Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 7/1 pp. 27-31
  • “Ku Rinjayi Mugunta Da Nagarta”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Rinjayi Mugunta Da Nagarta”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ya Hasala, Ya Ji Haushi Ƙwarai”
  • ‘Sai Mun Kashe Ku’
  • “Mu Zo, Mu Gamu”
  • Yin Shelar Bishara Duk da Mugunta
  • Darussa Daga Littafin Nehemiah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Ka Tuna da Ni, Ya Allahna, Tare da Alheri”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ganuwar Urushalima
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ganuwar Urushalima
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 7/1 pp. 27-31

“Ku Rinjayi Mugunta Da Nagarta”

“Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.”—ROMAWA 12:21.

1. Me ya sa muke da tabbaci cewa za mu iya cin nasara bisa mugunta?

ZA MU iya tsayayya da waɗanda suke hamayya da bauta ta gaskiya kuwa? Za mu iya mu sha kan tasirin da ke ƙoƙarin komar da mu cikin duniya marar ibada? Amsar waɗannan tambayoyin ita ce e! Me ya sa muka faɗi haka? Saboda abin da manzo Bulus ya ce a wasiƙarsa ga Romawa. Ya Rubuta: “Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.” (Romawa 12:21) Idan muka dogara da Jehobah kuma muka ƙudurta cewa ba za mu yarda duniya ta yi nasara a kan mu ba, muguntarta ba za ta sha kanmu ba. Bugu da ƙari, furcin nan “ku rinjayi mugunta” ya nuna cewa za mu iya cin nasara bisa mugunta idan muka ci gaba da ƙoƙartawa a yaƙinmu na ruhaniya. Wannan muguwar duniya da mugun shugabanta, Shaiɗan Iblis, za su sha kan waɗanda suka daina kasancewa a faɗake da kuma waɗanda suka daina yaƙi na ruhaniya ne kawai.—1 Yohanna 5:19.

2. Me ya sa za mu tattauna waɗansu abubuwan da suka auku a rayuwar Nehemiya?

2 A shekaru 500 kafin zamanin Bulus, wani bawan Allah da yake zaune a Urushalima ya nuna gaskiyar kalaman Bulus game da yaƙi da mugunta. Wannan mutumin Allah, Nehemiya, ya tsayayya wa matsi daga mutanen da ba sa bauta wa Allah kuma ya rinjayi mugunta da nagarta. Waɗanne ƙalubale ne ya fuskanta? Menene ya taimake shi ya ci nasara? Ta yaya za mu iya yin koyi da misalinsa? Don mu amsa waɗannan tambayoyin, bari mu tattauna waɗansu abubuwan da suka auku a rayuwar Nehemiya.a

3. A wane irin wuri ne Nehemiya ya zauna, kuma me ya cim ma?

3 Nehemiya yana aiki ne a fadan Sarki Artaxerxes na Farisa. Ko da yake Nehemiya yana zaune ne a cikin marasa bi, bai “biye wa zamanin” nan ba. (Romawa 12:2) Sa’ad da wata bukata ta taso a Yahuda, ya saɗaukar da rayuwa ta jin daɗin da yake yi, ya yi tafiya mai gajiyarwa zuwa Urushalima, ya kuma yi aiki mai wuya na sake gina ganuwar birnin. (Romawa 12:1) Ko da yake shi ne shugaba a Urushalima, Nehemiya ya yi aiki tuƙuru da ’yan’uwansa Isra’ilawa “daga fitowar rana har tamrari suka bayana.” A sakamakon haka, sun ƙarasa ginin bayan watanni biyu! (Nehemiah 4:21; 6:15) Wannan abin mamaki ne, saboda lokacin da ake ginin, Isra’ilawa sun fuskanci hamayya dabam dabam. Su wanene suke hamayya da Nehemiya, kuma menene burinsu?

4. Menene burin masu hamayya da Nehemiya?

4 Ainihin masu hamayyar su ne Sanballat, Tobiah, da kuma Geshem, waɗannan mutane ne masu iko da suke zaune kusa da Yahuda. Tun da su maƙiyan mutanen Allah ne, “ya ɓāta musu zuciya ƙwarai, da shi ke [Nehemiya] ya zo . . . biɗan lafiyar ’ya’yan Isra’ila.” (Nehemiah 2:10, 19) Abokan gaban Nehemiya sun ƙudurta ɓata shirin Nehemiya na ginin, har ya kai ga yin ƙulle-ƙulle na mugunta. Nehemiya zai yarda ‘mugunta ta rinjaye’ shi kuwa?

“Ya Hasala, Ya Ji Haushi Ƙwarai”

5, 6. (a) Ta yaya ne abokan gaban Nehemiya suka ɗauki aikin ginin? (b) Me ya sa ’yan hamayyar suka kasa tsorata Nehemiya?

5 Da gaba gaɗi Nehemiya ya umurci mutanensa: ‘Bari mu gina ganuwar Urushalima.’ Suka ce: “Mu yi ta gini.” Nehemiya ya ce: “Suka ƙarfafa hannuwansu fa domin wannan nagarin aiki,” amma sai ’yan hamayyar suka soma yi musu ba’a suna cewa, “Mi ne wannan da ku ke yi? Za ku tayas ma sarki?” Nehemiya bai tsorata da ba’a da kuma zargin ƙaryar da suke yi ba. Ya ce wa ’yan hamayyar: “Allah na sama, shi za ya arzutadda mu: domin wannan mu bayinsa za mu tashi mu yi gini.” (Nehemiah 2:17-20) Nehemiya ya ƙudurta cewa zai ci gaba da “wannan nagarin aiki.”

6 Sanballat, ɗaya daga cikin ’yan hamayyar “ya hasala, ya ji haushi ƙwarai” ya ci gaba da yi musu ba’a yana cewa: “Waɗannan Yahudawa fa, rabkana, mi su ke yi?” “Za su sake rayadda duwatsu daga cikin tullai na jibjai?” Tobiah ma ya soma nasa ba’ar, yana cewa, “Abin da su ke gina fa, ko dila ta hau kan, sai ta karye bangonsu na dutse.” (Nehemiah 4:1-3) Menene Nehemiya ya yi?

7. Menene Nehemiya ya yi game da zargin ƙarya na ’yan hamayya?

7 Nehemiya ya yi banza da ba’a da suke yi. Ya bi umurnin Allah kuma bai yi ƙoƙarin ramawa ba. (Leviticus 19:18) Maimakon haka, ya bar komi a hannun Jehobah kuma ya yi addu’a: “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana rena mu: ka juyasda zarginsu a bisa kansu.” (Nehemiah 4:4) Nehemiya ya dogara da tabbacin da Jehobah ya bayar: “Ramawa gareni ta ke, da sakamako kuma.” (Kubawar Shari’a 32:35) Bugu da ƙari, Nehemiya da mutanensa suka ci gaba da “gina ganuwa.” Ba su bar wani abu ya raba hankalinsu ba. Hakika, “dukan ganuwa fa ta harhaɗu har ga rabin tsawonta: gama jama’a suna da nufin aiki.” (Nehemiah 4:6) Maƙiyan bauta ta gaskiya sun kasa tsayar da aikin ginin! Ta yaya za mu yi koyi da Nehemiya?

8. (a) Ta yaya za mu yi koyi da Nehemiya sa’ad da ’yan hamayya suka yi mana zargin ƙarya? (b) Ka ba da labarin abin da ka gani ko ka taɓa ji da ya nuna amfanin ƙin ramuwa?

8 A yau, ’yan hamayya a makaranta, wajen aiki, ko a gida suna iya yi mana ba’a da kuma zargin ƙarya. Amma, a yawancin lokaci ya fi kyau a yi amfani da ƙa’ida na Nassosi, da ya ce: “Akwai lokacin . . . shuru,” a irin waɗannan zargin ƙarya. (Mai-Wa’azi 3:1, 7) Saboda haka, kamar Nehemiya, muna guje wa yin ramuwa da baƙar magana. (Romawa 12:17) Amma mu yi addu’a ga Allah, kuma mu dogara ga wanda ya tabbatar da mu cewa: “Ni zan yi sakamako.” (Romawa 12:19; 1 Bitrus 2:19, 20) Ta haka, ba za mu bari ’yan hamayya su janye hankalinmu daga aiki na ruhaniya da ake yi a yau ba, wato, aikin wa’azin bisharar Mulkin Allah da kuma almajirantarwa. (Matta 24:14; 28:19, 20) Duk lokacin da muka kasance a aikin wa’azi kuma ba mu ƙyale ’yan hamayya su hana mu yin aikin ba, muna nuna irin aminci da Nehemiya ya nuna.

‘Sai Mun Kashe Ku’

9. Wane irin hamayya ne maƙiyan Nehemiya suka yi musu, kuma menene Nehemiya ya yi?

9 Sa’ad da masu hamayya da bauta ta gaskiya a zamanin Nehemiya suka ji labarin cewa “gyaran ganuwa ta Urushalima yana cin gaba,” sai suka ɗauki takubbansu don su yi “yaƙi da Urushalima.” Yahudawan sun damu. Ga ’yan Samariya a arewa, Ammonawa a gabas, Larabawa a kudu da kuma Ashdodawa a yamma. An kewaye Urushalima; kuma kamar an tsare masu aikin ginin! Menene za su yi? Nehemiya ya ce: “Muka yi addu’armu ga Allahnmu.” Maƙiyan suka yi mana barazana suka ce: ‘Sai mun kashe ku, mu sa aikin shi ƙare.’ Nehemiya ya ɗauki mataki ta wajen ba masu ginin aikin kāre birnin “da takubansu, da māsunsu, da bakankunansu.” Hakika, a zahiri, Yahudawa kaɗan ba za su iya yin nasara bisa maƙiyansu masu yawa ba, amma Nehemiya ya aririce su: “Kada ku ji tsoronsu . . . Ku tuna da Ubangiji, wanda shi ke mai-girma, mai-ban razana.”—Nehemiah 4:7-9, 11, 13, 14

10. (a) Menene ya sa maƙiyan Nehemiya suka janye farat ɗaya? (b) Waɗanne matakai ne Nehemiya ya ɗauka?

10 Sai yanayin ya canja farat ɗaya. Maƙiyan suka janye. Me ya sa? Nehemiya ya ce: “Allah ya wofinta shawarassu.” Duk da haka, Nehemiya ya fahimci cewa maƙiyan suna iya kawo masu hari a kowane lokaci. Saboda haka, sai ya sake wa masu ginin tsarin aiki. Tun daga lokacin, “kowane yana aiki da ɗayan hannunsa a cikin aiki, da ɗayan hannu kuma yana riƙe da makaminsa.” Nehemiya kuma ya ba wani aikin tsaro idan maƙiyan suna zuwa sai ya ‘busa ƙaho’ don ya sanar da maginan. Mafi muhimmanci, Nehemiya ya tabbatar da mutanen cewa: ‘Allahnmu za ya yi yaƙi dominmu.’ (Nehemiah 4:15-20) Maginan sun ci gaba da aikin saboda sun sami ƙarfafa kuma a shirye suke su yi faɗa. Waɗanne darussa ne za mu koya daga wannan labarin?

11. Menene ya sa Kiristoci na gaskiya suka tsayayya wa mugunta a ƙasashen da aka hana aikin Mulki, kuma ta yaya suka rinjayi mugunta da nagarta?

11 A wani lokaci Kiristoci na gaskiya suna fuskantar mugun hamayya. Hakika, a wasu ƙasashe waɗanda suke mugun hamayya da bauta ta gaskiya suna tara magabta masu yawa. A zahiri, ba yadda ’yan’uwanmu da suke waɗannan ƙasashen za su yi. Duk da haka, waɗannan Shaidu sun tabbata cewa ‘Allah zai yi yaƙi dominsu.’ Hakika, waɗanda aka tsananta wa domin bangaskiyarsu, sun shaida cewa Jehobah yana amsa addu’o’insu kuma yana ‘wofinta shawarar’ maƙiya masu ƙarfi. Har a ƙasashen da aka hana yin wa’azin Mulki, Kiristoci sukan nemi zarafin da za su ci gaba da shelar bishara. Kamar yadda magina a Urushalima suka canja tsarin aikinsu, Shaidun Jehobah a yau suna canja tsarin wa’azinsu sa’ad da suke fuskantar matsi. Hakika, suna guje wa yin amfani da makaman yaƙi na zahiri. (2 Korinthiyawa 10:4) Ko barazanar mugunta na zahiri ba ta hana su yin wa’azi. (1 Bitrus 4:16) Maimakon haka, waɗannan ’yan’uwa masu gaba gaɗi sun ci gaba da ‘rinjayar mugunta da nagarta.’

“Mu Zo, Mu Gamu”

12, 13. (a) Wace dabara ce maƙiyan Nehemiya suka yi amfani da ita? (b) Me ya sa Nehemiya bai yarda da gayyatar da masu hamayya da shi suka yi masa ba?

12 Da maƙiyan Nehemiya suka ga cewa harin da suka kai bai yi nasara ba, sai suka koma yin amfani da dabaru. Hakika sun gwada hanyoyi uku. Waɗanne hanyoyi uku ne?

13 Na farko, maƙiyan Nehemiya sun yi ƙoƙari su ruɗe shi. Suka ce masa: “Mu zo, mu gamu a cikin ɗayan ƙauyukan nan a cikin kwarin Ono.” Ono yana tsakanin Urushalima da Samariya. Sai maƙiyan suka ce wa Nehemiya su haɗu a Ono don su daidaita rashin fahimtar. Da Nehemiya ya yi tunani: ‘Wannan daidai ne. Ya fi kyau a daidaita da a yi faɗa.’ Amma Nehemiya bai yarda ba. Ya bayyana abin da ya sa: “Za su yi mani ta’ada.” Ya fahimci shirinsu shi ya sa bai yarda ba. Ya gaya wa maƙiyansa sau huɗu: “Ina yin wani aiki mai-girma, da ba zan iya zuwa ba: don mi za a dena aiki yayinda ina barinsa ina zuwa wurinku?” Duka ƙoƙarin da maƙiyan suka yi don su rinjayi Nehemiya bai yi nasara ba. Ya mai da hankalinsa ga aikin ginin.—Nehemiah 6:1-4.

14. Menene Nehemiya ya yi game da zargin ƙaryar da aka yi masa?

14 Na biyu, maƙiyan Nehemiya suka soma yaɗa jita-jitar ƙarya, suna zargin Nehemiya da “nufin tayaswa” Sarki Artaxerxes. Sai kuma suka ce wa Nehemiya: “Ka zo fa yanzu, mu yi shawara.” Nehemiya ya ƙi, saboda ya gane nufin maƙiyan. Nehemiya ya bayyana: “Duka su tsoratadda mu, cewa su ke yi, Hannuwansu za su yi suwu a cikin aikin, har da ba za a yi shi ba.” A wannan lokacin, Nehemiya ya mai da martani ga zargin ƙaryar da maƙiyansa suka yi, yana cewa: “Abin da ka faɗi duka ba a yi irinsa ba, amma daga cikin zuciyarka ka cire su.” Bugu da ƙari, Nehemiya ya roƙi Jehobah ya taimake shi, ya yi addu’a: “Ka ƙarfafa hannuwana.” Ya tabbata cewa da taimakon Jehobah, zai iya lalata mugun ƙullin da aka yi kuma ya ci gaba da aikin ginin.— Nehemiah 6:5-9.

15. Wace shawara ce wani annabin ƙarya ya yi, kuma me ya sa Nehemiya bai yarda da shawarar ba?

15 Na uku, maƙiyan Nehemiya sun yi amfani da Shemaiya ɗan Isra’ila maci amana, don ya rinjayi Nehemiya ya taka dokar Allah. Shemaiya ya ce wa Nehemiya: “Bari mu haɗu a cikin gidan Allah, daga cikin haikali, mu rufe ƙofofin haikali: gama suna zuwa su kashe ka.” Shemaiya ya ce wai ana nan tafe za a kashe Nehemiya, amma zai iya ceton ransa idan ya shiga cikin haikalin. Amma, Nehemiya ba firist ba ne. Zai yi zunubi idan ya ɓoye a cikin gidan Allah. Zai taka dokar Allah ne don yana son ya tsira? Nehemiya ya ce: “Wanene kuwa, irina, da za ya shiga haikali garin ya tsira da ransa? Ba ni shiga.” Me ya sa Nehemiya bai faɗa tarkon da aka kafa masa ba? Saboda ya san cewa ko da yake Shemaiya ɗan Isra’ila ne kamarsa, “Allah ba ya aiko shi ba.” Hakika, annabin gaskiya ba zai shawarce shi ya taka Dokar Allah ba. Nehemiya kuma bai yarda maƙiyansa su rinjaye shi ba. Bayan haka, ya ce: “Hakanan aka gama ganuwa a kan kwana ashirin da biyar ga watan Elul, cikin kwana hamsin da biyu ke nan.”—Nehemiah 6:10-15; Litafin Lissafi 1:51; 18:7.

16. (a) Ta yaya za mu bi da abokan ƙarya, masu zargin ƙarya, da kuma ’yan’uwan ƙarya? (b) Ta yaya za ka nuna cewa za ka yi tsayin daka da bangaskiyarka a gida, a makaranta, ko kuma a wurin aiki ba?

16 Kamar Nehemiya, mu ma muna iya fuskantar mutanen da suke da’awar cewa su abokanmu ne amma abokan karya ne, masu zargin ƙarya, da kuma ’yan’uwan ƙarya. Wasu suna iya shawarce mu mu bar imaninmu. Suna iya gaya mana cewa idan muka ɗan nuna ƙwazo a bautar Jehobah, za mu iya neman abin duniya a lokaci guda. Amma, saboda mun mai da Mulkin Allah abu na farko a rayuwarmu, ba za mu yarda ba. (Matta 6:33; Luka 9:57-62) ’Yan hamayya kuma suna yaɗa zargin ƙarya game da mu. A wasu ƙasashe ana zarginmu cewa muna wa gwamnati barazana, kamar yadda aka zargi Nehemiya cewa yana wa sarki tawaye. An yi nasarar ƙaryata wasu zargin a kotu. Amma kowane sakamako ne muka samu, mun tabbata cewa Jehobah zai daidaita abubuwa bisa nufinsa. (Filibbiyawa 1:7) Waɗanda suke da’awar cewa suna bauta wa Jehobah za su iya yi mana hamayya. Kamar yadda ’yan’uwansa Yahudawa suka ƙoƙarta su rinjayi Nehemiya ya taka Dokar Allah don ya ceci ransa, haka nan ma ’yan ridda waɗanda a dā Shaidu ne, suna iya yin iya ƙoƙarinsu su rinjaye mu mu taka dokar Allah. Amma, muna ƙin ’yan ridda saboda mun san cewa za mu tsira ne kawai idan muka bi dokar Allah ba taka ta ba! (1 Yohanna 4:1) Hakika, da taimakon Jehobah za mu iya sha kan kowace irin mugunta.

Yin Shelar Bishara Duk da Mugunta

17, 18. (a) Menene Shaiɗan da mutanensa suke so su cim ma? (b) Menene ka ƙudurta za ka yi, kuma me ya sa?

17 Game da abokan Kristi shafaffu, Kalmar Allah ta ce: ‘Suka yi nasarar [a kan Shaiɗan] . . . saboda maganar shaidarsu.’ (Ru’ya ta Yohanna 12:11) Duk da haka, akwai dangantaka tsakanin yin nasara bisa Shaiɗan wanda shi ne tushen mugunta, da kuma yin wa’azin saƙon Mulki. Shi ya sa Shaiɗan yake kai hari ga shafaffun da suka rage da kuma “taro mai-girma.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9; 12:17.

18 Kamar yadda muka gani, ana iya yi mana hamayya ta wajen maganar baki, zalunci ko kuma ta hanyoyin wayo. Ko ta yaya ne, nufin Shaiɗan shi ne ya dakatar da aikin wa’azi. Amma, ba zai yi nasara ba, saboda kamar Nehemiya na dā, mutanen Allah sun ƙudurta cewa za su ci gaba da ‘rinjayar mugunta da nagarta.’ Za su yi haka ta wurin ci gaba da wa’azi har sai Jehobah ya ce aikin ya isa!—Markus 13:10; Romawa 8:31; Filibbiyawa 1:27, 28.

[Hasiya]

a Don ka fahimci abubuwan da suka auku, ka karanta Nehemiah 1:1-4; 2:1-6, 9-20; 4:1-23; 6:1-15.

[Akwati a shafi na 29]

Darussa da ke cikin Littafin Nehemiya

Bayin Allah suna fuskantar

• ba’a

• barazana

• rinjaya

Waɗanda suke rinjaya sune

• abokan ƙarya

• masu zargin ƙarya

• ’yan’uwan ƙarya

Bayin Allah sun yi nasara bisa mugunta ta wajen

• manne wa aikin da Allah ya ba su

[Akwati a shafi na 31]

Ka Tuna?

• Wace hamayya ce mutanen Allah suka fuskanta a dā kuma Kiristoci a yau suna fuskantarta?

• Menene nufin maƙiyan Nehemiya, kuma menene nufin maƙiyan Allah yau?

• Ta yaya ne muke rinjayar mugunta da nagarta a yau?

[Hoto a shafi na 27]

Nehemiya da abokan aikinsa sun gina ganuwar Urushalima duk da matsi daga wurin ’yan hamayya

[Hoto a shafi na 31]

Kiristocin gaskiya suna wa’azi da gaba gaɗi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba