Allon Laka na Dā da Kuma Littafi Mai Tsarki
BAYAN an riƙitar da yaren ’yan adam a Babel, an tsara hanyoyin yin rubutu dabam dabam. Mutanen da suke zaune a Mesopotamiya, kamar su Sumariyawa da Babiloniyawa sun yi amfani da cuneiform, wato, rubutun da aka yi a kan allon laka. Wannan kalmar ta fito ne daga yaren Latin kuma tana nufin rubutu mai kusurwa uku wanda ake yi da alƙalami mai tsini a kan allon laka.
Masu tona ƙasa sun tono rubuce-rubucen cuneiform da suka yi magana game da mutane da aukuwa da aka ambata cikin Nassosi. Menene muka sani game da wannan tsarin rubutu na dā? Ta yaya waɗannan rubuce-rubucen suka tabbatar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki?
Rubuce-Rubucen da Suka Ɗore
Masana sun gaskata cewa tsarin rubutu da aka yi amfani da shi dā a Mesopotamiya yana kama ne da zane, wato, alama ko hoto da ke wakiltar kalmar ko abin da ake nufi. Alal misali, alamar takarkari yana kama ne da kan takarkari. Yayin da bukatun ajiye bayanai ya daɗu, an bunƙasa rubutun cuneiform. “Alamun sun wakilci kalaman da kuma gaɓoɓinsu, ana kuma iya haɗa yawancinsu su wakilci gaɓoɓin kalma,” in ji NIV Archaeological Study Bible. Daga baya, alamu dabam dabam guda 200 sun sa cuneiform “ya zama furci, tare da dukan kalmominsa da nahawunsa.”
A zamanin Ibrahim, a wajen shekara ta 2,000 K.Z., cuneiform ya riga ya bunƙasa. Bayan ƙarnuka ashirin, harsuna sha biyar ne suka soma amfani da irin wannan rubutun. Fiye da kashi tasa’in da tara na rubuce-rubucen cuneiform da aka gani an yi su ne a kan allon laka. A cikin shekaru 150 da suka shige, an samu yawancin waɗannan allunan a ƙasar Ur, Uruk, Babila, Nimrud, Nippur, Ashur, Nineveh, Mari, Ebla, Ugarit, da Amarna. Littafin Archaeology Odyssey ya ce: “Masana sun kimanta cewa allon cuneiform wajen miliyan ɗaya zuwa biyu ne aka haƙo, kuma ana samun wajen 25,000 ko fiye da haka a kowace shekara.”
Masanan cuneiform a dukan duniya suna da jan aiki na yin fassara. In ji wani kimantawa da aka yi, “kashi ɗaya cikin goma na rubutun cuneiform ne kawai aka karanta a wannan zamanin.”
Rubutun cuneiform da aka gano masu harsuna biyu da uku ne suka sa aka fahimci ma’anar rubutun. Masana sun gano cewa waɗannan allunan suna ɗauke ne da rubutu iri ɗaya na cuneiform amma a harsuna dabam-dabam. Abin da ya taimaka aka fahimci waɗannan rubuce-rubucen shi ne cewa ana yawan maimaita sunayen waɗanda suka yi sarauta, mukaminsu, da kuma yabon kansu da suka yi.
A cikin shekara ta 1850, masana sun karanta harsuna dabam dabam na ƙasar Gabas ta Tsakiya ta dā, Akkadiya, ko Assuriya da Babila da ke cikin cuneiform. Littafin Encyclopædia Britannica ya bayyana cewa: “Sa’ad da aka fahimci harshen Akkadiya, hakan ya sa an fahimci ainihin ma’anar rubutun, kuma an yi amfani da irin wannan salon wajen fassara sauran harsuna da ke cikin cuneiform.” Ta yaya ne waɗannan rubuce-rubucen suka jitu da Nassosi?
Shaidar da ta Amince da Littafi Mai Tsarki
Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa sarakunan Ka’aniya ne suka mulka Urushalima har sa’ad da Dauda ya kame ta, a kusan shekara ta 1070 K.Z. (Josh. 10:1; 2 Sam. 5:4-9) Amma wasu masana sun yi shakkar hakan. A shekara ta 1887, wata mata manomi ta ga allon laka a Amarna, ta ƙasar Masar. Bayan da aka fassara kalamai guda 380, masana sun fahimci cewa batu ne na jakadanci da aka yi tsakanin sarakunan Masar (Amenhotep na 3 da Akhenaton) da kuma masarautun Ka’aniyawa. Wasiƙu guda shida sun fito ne daga ‘Abdi-Heba, sarkin Urushalima.
Littafin Biblical Archaeology Review ya ce: “Domin allon Amarna ya kira Urushalima birni, ba ɗan ƙaramin mazauni ba, kuma ya ambata cewa ‘Abdi-Heba . . . gwamna ne wanda yake zaune a Urushalima kuma yana da sojoji hamsin ’yan Masar waɗanda suke kāre ƙasar, hakan ya nuna cewa Urushalima ’yar ƙaramar ƙasa ce da ke da ’yancin kanta.” Wannan littafin ya sake cewa: “Muna da tabbaci bisa ga wasiƙun Amarna cewa, akwai birnin da ya fita dabam a wannan lokacin.”
Sunayen da ke Cikin Tarihin Assuriyawa da Babiloniyawa
Assuriyawa da Babiloniyawa sun rubuta tarihinsu ne a kan allunan laka, silinda, gilashi, da kuma abubuwan da aka gina don tunawa. Saboda haka, sa’ad da masana suka fassara cuneiform na Akkadiyawa, sun ga cewa waɗannan rubuce-rubucen sun ambata sunayen mutane da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
In ji littafin nan The Bible in the British Museum: “A cikin jawabinsa ga Society of Biblical Archaeology a shekara ta 1870, Dakta Samuel Birch ya gano [sunaye a cikin rubuce-rubucen cuneiform] na sarakuna Ibraniyawa kamar Omri, Ahab, Jehu, Azariah . . . , Menahem, Pekah, Hoshea, Hezekiya da Manassa, da sarakunan Assuriya Tiglath-Pileser . . . [na 3], Sargon, Sennacherib, Esarhaddon da Ashurbanipal, . . . da kuma sarakunan Suriya, Benhadad, Hazael da Rezin.”
Littafin nan The Bible and Radiocarbon Dating ya kwatanta tarihin da ke cikin Littafi Mai Tsarki na Isra’ila da Yahuda da rubuce-rubucen cuneiform na dā. Menene sakamakon? “Gabaki ɗaya, sarakunan Yahuda su 15 ko 16 ne suka bayyana a cikin tarihin wasu ƙasashe, kuma sunayensu da lokacin da suka rayu ya yi daidai da waɗanda suke cikin littafin Sarakuna [na Littafi Mai Tsarki]. Babu sarkin da ba a ambata ba, kuma waɗannan tarihin na ƙasashen waje ba su ambata sunan da ba ya cikin littafin Sarakuna ba.”
Wani sanannen rubutun cuneiform da aka gano a shekara ta 1879, mai suna Cyrus Cylinder, ya rubuta cewa bayan Cyrus ya kame Babila a shekara ta 539 K.Z., ya yi amfani da tsarinsa na mai da bayi zuwa ƙasarsu. Wasu cikin waɗanda suka amfana su ne Yahudawa. (Ezra 1:1-4) Masana da yawa na ƙarni 19 sun yi shakkar gaskiyar wannan dokar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Amma, rubuce-rubucen cuneiform na zamanin Farisa, har da Cyrus Cylinder, sun ba da tabbatacciyar shaidar da ta nuna cewa abin da ke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki daidai ne.
A shekara ta 1883, an gano rubuce-rubucen cuneiform a Nippur, a kusa da Babila. A cikin sunaye 2,500 da aka ambata, guda 70 Yahudawa ne. Sun bayyana, in ji ɗan tarihi Edwin Yamauchi, “a matsayin mutanen da suka karɓi kwangila, wakilai, shaidu, masu karɓan haraji, da kuma fadawa.” Alamar da ta nuna cewa Yahudawa sun ci gaba da yin waɗannan ayyukan a kusa da Babila a wannan lokacin yana da muhimmanci. Ya jitu da annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da ya ce yayin da “wani ringi” na Isra’ilawa suka koma Yahudiya daga bauta a Assuriya da Babila, yawancinsu sun ƙi komawa.—Isha. 10:21, 22.
A shekara ta Alif dubu ɗaya K.Z., rubuce-rubucen cuneiform sun wanzu tare da rubutun zamani. Amma Assuriyawa da Babiloniyawa sun yi watsi da cuneiform domin rubutun zamani.
Har yanzu ba a yi nazarin ɗarurruwan rubuce-rubucen nan ba da ke adane a gidajen tarihi. Rubuce-rubucen da ƙwararru suka riga suka fassara sun tabbatar da cewa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. Wa ya san ƙarin gaskiyar da rubuce-rubucen da ba a fassara ba za su bayyana?
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 21]
Ma’adanar kayayyakin tarihi na Britaniya ne suka ba da izinin ɗaukan hoton