Masu Karatu Sun Yi Tambaya
Mulkin Allah Yana Zuciyarka Ne?
Yawancin mutane a yau suna ganin cewa amsar wannan tambayar e ce. Alal misali, littafin nan The Catholic Encyclopedia ya ce: “Mulkin Allah na nufin yadda Allah yake sarauta a zuciyarmu.” Malaman addinai suna koyar da wannan ra’ayi. Shin Littafi Mai Tsarki ainihi ya koyar da cewa Mulkin Allah a zuciyar ’yan adam yake?
Wasu suna tunani cewa Yesu ne da kansa ya fara gabatar da wannan ra’ayin cewa Mulkin Allah na cikin zuciyar mutane. Hakika, Yesu ya ce: “Mulkin Allah a tsakaninku yake.” (Luka 17:21, Littafi Mai Tsarki) Wasu sun fassara nan cewa “Duba, mulkin Allah yana cikinku.” Waɗannan juyin sun fassara furcin Yesu daidai kuwa? Yana nufi cewa Mulkin Allah yana cikin zuciyar ’yan adam ne?
Na farko, ka yi la’akari da yadda zuciyar ɗan adam take. Idan aka yi maganar zuciya ta alama a cikin Littafi Mai Tsarki, tana nufin mutum na ciki, tushen tunanin mutum, halayensa, da sosuwar zuciyarsa. Ra’ayin da wai abu mai girma kamar Mulkin Allah yana cikin zuciyar ’yan adam, yana iya kasancewa da ban sha’awa, musamman ma domin an ce yana iya canja mutum kuma ya ɗaukaka shi, amma irin wannan koyarwa na da tushe ne?
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Zuciya ta fi komi rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya.” (Irmiya 17:9) Yesu da kansa ya ce: “Abin da ke fitowa daga cikin mutum, shi ke ƙazantadda mutum. Gama daga ciki, daga cikin zuciyar mutum, miyagun tunani ke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, kwaɗai, mugunta.” (Markus 7:20-22) Ka yi tunanin wannan: Masifu da muke gani a duniyarmu ta yau daga zuciya mai zunubi na ’yan adam suka fito. To, ta yaya Mulkin Allah zai zo daga wannan tushe? Hakika, zuciyar ’yan adam ba za ta iya kawo Mulkin Allah ba yadda zaƙami ba zai iya ba da ’ya’yan ɓaure ba.—Matta 7:16.
Na biyu, ka yi la’akari da mutanen da Yesu yake musu magana sa’ad da ya faɗi kalmomi da ke Luka 17:21. Aya ta baya ta ce: “Da Farisawa suka tambaye shi lakacinda mulkin Allah za shi zo, ya amsa masu.” (Luka 17:20) Farisawa magabtan Yesu ne. Yesu ya faɗa cewa waɗannan masu riya ba za su shiga Mulkin Allah ba. (Matta 23:13) Idan Farisawa ba za su shiga cikin Mulkin Allah ba, Mulkin zai kasance cikin zuciyarsu kuwa? Da ƙyar! To, menene ainihi Yesu yake nufi?
Sa’ad da suke fassara wannan kalmomin Yesu, juyin Littafi Mai Tsarki masu yawa sun yi amfani da kalmomi da ya yi daidai da waɗanda ke cikin New World Translation. Wasu sun ce Mulkin yana “cikinku” ko kuma “tsakaninku.” Ta yaya Mulkin Allah yake tsakanin mutanen wannan zamanin, har da Farisawa? Yesu ne Jehobah Allah ya naɗa ya zama Sarkin Mulkin. Da yake shi ne Sarkin da aka naɗa, Yesu yana tsakanin waɗannan mutanen. Ya koyar game da Mulkin Allah kuma ya yi mu’ujizai, yana nuna musu abin da Mulkin zai yi. A wannan azancin, Mulkin yana tsakaninsu.
A bayyane yake cewa babu inda Nassi ya goyi bayan wannan ra’ayin cewa Mulkin Allah yana cikin zuciyar ’yan adam. Maimakon haka, gwamnati ce ta gaske da za ta kawo canji a duniya, yadda annabawa suka annabta.—Ishaya 9:6, 7; Daniel 2:44.