Na Ga Yadda Suka Ƙaru A Koriya
Milton Hamilton ne ya ba da labarin
“Muna baƙin cikin sanar da ku cewa gwamnatin Jamhuriyar Koriya ta kwace dukan bizar ku masu wa’azi a ƙasashen waje kuma ta nuna cewa ba ta son zaman ku a ƙasar. . . . Saboda haka, za ku koma ƙasar Japan na ɗan lokaci.”
A KUSAN ƙarshen shekara ta 1954 ce ni da matata muka karɓi saƙon da ke sama daga Brooklyn, New York, Amirka. A farkon shekarar nan ce muka sauke karatu a aji na 23 ta Makarantar Gileyad da ke New York. Sa’ad da muka karɓi wannan wasiƙar, muna hidima ce na ɗan lokaci a Indianapolis, a ƙasar Indiana.
Ajinmu ɗaya da matata, Liz (a dā Liz Semock), sa’ad da nake sakandare. Mun yi aure a shekara ta 1948. Tana son hidima na cikakken lokaci amma tana jin tsoron barin ƙasar Amirka don yin hidima a ƙasar waje. Menene ya canja ra’ayinta?
Liz ta yarda ta bi zuwa taron waɗanda suke son su halarci makarantar Gileyad. An yi wannan taron ne a taron gunduma na dukan ƙasashe a Yankee Stadium, New York, a cikin rani ta shekara ta 1953. Bayan wannan taron mai ƙarfafawa ne muka cika takardar shiga makarantar Gileyad. Abin mamaki shi ne, an gayyace mu mu halarci aji na gaba, wanda zai soma a watan Fabrairu 1954.
An aika mu hidima a Koriya, ko da yake bai daɗe ba da yaƙin da aka yi shekara uku a ƙasar ta ƙare a cikin rani ta shekara ta 1953, kuma hakan ya ɓata ƙasar. Ƙasar Japan muka fara zuwa bisa ja-gorar da aka ba mu a cikin wasiƙar da muka yi ƙaulinta a baya. Bayan mun yi tafiya ta kwana 20 a cikin jirgin ruwa, mun isa Japan a Janairu ta 1955 tare da wasu masu wa’azi a ƙasashen waje su shida da aka tura ƙasar Koriya. Lloyd Barry, mai kula da ofishin reshe na Japan a wannan lokacin, ne ya zo ya same mu a bakin ruwa da ƙarfe shida na asuba. Ba da daɗewa ba muka tafi masaukin masu wa’azi a ƙasashen waje da ke garin Yokohama. A wannan ranar mun fita hidimar fage.
Mun Isa Ƙasar Koriya
Ba da daɗewa ba, mun sami bizar shiga Jamhuriyar Koriya. A ranar 7 ga Maris, 1955, jirgin sama da muka hau ya bar Babban Filin Jirgin Sama da ke Haneda a Tokyo, kuma mun yi tafiyar awa uku zuwa filin jirgin sama da ke Yoido a Seoul. Shaidu ’yan Koriya fiye da ɗari biyu ne suka marabce mu, kuma mun yi hawayen farin ciki. A lokacin, Shaidu dubu ɗaya ne kawai suke Koriya. Kamar yawancin mutanen da suke Turai, mun ɗauka cewa mutanen da suke Ƙasashen Gabas halinsu ɗaya ne kuma kamanninsu ɗaya ko da daga wace ƙasa ko tushe suka fito. Amma, ba daɗewa ba mun fahimci cewa ba hakan ba ne. Koriyawa suna da harshensu da kuma baƙaƙen rubutu da yadda suke yin dahuwa, kamaninsu, da kuma kayansu, da kuma wasu abubuwan da su kaɗai suke yi, kamar irin gidajen da suke ginawa.
Ƙalubalenmu na farko shi ne koyan yaren. Ba mu da littafin da za mu yi amfani da shi mu koyi yaren Koriya. Ba da daɗewa ba muka fahimci cewa ba zai yiwu ba mu yi amfani da sauti na Turanci wajen koyan yaren Koriya. Mutum zai iya koyan yadda zai faɗi yaren ne ta wajen koyan kalmomin Koriya.
Mun yi kurakurai wajen faɗin kalmomi. Alal misali, Liz ta tambayi wata mata ko tana da Littafi Mai Tsarki. Matar ta kalle ta cike da mamaki sai ta shiga gida ta kawo kwalin ashana. Liz ta ce a ba ta sungnyang (ashana) maimakon sungkyung, kalmar da ake amfani da ita don “Littafi Mai Tsarki.”
Bayan ’yan watanni, an ce mu je mu buɗe gidan da masu wa’azi a ƙasashen waje suke zama a Pusan, a kudancin birnin da ke kusa da tashan jirgin ruwa. Mun yi hayar ƙananan ɗakuna uku inda mu da kuma ’yan’uwa mata biyu da aka tura mu wurin tare za mu zauna. Babu ruwan famfo da gidan ba haya na zamani a gidan. Daddare ne kawai ƙarfin ruwan yake ɗan ƙaruwa. Saboda haka, muna tashiwa tun da duku-duku don mu ɗibi ruwa cikin galan. Muna tafasa ruwan ko kuma mu saka maganin kashe cutar da ke cikin ruwa domin mu sha ruwan.
Da akwai wasu ƙalubalen da muka fuskanta. Lantarkin ba shi da ƙarfin da zai ɗauki na’urar wanki da ta guga. Kicin ɗinmu na waje, kuma da rasho muke dafa abinci. Ba da daɗewa ba, kowannenmu ya koyi dafa abinci a ranar girkinsa. Bayan shekara uku, da ni da Liz muka kamu da ciwon huhu. Yawancin masu wa’azi a ƙasashen waje a lokacin sun kamu da wannan ciwon. An yi watanni kafin mu warke, kuma mun yi wasu ciwon bayan hakan.
An Taimaka Mana Mu Sha Kan Matsaloli
An yi shekaru 55 ana tashin hankali na siyasa a ɓangaren ƙasar Koriya da ke gefen teku. Shiyyar da sojoji ba sa faɗa ce ta raba wannan ɓangaren ƙasar. Tafiyar mil 35 ce daga arewacin Seoul, birnin tarayyar Jamhuriyar Koriya. A shekara ta 1971, Frederick Franz ya ziyarce mu daga hedkwata da ke Amirka. Na raka shi zuwa wannan shiyyar da sojoji ba sa faɗa, kuma ita ce iyakar ƙasa wadda aka fi kārewa a duniya. A shekaru, shugabanni da ke Majalisar Ɗinkin Duniya sukan haɗu a wurin da wakilan gwamnatocin biyu.
Hakika, mun kasance da tsakatsaki a batun siyasar wannan duniyar, har da abin da ke faruwa a shiyyar da ke gefen teku a Koriya. (Yoh. 17:14) Domin sun ƙi su ɗauki makamai su yaƙi ’yan’uwansu, Shaidu ’yan Koriya fiye da 13,000 gabaki ɗaya ne suka yi shekaru 26,000 a kurkuku. (2 Kor. 10:3, 4) Dukan ’yan’uwa matasa da ke wannan ƙasar ne suka san cewa za su fuskanci wannan batun, amma hakan bai ba su tsoro ba. Abin baƙin ciki ne cewa gwamnati ta kira Kiristoci masu wa’azi, “masu laifi,” waɗanda “laifinsu” kawai shi ne sun ƙi su karya tsakatsakinsu na Kiristanci.
A shekara ta 1944, a lokacin da ake Yaƙin Duniya ta biyu, ni ma na ƙi shiga aikin soja kuma saboda haka, sai da na yi shekaru biyu da rabi a kurkukun da ke Lewisburg a Pennsylvania. Ko da yake ’yan’uwanmu da ke Koriya sun fuskanci matsanancin yanayi a kurkuku, na san abin da waɗannan Shaidu matasa suka fuskanta. Hakan ya ƙarfafa mutane da yawa su san cewa wasu a cikinmu da ke wa’azi a ƙasashen waje a Koriya mun fuskanci irin waɗannan matsalolin.—Isha. 2:4.
Mun Fuskanci Yanayi Mai Wuya
Tsakatsakinmu ya shafi wani batu da ya taso a shekara ta 1977. Shugabanni sun ce mu ne muka hana Koriyawa matasa su shiga aikin soja. Saboda haka, gwamnatin ta yanke shawarar hana takardar izinin sake shiga ƙasar ga duk wani mai wa’azi na ƙasashen waje da ya bar ƙasar. Wannan hanin ya ci gaba daga shekara ta 1977 zuwa 1987. Da a ce mun bar Koriya a cikin waɗannan shekarun, da ba za a ƙyale mu mu koma ƙasar ba. Saboda haka, mun ƙi mu ziyarci ƙasarmu a cikin waɗannan shekarun.
Sau da yawa mun sadu da manyan ma’aikata na gwamnati kuma mun bayyana musu matsayinmu na masu bin Kristi. Daga baya, sun fahimci cewa hakan ba zai ba mu tsoro ba, sai suka cire hanin, bayan shekara goma. A cikin waɗannan shekarun, wasu masu wa’azi na ƙasashen waje sun bar ƙasar domin kula da lafiyar jikinsu, amma mu da muka rage mun zauna a ƙasar, kuma mun yi farin cikin yin hakan.
A kusan shekara ta 1985, waɗanda suke hamayya da hidimarmu sun yi ƙarya cewa waɗanda suke kula da aikinmu a ƙasar ne suke koya wa matasa su guji aikin soja. Saboda haka, gwamnati ta kira dukanmu don ta tuhume mu. A ranar 22 ga Janairu, 1987, lauyan gwamnati ya ga cewa zarge-zargen ƙarya ce. Hakan ya taimaka wajen daidaita batutuwa don gaba.
Allah Ya Albarkaci Aikinmu
A Koriya, hamayya da aikinmu na wa’azi ya yi tsanani sosai a cikin waɗannan shekarun domin tsakatsakinmu. Da hakan, samun wurare masu kyau don yin manyan taronmu ya yi wuya sosai. Saboda haka, Shaidu suka gina Majami’ar Taro a birnin Pusan, na farko a Ƙasashen Gabas. Na sami gatar ba da jawabin keɓe wannan wurin a ranar 5 ga Afrilu, 1976, a gaban mutane 1,300.
Tun shekara ta 1950, an tura dubban sojoji daga Amirka zuwa ƙasar Koriya. Bayan sun koma Amirka, yawancinsu sun zama Shaidu masu ƙwazo. Mukan sami wasiƙu daga wurinsu, kuma muna farin ciki cewa mun taimaka musu su san Jehobah.
Abin baƙin ciki, na yi rashin matata, Liz, a ranar 26 ga Satumba, 2006. Ina kewarta sosai. A shekaru 51 da ta yi a nan, ta yi dukan aikin da aka ba ta cikin farin ciki kuma ba ta taɓa kuka ba. Ba ta taɓa kawo shawara ko ambata komawa Amirka ba, ƙasar da ta ce ba ta so ta bari!
Har yanzu ina hidima a Bethel da ke Koriya. Iyalin ta ƙaru zuwa 250. Gata ne na yi hidima tare da mutane shida a matsayin Kwamitin Reshe da ke kula da aiki a nan.
Ko da yake Koriya ba ta da arziki a lokacin da muka zo, a yanzu, tana ɗaya cikin ƙasashen da suka sami ci gaba sosai. Akwai Shaidu fiye da 95,000 a Koriya, kusan kashi 40 suna hidima a matsayin majagaba na kullum ko na ɗan lokaci. Dukan waɗannan sun daɗa ga dalilan da nike da su na jin daɗin bauta wa Allah a nan kuma na ga tumakin Allah sun daɗu.
[Hoto a shafi na 24]
Isowarmu Koriya tare da waɗanda muke wa’azi a ƙasashen waje da su
[Hoto a shafi na 24]
Yin hidima a birnin Pusan
[Hoto a shafi na 25]
Tare da Ɗan’uwa Franz a shiyyar da sojoji ba sa faɗa, a shekara ta 1971
[Hoto a shafi na 26]
Tare da Liz jim kaɗan kafin mutuwarta ▸
[Hoto a shafi na 26]
Ofishin Reshe na Koriya a inda nake hidima a matsayin wanda ke cikin iyalin Bethel ▼