Ka Nace Bi Zuwa Kamala Don “Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”
“Mu nace bi zuwa kamala.”—IBRAN. 6:1.
1, 2. Wane zarafi na ‘guduwa zuwa duwatsu’ ne Kiristoci na ƙarfi na farko a Urushalima da Yahudiya suka samu?
SA’AD da Yesu yake duniya, almajiransa suka zo wajensa suka tambaye shi: “Mi ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” Cikawa na farko na annabcin da Yesu ya ba su ya faru ne a ƙarni na farko. Yesu ya ambata wata aukuwar da ba ta taɓa faruwa ba da za ta nuna alamar cewa ƙarshe ya yi kusa sosai. Da zarar sun ga hakan na faruwa, “waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.” (Mat. 24:1-3, 15-22) Almajiran Yesu za su fahimci alamar kuma su aikata bisa umurninsa kuwa?
2 Bayan kusan shekara talatin, a shekara ta 61 A.Z., manzo Bulus ya rubuta saƙo da ya bayyana abubuwa sarai ga Kiristoci Ibraniyawa da ke zaune a Urushalima da kewaye. Ba tare da sanin Bulus da ’yan’uwansa masu bi ba, shekara biyar ce kawai ta rage su ga alamar somawar “ƙunci mai-girma.” (Mat. 24:21) A shekara ta 66 A.Z., Cestius Gallus tare da rundunar Romawa sun so su kame Urushalima. Amma sai suka janye ba zato ba tsammani, kuma hakan ya ba Kiristoci zarafin su tsira.
3. Wane gargaɗi ne Bulus ya ba Kiristoci Ibraniyawa, kuma me ya sa?
3 Waɗannan Kiristocin suna bukatar sani da fahimi na ruhaniya don su fahimci cewa abubuwan da ke faruwa cikar kalmomin Yesu ne kuma su gudu. Amma, wasu sun zama “masu nauyin ji.” Sun zama kamar jarirai na ruhaniya da ke bukatar “madara.” (Karanta Ibraniyawa 5:11-13.) Wasu da suka yi shekaru suna bin hanyar gaskiya suna nuna alamar yin “ridda daga Allah mai-rai.” (Ibran. 3:12) Wasu sun “saba” da ƙin zuwa taron Kirista a daidai lokacin da wannan muguwar “ranan nan tana gusowa.” (Ibran. 10:24, 25) Bulus ya ba su gargaɗin da ya dace, yana cewa: “Domin wannan fa bari mu daina zancen ruknai na Kristi, mu nace bi zuwa kamala.”—Ibran. 6:1.
4. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance a faɗake a ruhaniya, kuma menene zai taimake mu mu yi hakan?
4 Muna zama ne a lokacin da annabcin Yesu zai sami cika na ƙarshe. “Babbar ranan Ubangiji,” wato, ranan da za a kawo ƙarshen dukan zamanin Shaiɗan “ta kusa.” (Zeph. 1:14) Fiye da dā, dole ne mu kasance da fahimi ta ruhaniya kuma mu yi zaman tsaro. (1 Bit. 5:8) Muna hakan kuwa? Kāmala za ta taimake mu mu mai da hankali ga inda muke a wannan lokacin.
Abin da Kāmala Take Nufi
5, 6. (a) Menene ci gaba na ruhaniya ya ƙunsa? (b) Nace bi zuwa kāmala na bukatar yin ƙoƙari a waɗanne wurare biyu?
5 Bulus ya ƙarfafa Kiristoci Ibraniyawa na ƙarni na farko su nace bi zuwa kāmala da kuma abin da kāmala ta ruhaniya ta ƙunsa. (Karanta Ibraniyawa 5:14.) Shan “madara” kawai ba ya ƙosar da “isassun mutane.” Suna cin “abinci mai-ƙarfi.” Saboda haka, sun san tushen “farkon zantattuka” da “zurfafa” na gaskiya. (1 Kor. 2:10) Bugu da ƙari, ana koyar da hankalinsu ta wurin yin amfani da abin da suka sani, kuma hakan na taimaka masu su rarrabe nagarta da mugunta. Sa’ad da suke son su tsai da shawara, wannan koyarwa tana taimaka masu su fahimci ƙa’idodin Nassi da za su yi amfani da shi da kuma yadda za su yi hakan.
6 Bulus ya rubuta: “Ya kamata mu daɗa mai da hankali musamman ga abin da aka ji, domin kada mu zakuɗa.” (Ibran. 2:1) Muna iya zakuɗa daga bangaskiya kafin mu ankara. Muna iya guje wa hakan ta wajen “daɗa mai da hankali” sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, kowannenmu yana bukatar ya tambayi kan shi: “Har ila ina nazarin abubuwa masu sauƙi ne? Ina yin abubuwa ne kawai don ana yi, ba tare da sa dukan zuciyata a cikin gaskiya ba. Ta yaya zan samu ci gaba na gaske a cikin gaskiya?’ Nace bi zuwa kāmala na bukatar mu yi ƙoƙari a wurare biyu. Dole ne mu san Kalmar Allah sosai. Kuma muna bukatar mu koyi biyayya.
Ka San Kalmar Sosai
7. Ta yaya za mu amfana daga sanin Kalmar Allah da kyau?
7 Bulus ya rubuta: ‘Kowane mai-shan madara mara-sanin maganar adalci ne; gama jariri ne shi.’ (Ibran. 5:13) Don mu samu ci gaba, dole ne mu san kalmar Allah sosai, wato, saƙonsa a gare mu. Tun da yake wannan saƙon yana cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ya kamata mu zama masu nazarin Nassosi da kyau da kuma littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45-47) Yin nazarin tunanin Allah a wannan hanyar zai taimake mu mu koyar da hankalinmu. Ka yi la’akari da misalin wata Kirista mai suna Orchid.a Ta ce: “Tunasarwa da ta shafi rayuwata sosai ita ce ta karanta Littafi Mai Tsarki a kullum. Ya ɗauke ni wajen shekara biyu na karance dukan Littafi Mai Tsarki, amma ji nake kamar wannan ne lokaci na farko da zan san Mahaliccina. Na koyi hanyoyinsa, abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so, yawan ikonsa, da kuma yawan hikimarsa. Karanta Littafi Mai Tsarki a kullum ya kiyaye ni a lokaci mai wuya a rayuwata.”
8. Ta yaya Kalmar Allah za ta iya shafanmu sosai?
8 Karanta Kalmar Allah a kai a kai yana sa saƙonsa ya ‘aikata’ a kanmu. (Karanta Ibraniyawa 4:12.) Irin wannan karatun yana mulmula mu kuma ya sa mu ƙara faranta wa Jehobah rai. Kana bukatar ka ƙara ba da lokacin ne don karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka yi bimbini a kan abin da ya ce?
9, 10. Menene sanin Kalmar Allah ya ƙunsa? Ka ba da misali.
9 Sanin Littafi Mai Tsarki ya wuce sanin abin da ya ce. Jarirai na ruhaniya na zamanin Bulus sun san abin da Kalmar Allah hurarriya ta faɗa. Amma, ba su yi amfani da shi ba kuma ba su aikata ba don su ga amfaninsa. Ba su sanar da kansu saƙon domin sun ƙi barinsa ya yi musu ja-gora sa’ad da suke tsai da shawara mai kyau a rayuwarsu.
10 Sanin Kalmar Allah yana nufin sanin abin da ta ce da yin amfani da wannan sanin. Abin da ya faru da wata ’yar’uwa mai suna Kyle ya nuna yadda za a iya yin hakan. Kyale ta yi ƙazamar gardama da wata abokiyar aikinta. Menene ta yi don ta magance matsalar? Ta yi bayani: “Nassi da na tuna shi ne Romawa 12:18, wadda ta ce: ‘A gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.’ Sai na gaya wa abokiyar aikina cewa zan so mu tattauna tare bayan aiki.” Kwalliya ta biya kuɗin sabulu domin matakin da Kyle ta ɗauka na magance matsalar ya burge abokiyar aikinta sosai. “Na koyi cewa ba za mu taɓa yin kuskure ba idan muka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki,” in ji Kyle.
Ka Koyi Yin Biyayya
11. Menene ya nuna cewa yin biyayya cikin yanayi mai wuya zai iya zama kaluɓale?
11 Yin amfani da abin da muka koya daga Nassosi yana iya zama ƙalubale, musamman sa’ad da abubuwa suka yi wuya. Alal misali, bayan Jehobah ya ’yantar da ’ya’yan Isra’ila daga bauta a ƙasar Masar, sai “suka faɗa ma Musa da faɗa,” kuma suka ci gaba da “auna Ubangiji.” Me ya sa? Domin rashin ruwan sha. (Fit. 17:1-4) Kusan wata biyu da yin alkawari da Allah kuma suka yarda cewa za su yi “dukan zantattukan da Ubangiji ya faɗi,” sun keta dokarsa ta wajen bauta wa gunki. (Fit. 24:3, 12-18; 32:1, 2, 7-9) Sun yi hakan ne domin suna jin tsoro cewa Musa ya daɗe sosai domin ana ba shi umurni a kan Dutsen Horeb? Suna tunani ne cewa Amalekawa za su sake kai musu hari kuma Isra’ilawa ba za su samu taimako ba domin Musa ba ya nan, wanda Jehobah ya yi amfani da shi kuma suka ci nasara a kan Amalekawa? (Fit. 17:8-16) Mai yiwuwa haka ne, amma ko da menene dalilin, Isra’ilawa “suka ƙi biyayya.” (A. M. 7:39-41) Bulus ya aririci Kiristoci su “yi anniya” kuma su guji “fāɗi bisa wannan misalin kangara” da Isra’ilawa suka nuna sa’ad da suka ji tsoron shiga Ƙasar Alkawari.—Ibran. 4:3, 11.
12. Ta yaya ne Yesu ya koyi biyayya, da wane sakamako?
12 Nace bi zuwa kāmala na bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu wajen yin biyayya ga Jehobah. Kamar yadda Yesu Kristi ya nuna, a yawancin lokaci, muna koyan biyayya ne ta wajen wahalar da muka sha. (Karanta Ibraniyawa 5:8, 9.) Kafin ya zo duniya, Yesu ya yi wa Ubansa biyayya. Amma yin nufin Ubansa a duniya ya ƙunshi wahala na zahiri da na hankali. Da yake ya koyi biyayya ta wurin wahala mai tsanani da ya sha, Yesu “ya zama cikakke” don sabon matsayin da Allah zai ba shi, wato, zama Sarki da Babban Firist.
13. Menene zai nuna cewa mun koyi yin biyayya?
13 Mu kuma fa? Mun ƙuduri aniya mu yi biyayya ga Jehobah ko sa’ad da muke fuskantar matsaloli masu wuya? (Karanta 1 Bitrus 1:6, 7.) Allah ya bayyana gargaɗinsa sarai game da ɗabi’a, faɗan gaskiya, yin magana mai kyau, yin karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki na kai, halartan taron Kirista, da fita aikin wa’azi. (Josh. 1:8; Mat. 28:19, 20; Afis. 4:25, 28, 29; 5:3-5; Ibran. 10:24, 25) Muna biyayya ga Jehobah a waɗannan batutuwa ko sa’ad da muke shan wahala? Yin biyayya zai nuna cewa mun samu ci gaba zuwa ga kāmala.
Me Ya Sa Manyanta na Kirista Yake da Amfani?
14. Ka bayyana yadda nace bi zuwa kāmala zai iya zama kāriya.
14 Kāriya ce sosai idan Kirista yana da hankali wasasshe da aka koyar da kyau don ya rarrabe tsakanin nagarta da mugunta a duniya da ta “wuce gaban [ta] ji.” (Afis. 4:19) Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna James, da yake karanta da kuma yin nazarin littattafai da ke bisa Nassi sosai ya samu aiki inda dukan abokan aikinsa mata ne. “Ko da yake yawancinsu ba su damu da nuna ɗabi’a mai kyau ba,” in ji James, “wata a cikinsu tana da halin kirki kuma ta nuna tana son koyarwar Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ni da ita kaɗai ke cikin ɗaki muna aiki, sai ta fara gaya mini mu yi lalata. Na ɗauka wasa take yi amma ya yi mini wuya na sa ta daina. Nan da nan na tuna wani labari da aka ba da a cikin Hasumiyar Tsaro game da wani ɗan’uwa da ya fuskanci irin wannan gwaji a wajen aikinsa. Talifin ya yi amfani da misalin Yusufu da matar Fotifar.b Nan da nan na ture yariyar, kuma ta fice.” (Far. 39:7-12) James ya gode wa Allah cewa babu abin da ya sake faruwa kuma ya kasance da lamiri mai kyau.—1 Tim. 1:5.
15. Ta yaya nace bi zuwa kāmala yake ƙarfafa zuciyarmu ta alama?
15 Manyanta a ruhaniya tana da amfani domin tana ƙarfafa zuciyarmu ta alama kuma tana sa kada mu “kawu bisa ga koyarwa iri iri sababbi.” (Karanta Ibraniyawa 13:9.) Sa’ad da muka yi ƙoƙari mu ci gaba a ruhaniya, muna mai da hankalinmu ga “mafifitan al’amura.” (Filib. 1:9, 10) Ta haka muna nuna godiya ga Allah da kuma don dukan tanadodin da ya yi don amfaninmu. (Rom. 3:24) Kiristan da a ‘azanci kuwa cikakken mutum ne’ yana nuna irin wannan godiya kuma yana more dangantaka na kud da kud da Jehobah.—1 Kor. 14:20.
16. Menene ya taimaki wata ’yar’uwa ta ‘tsai da zuciyarta’?
16 Wata ’yar’uwa mai suna Louise ta faɗi cewa bayan da ta yi baftisma, ta fi damuwa da ainihin yadda za ta faranta wa mutane rai. Ta ce: “Ba na yin abin da ba shi da kyau amma ba na sha’awar bauta wa Jehobah sosai. Na fahimci cewa ina bukatar na yi canje-canje idan ina son in gamsu cewa ina ba Jehobah dukan kome da zan iya ba shi. Canji mafi girma da zan yi shi ne bauta masa da dukan zuciya ta.” Ta wurin yin iya ƙoƙarinta, Louise ta ‘tsai da zuciyarta,’ kuma hakan ya taimake ta sa’ad da ta fuskanci matsalar ciwon jiki. (Yaƙ. 5:8) Louise ta ce, “Na yi fama sosai, amma na kusaci Jehobah sosai.”
‘Da Zuciya Ɗaya Ka Zama Mai Biyayya’
17. Me ya sa yin biyayya yake da muhimmanci a ƙarni na farko?
17 Shawarar da Bulus ya bayar na “nace bi zuwa kāmala” ta ceci ran Kiristoci na ƙarni na farko da ke zama a Urushalima da Yahudiya. Waɗanda suka yi biyayya ga wannan shawarar suna da fahimi na ruhaniya da ake bukata don su fahimci alamar da Yesu ya ba su na soma guduwa “zuwa duwatsu.” Sa’ad da suka ga “ƙyamar lalata, . . . tana tsaye a cikin tsatsarkan wuri,” wato, sojojin Roma da suka kewaye kuma suke shigan Urushalima, sun san cewa lokacin guduwa ya yi. (Mat. 24:15, 16) Ta wajen yin biyayya ga gargaɗin da Yesu ya ba da a annabcinsa, Kiristoci sun gudu daga birnin Urushalima tun kafin a halaka ta, kuma in ji ɗan tarihi na coci mai suna Eusebius, sun tare a birnin Pella da ke tsaunukan Gileyad. Ta hakan sun guje wa bala’in da ya faɗa wa Urushalima wanda shi ne ya fi muni a tarihi.
18, 19. (a) Me ya sa yin biyayya yake da muhimmanci a zamaninmu? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
18 Biyayya da ake yi don nace bi zuwa kāmala za ta kuma ceci ranmu sa’ad da muka fuskanci ainihin cikawar annabcin Yesu cewa “za a yi ƙunci mai-girma” da ba a taɓa yin irin sa ba. (Mat. 24:21) Za mu yi biyayya kuwa ga duk wani umurni na gaggawa da za mu samu daga “wakili mai-aminci” a nan gaba? (Luk 12:42) Yana da muhimmanci mu koyi yin biyayya “da zuciya ɗaya”!—Rom. 6:17.
19 Idan za muna son mu manyanta a ruhaniya muna bukatar mu koyar da hankalinmu. Muna yin hakan ta wajen yin iya ƙoƙarinmu mu san Kalmar Allah sosai kuma mu koyi yin biyayya. Manyanta a matsayin Kirista na jawo ƙalubale na musamman ga matasa. Talifi na gaba ya tattauna yadda za a yi nasara wajen bi da irin wannan ƙalubalen.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye.
b Ka duba talifin nan mai jigo “Fortified to Say No to Wrongdoing” (Samun Ƙarfafa na Ƙin Yin Lalata) da ke cikin fitowar Hasumiyar Tsaro na 1 ga Oktoba, 1999.
Menene Ka Koya?
• Menene manyanta a ruhaniya, kuma yaya muke samun ta?
• Yaya sanin Kalmar Allah da kyau yake taimaka wa wajen nace bi zuwa kāmala?
• Ta yaya muke koyan yin biyayya?
• A waɗanne hanyoyi ne manyanta take amfanar mu?
[Hotunan da ke shafi na 10]
Bin gargaɗin Littafi Mai Tsarki na taimakonmu mu bi da matsaloli a hanyar da ta nuna cewa mun manyanta
[Hotunan da ke shafi na 12]
Bin gargaɗin Yesu ya ceci ran Kiristoci na ƙarni na farko