sauran su. Yaya ka ke ji idan ka fuskanci irin waɗannan gwajin? Yawancin mutane a yau sukan ce, ‘Zan sa su biya tara!’
A Amirka, yawancin daliɓan makarantar sakandare sukan kai karan malaminsu da ya hore su. In ji Brenda Mitchell, shugabar Ƙungiyar Malamai a New Orleans, “Idan an kai karan malamin, an riga an ɓata sunan sa.” Ko da an tabbatar cewa zargin ba hakan ba ne, ɓacin sunan yana nan.
A wurin aiki, yawancin waɗanda aka sallama daga wurin aiki sukan rama ta ɓata abubuwan da aka saka cikin kwamfutar kamfanin. Wasu sukan saci asirin kamfanin sai su sayar da shi. Ƙari ga satan abubuwan da ke cikin kwamfuta, “wasu sukan saci kayayyakin kamfanin,” in ji The New York Times. Don magance ramuwa, yawancin kamfani sukan sa masu tsaro su raka ma’aikatan da aka sallama zuwa ofishinsa, su jira shi ya kwashe kayansa, sai su raka shi har sai ya fita daga kamfanin.
Ramawa da ya fi faruwa shi ne daga waɗanda suke kusa da mu sosai, abokai da iyalanmu. Zafin baƙar magana takan sa a rama da kalamai mara kyau. Idan abokinka ya yi maka magana da furci mara daɗi, za ka mayar masa ma da kalamai mara daɗi? Idan danginka ya yi maka laifi, kana neman hanyar da za ka rama? Yana da sauƙi mu aikata hakan idan wanda ya yi mana laifin yana kusa da mu!
Ramuwa Wauta ce
Sau da yawa, waɗanda suke son ramawa sukan yi hakan ne don su sauƙaƙa zafin laifin da aka yi musu. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana cewa sa’ad da ’ya’yan Yakubu uban iyalin Ibraniyawa suka ji cewa Shechem wani Ba-kan’aniya, ya ɓata ’yar’uwarsu Dinah, “ransu ya ɓāci, suka hasala ƙwarai kuma.” (Farawa 34:1-7) Don su rama abin da aka yi wa ’yar’uwarsu, yaran Yaƙubu biyu suka gama kai game da Shechem da iyalansa. Da wayo, Simeon da Levi suka shiga ƙasar Kana kuma suka kashe dukan mazajen, haɗe da Shechem.—Farawa 34:13-27.
Shin dukan jinin da aka zubar ya daidaita zancen? Sa’ad da Yuƙub ya ji abin da yayansa suka yi, sai ya ce musu: “Kun wahalshe ni, da kun sa in zama abin ƙyama a cikin mazaunan ƙasan, . . . za su tar mani, su buga ni: zan hallaka kuwa, da ni da gidana.” (Farawa 34:30) Maimakon ya magance matsalar, fushin da suka yi ya jawo sakamako mara kyau; iyalan Yaƙub suka soma yin tsaro don kada maƙwabtansu su mamaye su. Babu shakka don ya sa su magance wannan matsalar, Allah ya umurce Yaƙub ya ƙaura da iyalinsa zuwa Bethel.—Farawa 35:1, 5.
Waɗannan abubuwan da suka faru bayan da aka ɓata Dinah ya koya mana darassi mai kyau. Ramawa yakan kai ga ƙarin ramuwa, kuma akan ci gaba da yin hakan. Hakan ya yi daidai da karin maganar ’yan Jamus: Ramuwa ba ta ƙarewa.
Ci gaba da Ramawa
Bai dace mu dinga neman rama laifofin da mutane suka yi mana ba. Littafin nan Forgiveness—How to Make Peace With Your Past and Get On With Your Life ya ce: “Fushi yakan ci rai. Yana ɗaukan lokaci sa’ad da kake yin tunani game da abin da ya faru, ka dinga yin zage-zage a cikin zuciya, kana neman yadda za ka rama.” Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana, “kishi ruɓar ƙasussuwa ne.”—Misalai 14:30.
Hakika, mutum ba zai iya samun farin ciki ba idan yana cike da fushi. Wani mai bayani ya lura cewa: “Idan kana tunani cewa ‘ramuwa na da daɗi,’ ka kalli fuskar waɗanda suke fushi a shekaru da yawa.”
Ka yi la’akari da abin da ke faruwa a wuraren da ake yawan yin faɗace-faɗacen ƙabila da na addini. Sau da yawa, kisa ɗaya yakan jawo wani, wanda yake ci gaba da jawo ƙiyayya da mutuwa. Alal misali, sa’ad da fashewar bam ɗin ’yan ta’adda ya kashe matasa goma sha takwas, wata mata da take kuka ta ce: “Za mu rama sau dubu!” Da hakan, mugunta yana karuwa, kuma mutane da yawa suna saƙa hannu a tarzomar.
“Ido Domin Ido”
Wasu sukan yi tunanin cewa Littafi Mai Tsarki ya goyi bayan halin ramawarsu. Sukan ce, “Ba Littafi Mai Tsarki yi magana game da ‘ido domin ido, haƙori domin haƙori’ ba?” (Levitikus 24:20) Zai yi kamar dokar “ido domin ido” yana yin magana game da ramuwa. Amma dai, an ƙafa ta ne don ta sarrafa ramuwa. Ta yaya?
Idan Ba’isra’ila ya zalunci wani ɗan’uwansa Ba’isra’ila kuma ya ɓata idonsa, dokar ta aminci da hukunci. Amma dai, ba hakin wanda aka zalunci ba ne ya ɗauki mataki ko kuma ɗaya cikin danginsa. Dokar tana bukatar ya kai zancen wurin hukuma, alƙalan da aka naɗa, don a daidaita zancen. Sanin cewa za a hukunta wanda ya yi laifi ko aikata laifi ga wani yakan hana ramuwa. Amma akwai waɗansu al’amura game da batun.
Gab da kafa dokar ramuwa, Jehobah Allah ya gaya wa al’ummar Isra’ila ta Musa cewa: “Ba za ka ƙi ɗan’uwanka cikin zuciyarka ba. . . . Ba za ka ɗauka ma kanka fansa, ba kuwa za ka yi nukuran” ba. (Levitukus 19:17, 18) Ya dace a fahimci dokar “ido domin ido, haƙori domin haƙori” ta kalaman Dokar alkawari, wanda Yesu ya bayyana da kalma ɗaya: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka” da “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:37-40) Menene ya kamata Kiristoci na gaskiye su yi idan sun fuskanci rashin gaskiya?
Ka bi Hanyar Salama
Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Jehobah kamar “Allah na salama” kuma ya umurci masu bautarsa su ‘yi nagarta, su nemi salama.’ (Ibraniyawa 13:20; 1 Bitrus 3:11) Amma neman salama yan yiwuwa kuwa?
Sa’ad da yake duniya, an tofa wa Yesu miyau, an doke shi, maƙiyinsa sun kuma tsananta shi, abokinsa ya ci amanarsa, kuma almajiransa sun yasar da shi. (Matta 26:48-50; 27:27-31) Menene ya yi? Manzo Bitrus ya rubuta, “Sa’anda aka zage shi, ba ya mayar da zagi ba; sa’anda ya sha azaba, ba ya yi kashedi ba; amma ya danƙa maganatasa ga wanda ke yin shari’a mai-adalci.”—1 Bitrus 2:23.
“Kristi kuma ya sha azaba dominku,” Bitrus ya bayyana “yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.” (1 Bitrus 2:21) An ƙarfafa Kiristoci su yi koyi da Yesu, haɗe da rashin gaskiya da ya fuskanta. Game da wannan, Yesu da kansa ya ce a Huɗuba akan dutse: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a; Domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama.”—Matta 5:44, 45.
Menene waɗanda suke yin koyi da ƙaunar Kristi suke yi idan an yi musu laifi? Misalai 19:11 ya ce: “Hankalin mutum ya kan sa fushinsa shi yi jinkiri: Daraja ne kuwa a gareshi shi ƙyale laifi.” Sukan kuma saka wannan umurnin a cikin zuciya: “Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.” (Romawa 12:21) Hakan ya bambanta da halin ramuwa da ke duniya a yau! Ƙaunar Kiristoci na gaskiya zai iya taimaka mana mu magance halin ramawa kuma za mu “ƙyale laifi” saboda ƙauna “ba ta yin nukura.”—1 Korintiyawa 13:5.
Hakan yana nufin ne cewa idan an yi mana laifi, mu haƙura kawai? A’a! Sa’ad da Bulus ya ce “ku rinjayi mugunta da nagarta,” ba ya nufin cewa Kiristoci su so a wulakanta su ba. Akasin hakan, idan an kai mana farmaki, muna da hujjar tsare kanmu. Idan an wulakanta ka ko dukiyarka, wataƙila za ka so ka kira ’yan sanda. Idan matsalar ya shafi wani a wurin aiki ko a makaranta, akwai hukumomi da za mu iya kai kara wurinsu.—Romawa 13:3, 4.
Duk da haka, ya dace mu san cewa yana da wuya a yi shari’a daidai wa daida a wannan zamanin. Hakika, yawanci sun ɓatar da dukan rayuwarsu suna neman shari’a, amma don ba su same ta ba suka cika da fushi.
Shaiɗan yana son ya ga mutane suna ramako da ƙiyayya. (1 Yohanna 3:7, 8) Ya fi dacewa mu bi kalaman nan da ke cikin Littafi Mai Tsarki: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce wa fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” (Romawa 12:19) Ta ƙyale Allah ya ɗauki mataki, za mu tsare kanmu daga azaba, fushi, da nuna ƙarfi.—Misalai 3:3-6.
[Bayanin da ke shafi na 22]
“Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka” da “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka”
[Hotunan da ke shafi na 23]
Ƙauna “ba ta yin nukura.”—1 Korintiyawa 13:5