Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/1 pp. 14-16
  • Tattaunawa da Matasa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tattaunawa da Matasa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Fahimtar Abin da ke Kawo Tangarɗa
  • Yadda Za a Shawo Kan Ƙalubale
  • Sa’ad da Ɗanka Matashi Ya Fara Shakkar Addinin da Kake Bi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Shirya Matasa Su Zama Manya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Tattauna da Yaranka Game da Jima’i
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Iyaye, Ku Kula da Yaranku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/1 pp. 14-16

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Tattaunawa da Matasa

“A dā, tattaunawa da ɗana yana da sauƙi amma yanzu da ya kai shekara 16, da kyar ni ko maigidana ke sanin abin da ke zuciyarsa. Sai ya tare a ɗakinsa shi kaɗai kuma da kyar yake magana da mu!”—MIRIAM, A ƘASAR MEXICO.

“A dā yarana suna saurarana sosai. Suna kasa kunne kwarai da gaske! Amma a yanzu da suka zama matasa suna ganin cewa an bar yayi na.”—SCOTT, A OSTARELIYA.

IDAN kana renon matashi, kana iya fahimtar waɗannan iyayen da aka ambata a baya. Wataƙila a dā kai da ɗanka kuna taɗi sosai. Amma kamar dai hanyar ta toshe yanzu. Angela a Italiya ta ce: “Da yake ɗan yaro, kullum ɗana sai ya yi mini tambayoyi. Yanzu sai dai na taɓo shi kafin ya yi magana. Idan ban yi hakan ba, sai mu yi kwanaki ba mu yi wani zancen kirki ba.”

Kamar Angela, wataƙila ka lura cewa ɗanka wanda a dā mai yawan magana ne ya canja, ya zama mai shuru-shuru. Duk tambayar da ka yi sai ya ba da gajeriyar amsa. “Ya yau?” ka tambayi ɗanka. Sai ya haɗa fuska ya amsa “Kalau.” Ka tambayi ’yarka: “Me ya faru yau a makaranta?” Sai ta ɗaga kafaɗa ta ce “ba kome.” Da niyar ka jawo shi don ku tattauna, ka tambaye shi “me ya sa ba za ka yi min bayani ba?” sai dai ya daɗa shuru.

Hakika, yin magana ba ya yi wa wasu matasa wuya. Amma abin da suke faɗi ba abin da iyayensu suke so su ji ba ne. “‘Ki ƙyale ni’ abin da ’yata take faɗa ke nan in na ce ta yi wani abu,” in ji Edna wata mace a Nijeriya. Ramón a Mexico ya lura cewa ɗansa mai shekara 16 yana da irin wannan halin. Ya ce: “Kusan kowace rana ce muke musu. Idan na ce masa ya yi wani aiki, sai ya soma gaya mini hanzarinsa.”

Tattaunawa da matashi da ba ya son ya ba da haɗin kai zai iya ɓata ran iyayensa. Littafi Mai Tsarki ya amince da cewa “wurinda babu shawara, nufe nufe su kan warware.” (Misalai 15:22) “Idan ban san abin da ɗana yake tunani ba, sai in ji kamar in yi masa tsawa,” in ji Anna, wata gwauruwa a Rasha. Me ya sa lokacin da aka fi bukatar tattaunawa da juna, sai matasa da iyayensu su kasa yin hakan?

Fahimtar Abin da ke Kawo Tangarɗa

Tattaunawa ba kawai yin magana ba ne. Yesu ya ce: ‘Gama daga cikin yalwar zuciya baki ya ke zance.’ (Luka 6:45) Ta wajen tattaunawa da kyau mukan koya daga mutane kuma mu bayyana abin da ke zuciyarmu. Faɗin abin da ke zuciyarsa zai iya kasance wa matashi ƙalubale domin sa’ad da ya balaga, yaro ko yarinya da a dā yake yawan magana zai ko za ta iya koma mai jin kunya sosai. Masana sun ce matasa sai su ji a kullum kamar suna kan fage kuma ana haska masu wuta domin jama’a su kalle su. Maimakon su sha kan irin wannan tunanin, wasu matasa masu kunya sai su ja da baya kuma iyayensu su kasa fahimtar abin da ke zuciyarsu.

Wata tangarɗa da ke hana tattaunawa ita ce neman ’yanci na matasa. Ba za ka iya guje wa gaskiyar cewa ɗanka na girma ba kuma wata alamar hakan ita ce ware kansa daga iyali. Hakan baya nufin cewa ɗanka ya kai ya bar gida. A hanyoyi masu yawa yanzu zai bukaci taimakonka fiye da dā. Amma, wariya tana somawa ne da daɗewa kafin a cika mutum. Matasa da yawa sun fi so su yi tunani da kansu kafin su faɗi abin da ke zuciyarsu, domin hakan hanya ce ta girma.

Hakika, matasa ba sa yawan ɓoye wa juna tunaninsu, kamar yadda wata mata mai suna Jessica a Mexico ta lura. Ta ce, “Sa’ad da ’yata take ’yar ƙarama, tana gaya mini matsalolinta. Amma yanzu kawayenta take gaya wa.” Idan ɗanka yana yin haka, kada ka kammala cewa ya daina ganin ka a matsayin mahaifinsa. Nazari ya nuna cewa ko da yake matasa ba sa furtawa, suna ɗaukan shawarar iyayensu da muhimmanci fiye da ta tsaransu. Amma, ta yaya za ka tabbata cewa ba ku daina tattaunawa ba?

Yadda Za a Shawo Kan Ƙalubale

A ce kana tuki a wata babbar hanya, miƙaƙƙiya mai tsawo. Za ka yi tafiyar mil masu yawa ba tare da ka bukaci gyara mai yawa ba ga sitiyarinka. Farat ɗaya, sai ka lura cewa da wata babban kwana a hanyar. Idan kana son motarka ta ci gaba da tafiya a kan hanyar, dole ne ka daidaita sitiyarin naka. Hakan yake sa’ad da yaronka ya zama matashi. Wataƙila a shekaru masu yawa da suka gabata, yadda kake renon ɗanka bai bukaci wani babban gyara ba. Amma a yanzu, rayuwar ɗanka ta canja kuma dole ne kai ma ka yi gyara. Ka yi wa kanka waɗannan tambayoyi na gaba.

▪ ‘Sa’ad da ɗana ko ’yata take son mu tattauna, zan kasance a shirye in yi hakan?’ Littafi Mai Tsarki ya ce: “Magana a kan kari Tana kama da tuntuwa na zinariya cikin kwanduna na azurfa.” (Misalai 25:11) Kamar yadda wannan nassin ya bayyana, asirin shine sanin lokacin da ya dace. Alal misali: Manomi ba zai iya hanzarta lokacin girbi, ko kuma ya hana shi zuwa ba. Sai dai ya yi abin da ya dace idan lokaci ya zo. Ƙila, da wani lokaci da ɗanka ya fi kasancewa da niyar tattaunawa. Ka yi amfani da wannan zarafi. Frances, wata gwauruwa a Ostareliya ta ce: “’Yata takan zo ɗakina da daddare, wani lokaci har mu yi kusan awa guda. Da shike ina barci da wuri, hakan yana da wuya, amma a waɗannan dare da muka raba, mun tattauna sosai.”

KA GWADA WANNAN: Idan ɗanka ba ya da niyar tattaunawa, ku yi wasu abubuwa tare, kamar su, fita yawo, fita tuki, ko kuma ku yi wasu Ayukan gida. Sau tari, a irin waɗannan lokatai matasa suna faɗin abin da ke zuciyarsu.

▪ ‘Shin na fahimci abin da furcin yake nufi?’ Ayuba 12:11 ta ce: “Kunne ba ya kan auna magana ba, Kamar yadda baki yana ɗanɗana abincinsa?” Yanzu kana bukatar ka “auna” abin da ɗanka ko ’yarka ya faɗa fiye da dā. Matasa sukan yi magana kamar dai abin da suke faɗa kullum haka yake. Alal misali, ’yarka ko ɗanka yana iya cewa, “ kullum kamar ɗan yaro kake ganina!” ko kuma “Ba ka taɓa sauraron abin da na ce ba!” Maimakon ka shiga jayayya a kan kalmomin nan “kullum” ko “taɓa,” ka san cewa maganar ’yarka ko ɗanka ba ta zahiri ba ce . Alal misali, “kullum kamar ɗan yaro kake ganina” na iya nufin “Ina gani ba ka yarda da ni ba” ko kuma “Ba ka taɓa sauraron abin da na ce ba” ƙila yana nufin “Ina son in gaya maka yadda nake ji.” Ka yi ƙoƙari ka fahimci abin da furcin ke nufi.

KA GWADA WANNAN: Yayin da ɗanka ya faɗi wata magana mai zafi, kana iya cewa: “Na ga ka ɓata rai kuma zan so in ji abin da kake da niyar faɗa. Ka gaya mini abin da ya sa kake gani kamar ina ɗaukan ka kamar ɗan yaro.” Sai ka saurara ba tare da ka karɓi magana a bakinsa ba.

▪ ‘Ina sa tattaunawa ta kasance da wuya ba da sani na ba ta wajen tilasta wa ɗana ya yi magana?’

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ana shibka ɗiyan adilci cikin salama domin masu-yin salama.” (Yaƙub 3:18) Ta wajen furcinka da halayenka, ka sa yanayin ya kasance na “salama” domin ɗanka ya kasance da niyar tattaunawa. Ka tuna cewa kai ne mai goyon bayan ɗanka. Saboda haka, yayin da ka ke tattaunawa da shi kada ka bi da shi kamar lauyan da yake so ya kayar da wani shaida a kotu. Ahn, wani mutum a Koriya ya ce: “Uba mai hikima ba zai furta kalamai kamar su, ‘Yaushe za ka girma?’ ko ‘Sau nawa zan gaya maka?’ Bayan na sha yin kuskure a wannan fanni, na lura cewa ’ya’yana maza sun ɓata rai ba kawai domin yadda nake bi da su ba amma kuma domin abin da na furta.”

KA GWADA WANNAN: Idan ’yarki ba ta son ta amsa tambaya, ki sake dabara. Alal misali, maimakon ki tambayi ’yarki ko yaya abubuwa suka kasance mata, ki faɗa mata yadda abubuwa suka kasance miki kuma ki lura ko za ta amsa. Idan kina son ki ji ra’ayin ’yar ki a kan wani batu, kada ki yi mata tambayoyi kai tsaye ba. Ki tambaye ta ra’ayin kawarta a kan batun. Sai ki tambaye ta shawarar da za ta ba wa kawartata.

Tattaunawa da matasa ba abu ba ne marar yiwuwa. Ka gyara yadda kake renon yaranka kamar yadda bukata ta kama. Ka nemi shawarar wasu iyaye da suka yi nasara a wannan fanni. (Misalai 11:14) Sa’ad da kake zance da ɗanka ko ’yarka ka ‘yi hanzarin ji, ka yi jinkirin yin magana, ka yi jinkirin yin fushi.’ (Yaƙub 1:19) Fiye da kome, kada ka fid da rai wajen renon yaranka “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.”—Afisawa 6:4.

KA TAMBAYI KANKA . . .

▪ Waɗanne canje-canje ne na lura a ɗiyata ko ɗana tun da ya zama matashi?

▪ Ta yaya zan kyautata ingancin tattaunawa ta?

[Akwati a shafi na 16]

Shawarwari Daga Iyaye

“Ɗana yana zance sosai sa’ad da muke tare da wasu. Bayan haka, sa’ad da muke tare, sai in ci gaba da tattauna da shi a kan batutuwa da muka yi zancensu lokacin da muke tare da mutane.”—ANGELA A ITALIYA.

“Idan muka fara yabon yaranmu kuma mun furta cewa muna ƙaunarsu sosai, sai su gaya mana abin da ke zuciyarsu.”— DONIZETE A BRAZIL.

“Na tattauna da manya da aka yi renonsu bisa mizanan Littafi Mai Tsarki kuma na tambaye su yadda suka ji sa’ad da suke matasa da kuma yadda iyayensu suka taimaka masu. Hakan ya sa na fahimci abubuwa masu yawa.”—DAWN A BRITANIYA.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba