Kiristoci Suna Da Begen Rai Na Har Abada A Duniya ne?
“[Allah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.”—R. YOH. 21:4.
1, 2. Yaya muka san cewa Yahudawa da yawa na ƙarni na farko suna da begen rai na har abada a duniya?
WANI saurayi mai arziki ya sheƙo a guje zuwa wajen Yesu ya durƙusa a gabansa, kuma ya tambaye shi: “Malam managarci, me zan yi domin in gāji rai na har abada?” (Mar. 10:17) Saurayin yana tambaya ne game da samun rai na har abada, amma a ina? Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, ƙarnuka da suka wuce, Allah ya ba Yahudawa begen tashin matattu da kuma rai madawwami a duniya. Har ila, Yahudawa da yawa na ƙarni na farko suna da wannan begen.
2 Babu shakka, Martha abokiyar Yesu tana nufin tashin matattu a duniya sa’ad da ta ce game da ɗan’uwanta da ya rasu: “Na sani za ya tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta ƙarshe.” (Yoh. 11:24) Hakika, Sadukiyawa na lokacin ba su gaskata da tashin matattu ba. (Mar. 12:18) Amma, a cikin littafinsa, Judaism in the First Centuries of the Christian Era, George Foot Moore ya ce: “Rubuce-rubuce . . . na ƙarnuka na biyu ko na farko kafin zamaninmu sun nuna cewa mutane da yawa sun gaskata cewa a wani lokaci za a ta da waɗanda suka mutu a dā daga matattu a duniya.” Mawadacin da ya tuntuɓi Yesu, yana son ya samu rai na har abada a duniya ne.
3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A yau, addinai da yawa da masana na Littafi Mai Tsarki sun ce Yesu bai koyar da begen yin rayuwa a duniya har abada ba. Yawancin mutane suna da begen cewa sa’ad da suka mutu za su ci gaba da rayuwa a duniya ta ruhu. Saboda haka, sa’ad da masu karanta Nassosin Helenanci na Kirista suka karanta furcin nan “rai na har abada,” mutane da yawa suna tunanin cewa yana nufin rai a sama. Hakan gaskiya ne? Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya yi maganar rai na har abada? Menene almajiransa suka yi imani da shi? Nassosin Helenanci na Kirista ya koyar ne cewa za mu iya yin rayuwa har abada a duniya?
Rai na Har Abada a “Sabon Zamani”
4. Menene zai faru a “sabon zamani”?
4 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa za a ta da Kiristoci shafaffu don su yi sarauta bisa duniya daga sama. (Luk 12:32; R. Yoh. 5:9, 10; 14:1-3) Amma, sa’ad da Yesu ya yi magana game da rai na har abada, ba a koyaushe ba ne yake nufin wannan rukunin kawai ba. Ka yi la’akari da abin da ya gaya wa almajiransa bayan wannan saurayi mai arziki ya tafi yana baƙin ciki sa’ad da aka gaya masa ya bar dukan dukiyarsa ya zama mabiyin Kristi. (Karanta Matta 19:28, 29; Littafi Mai Tsarki.) Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa za su kasance cikin waɗanda za su yi sarauta kuma su yi wa “kabilan goma sha biyu na Isra’ila” shari’a, wato, dukan ’yan adam da ba sa cikin waɗanda za su yi sarauta a sama. (1 Kor. 6:2) Ya kuma yi maganar lada ga “kowanene” da ya biyo shi. Irin waɗannan mutane su ma za su “gāji rai na har abada.” Dukan waɗannan za su faru a “sabon zamani.”
5. Yaya za ka ba da ma’anar “sabon zamani”?
5 Menene Yesu yake nufi da “sabon zamani”? An fassara furcin nan zuwa “sabuwar duniya” a juyin The Bible—An American Translation. An fassara shi “sa’ad da aka sabonta dukan abubuwa” a cikin The Jerusalem Bible, kuma “sabonta dukan abubuwa” a juyin The Holy Bible—New International Version. Tun da yake Yesu ya yi amfani da furcin nan ba tare da faɗin abin da yake nufi ba, babu shakka yana nuni ne ga begen Yahudawa tun ƙarnuka da yawa. Za a yi sabon yanayi a duniya, don abubuwa su kasance yadda suke a cikin lambun Adnin kafin Adamu da Hauwa’u su yi zunubi. Sabon zamani zai cika alkawarin Allah na halittar “sabobin sammai da sabuwar duniya.”—Isha. 65:17.
6. Kwatancin tumaki da awaki ya koya mana menene game da begen rai na har abada?
6 Yesu ya sake ambata rai na har abada a jawabinsa game da cikar zamani. (Mat. 24:1-3) Ya ce: “Sa’anda Ɗan mutum za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajassa: a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi ya kan rarraba tumaki da awaki.” Waɗanda aka yi musu hukunci mai tsanani “za su tafi cikin hukunci na har abada: amma masu-adalci cikin rai na har abada.” “Masu-adalci” da suka samu rai na har abada su ne waɗanda suka nuna aminci wajen tallafa wa ‘’yan’uwan’ Kristi da aka shafa da ruhu. (Mat. 25:31-34, 40, 41, 45, 46) Tun da yake an zaɓi shafaffu su yi sarauta a Mulkin sama, dole ne “masu-adalci” su zama talakawan duniya na wannan Mulkin. Littafi Mai Tsarki ya annabta: “[Sarkin Jehobah] za ya yi mulki daga teku zuwa teku, daga Kogin har zuwa iyakan duniya.” (Zab. 72:8) Waɗannan talakawan za su more rai na har abada a duniya.
Menene Linjila ta Yohanna ta Nuna?
7, 8. Yesu ya yi magana ga Nikodimu game da waɗanne bege biyu?
7 Kamar yadda aka rubuta a Linjilar Matta, Markus, da Luka, Yesu ya yi amfani da furcin nan “rai na har abada” a lokatai da aka ambata ɗazu. Linjila ta Yohanna ta yi ƙaulin kalaman Yesu game da rayuwa har abada sau sha bakwai. Bari mu bincika wasu daga cikinsu don mu ga abin da Yesu ya ce game da begen rai na har abada a duniya.
8 In ji Yohanna, Yesu ya soma tattaunawa game da rai na har abada ne da wani Bafarisi mai suna Nikodimu. Ya gaya wa Nikodimu: “In ba a haifi mutum daga cikin ruwa da Ruhu ba, ba shi da iko ya shiga cikin mulkin Allah.” Dole ne a sake ‘haifan’ waɗanda za su shiga cikin Mulki na sama. (Yoh. 3:3-5) Ba a nan kawai Yesu ya tsaya ba. Bayan haka, ya yi maganar begen da dukan ’yan adam za su iya samu. (Karanta Yohanna 3:16.) Yesu yana nuni ga begen rai na har abada ga mabiyansa shafaffu a sama da kuma wasu a duniya.
9. Wane bege ne Yesu ya tattauna da mace Basamariya?
9 Bayan ya tattauna da Nikodimu a Urushalima, Yesu ya yi tafiya zuwa arewacin Galili. A hanya, ya sadu da wata mata a rijiyar Yakubu a birnin Sukar a Samariya. Ya gaya mata: “Dukan wanda zai sha daga cikin ruwan da ni zan ba shi, ba zai ji ƙishi har abada ba; amma ruwan da zan ba shi zai zama rijiyar ruwa a cikinsa, yana ɓulɓula zuwa rai na har abada.” (Yoh. 4:5, 6, 14) Wannan ruwa yana wakiltar tanadin Allah na mai da rai na har abada ga dukan ’yan adam, har da waɗanda za su yi rayuwa a duniya. A littafin Ru’ya ta Yohanna, an kwatanta Allah yana cewa: “Wanda yake jin ƙishi, zan ba shi daga cikin maɓulɓulan ruwa na rai kyauta.” (R. Yoh. 21:5, 6; 22:17) Da haka, Yesu ya tattauna da mace Basamariya game da rai na har abada ba kawai na shafaffu da za su yi gadōn Mulki ba amma har da na ’yan adam masu imani da suke da begen zama a duniya.
10. Bayan ya warkar da wani mutumi a tafkin Baitasda, menene Yesu ya gaya wa ’yan hamayya na addinai game da rai na har abada?
10 A shekara ta gaba, Yesu ya sake komawa Urushalima. A wajen, ya warkar da wani mutumi a tafkin Baitasda. Yesu ya bayyana wa Yahudawan da suke hamayya da abin da ya yi, cewa: “Ɗan ba shi iya yin kome don kansa ba, sai abin da ya ga Uban yana yi; gama dukan kome da shi yake yi, waɗannan kuma hakanan Ɗan yana yi.” Bayan ya gaya musu cewa Uban “dukan shari’a ya bayas ga Ɗan,” Yesu ya ce: “Wanda yana jin maganata, yana kuwa bada gaskiya ga wanda ya aiko ni, yana da rai na har abada.” Yesu ya kuma ce: “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma: waɗanda sun yi nagarta, su fito zuwa tashi na rai; waɗanda sun yi mugunta, zuwa tashi na shari’a.” (Yoh. 5:1-9, 19, 22, 24-29) Yesu yana gaya wa Yahudawan da suke hamayya da shi cewa, shi ne Allah ya naɗa ya cika begen Yahudawa na rai na har abada a duniya kuma zai yi hakan ta wajen ta da matattu.
11. Yaya muka san cewa abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 6:48-51 ya ƙunshi begen rai na har abada a duniya?
11 A Galili, dubban mutanen da suke son gurasar da Yesu ya yi tanadinta ta hanyar mu’ujiza suka soma bin shi. Yesu ya yi musu maganar wata irin gurasa, wato, “gurasa ta rai.” (Karanta Yohanna 6:40, 48-51.) Ya ce: “Gurasa wadda zan bayar namana ne.” Yesu ya ba da ransa ga waɗanda za su yi sarauta da shi a Mulkin sama da kuma “sabili da ran duniya” don ya ceci ’yan adam. “Idan kowane mutum ya ci wannan gurasa,” wato, ya ba da gaskiya ga ikon fansa na hadayar Yesu, zai samu begen rai na har abada. Hakika, yin ‘rayuwa har abada’ ya ƙunshi begen rai madawwami a duniya a lokacin sarautar Almasihu da Yahudawa suke da shi tun da daɗewa.
12. Yesu yana maganar wane bege ne sa’ad da ya gaya wa ’yan hamayya cewa ‘zai ba da rai na har abada ga tumakinsa’?
12 Daga baya, sa’ad da ake Idin Buɗewa a Urushalima, Yesu ya gaya wa masu hamayya da shi: “Ba ku gaskanta ba, domin ku ba na cikin tumakina ba ne. Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna biyona kuma. Ina ba su rai na har abada.” (Yohanna 10:26-28) Yesu yana magana ne kawai game da rai a sama, ko kuwa har da rai na har abada cikin aljanna a duniya? Ba da daɗewa ba, Yesu ya ƙarfafa mabiyansa da waɗannan kalmomi: “Ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro; gama Ubanku yana jin daɗi shi ba ku mulkin.” (Luk 12:32) Har ila, a lokacin Idin Buɗewar, Yesu ya ce: “Ina da waɗansu tumaki kuma, waɗanda ba na wannan garke ba ne: su kuma dole zan kawo.” (Yoh. 10:16) Saboda haka, sa’ad da Yesu ya yi magana da waɗannan ’yan hamayya, kalamansa sun haɗa da begen rai a sama don “ƙaramin garke” da kuma begen rai na har abada a duniya don miliyoyin “waɗansu tumaki.”
Begen da Ba Ya Bukatar Bayani
13. Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Za ka kasance tare da ni a Aljanna”?
13 Sa’ad da yake shan azaba a kan gungumen azaba, Yesu ya ba da tabbaci da ba za a iya ƙaryata ba game da begen ’yan adam. Wani mai laifi da aka kafa kusa da shi ya roƙi Yesu ya tuna da shi sa’ad da Yesu ya shiga mulkinsa. Yesu ya yi masa alkawari: “A gaskiya ina ce maka a yau, za ka kasance tare da ni a Aljanna.” (Luk 23:43, NW) Tun da yake wannan mutumin babu shakka Bayahude ne, ba ya bukatar bayani game da Aljanna. Ya san game da begen rai na har abada a duniya a nan gaba.
14. (a) Menene ya nuna cewa maganar bege na samaniya ya yi wa manzannin wuyar fahimta? (b) A wane lokaci ne mabiyan Yesu suka fahimci bege na samaniya sosai?
14 Abin da ke bukatar bayani shi ne maganar da Yesu ya yi game da bege na samaniya. Sa’ad da ya gaya wa almajiransa cewa zai tafi sama ya shirya musu wuri, ba su fahimci abin da yake nufi ba. (Karanta Yohanna 14:2-5.) Daga baya ya gaya musu: “Ina da sauran zance da yawa da zan yi maku tukuna, amma ba ku iya ku ɗauke su yanzu ba. Amma sa’adda shi, Ruhu na gaskiya, ya taho, zai bishe ku cikin dukan gaskiya.” (Yoh. 16:12, 13) Sai bayan Fentakos na shekara ta 33 K.Z., sa’ad da aka shafa su da ruhun Allah don su zama sarakuna masu jiran gado ne mabiyan Yesu suka fahimci cewa kursiyinsu zai kasance a sama. (1 Kor. 15:49; Kol. 1:5; 1 Bit. 1:3, 4) Begen gado na samaniya bayyanuwa ce, kuma ya zama abin da hurarrun wasiƙu na Nassosin Helenanci na Kirista suka mai da wa hankali. Amma waɗannan wasiƙun sun sake tabbatar da begen ’yan adam na samun rai na har abada a duniya ne?
Menene Hurarrun Wasiƙu Suka Ce?
15, 16. Yaya hurarriyar wasiƙa zuwa ga Ibraniyawa da kuma kalaman Bitrus suka yi nuni ga begen rai na har abada a duniya?
15 A cikin wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa, manzo Bulus ya yi magana da ’yan’uwansa masu bi a matsayin “’yan’uwa tsarkaka, masu-tarayya na kira ba-samaniya.” Amma bisa ga yare na asali, wato, Helenanci, ya kuma faɗi cewa Allah ya ƙasƙantar da “duniya mai zuwa da mutane ke cikinta” a ƙarƙashin Yesu. (Ibran. 2:3, 5, NW; 3:1) A cikin Nassosin Helenanci na Kirista, kalma ta asali don ‘duniya mai zuwa da mutane ke cikinta’ a koyaushe tana nuni ne ga duniyar da ke cike da mutane. Saboda haka, “duniya mai zuwa da mutane ke cikinta,” tsarin abubuwa ne na nan gaba a duniya a ƙarƙashin sarautar Yesu Kristi. A lokacin, Yesu zai cika alkawarin Allah: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zab. 37:29.
16 An hure manzo Bitrus ya rubuta yadda rayuwar ’yan adam za ta kasance a nan gaba. Ya rubuta: “Sammai da suke yanzu, da duniya kuma, bisa ga wannan magana kanta an tanaje su domin wuta, ajiyayyu zuwa ranar shari’a da halakar mutane masu-fajirci.” (2 Bit. 3:7) Menene zai canja sammai na gwamnati da kuma mugun tsarin ’yan adam da muke ciki yanzu? (Karanta 2 Bitrus 3:13.) “Sabobin sammai” za su canja su, wato, Mulkin Almasihu na Allah, da kuma “sabuwar duniya” wato, al’ummar ’yan adam masu adalci, masu bauta ta gaskiya.
17. Yaya aka kwatanta begen ’yan adam a Ru’ya ta Yohanna 21:1-4?
17 Littafi na ƙarshe a cikin Littafi Mai Tsarki ya motsa zuciyarmu da wahayinsa inda za a mai da ’yan adam zuwa kamiltattu. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.) Hakan shi ne begen mutane masu bangaskiya tun lokacin da mutum na farko ya yi zunubi a lambun Adnin. Mutane masu adalci za su zauna cikin Aljanna a duniya har abada ba tare da yin tsufa ba. Wannan begen yana bisa Nassosin Ibrananci da kuma Nassosin Helenanci na Kirista, kuma ya ci gaba da ƙarfafa bayin Jehobah masu aminci har zuwa yau.—R. Yoh. 22:1, 2.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene Yesu yake nufi da “sabon zamani”?
• Yesu ya yi wa Nikodimu magana game da menene?
• Wane alkawari ne Yesu ya yi wa mai laifin da aka kafa kusa da shi?
• Yaya wasiƙar da aka rubuta wa Ibraniyawa da kuma kalaman Bitrus suka tabbatar da begen rai na har abada?
[Hotunan da ke shafi na 8]
Masu kama da tumaki za su samu rai na har abada a duniya
[Hotunan da ke shafi na 10]
Yesu ya yi magana ga wasu game da rai na har abada