Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 8/1 pp. 12-16
  • Jehobah Yana Ceton Wanda Yake Wahala

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Ceton Wanda Yake Wahala
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sakamakon Wahala
  • Ajizancinmu Zai Iya Jawo Mana Wahala
  • Kasawarmu Zai Iya Sa Mu Sanyin Gwiwa
  • “Miyagun Zamanu” na Iya Sa Mu Sanyin Gwiwa
  • Matakai Masu Kyau na Sauƙaƙa Baƙin Ciki
  • Kasancewa a “Ƙarƙashin Hannu Mai-Iko na Allah”
  • Jehovah ‘Mai Kiyaye Mu A Lokatan Wahala’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehovah Yana Kula Da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Ci Gaba Da Farin Ciki A Lokacin Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 8/1 pp. 12-16

Jehobah Yana Ceton Wanda Yake Wahala

“Masifu na mai-adalci dayawa su ke: amma Ubangiji ya kan tsamarda shi daga cikinsu duka.”—ZABURA 34:19.

1, 2. Wace matsala ce wata Kirista mai aminci ta fuskanta, kuma me ya sa muke iya jin haka?

WATA matashiya mai suna Keikoa Mashaidiyar Jehobah ce fiye da shekaru 20. Wani lokaci, ta yi hidima na majagaba, ko kuma mai shelar Mulki na cikakken lokaci. Ta ɗauki wannan hidima da tamani. Amma ba da daɗewa ba, kaɗaici da jin ba ta da bege ya sha kan Keiko. “Sai kuka nake yi” in ji ta. Don ta daina baƙin cikinta, Keiko ta daɗa ba da lokaci wajen nazari. Ta ce “duk da haka, ban iya canja yanayi na ba. Na yi baƙin ciki sosai da har na fi son in mutu.”

2 Kai ma kana fama da irin wannan fid da rai ne? Da yake kai Mashaidin Jehobah ne, kana da dalili mai yawa na yin farin ciki domin ibada “tana da alkawari ga rai na yanzu, da na mai-zuwa.” (1 Timothawus 4:8) A yanzu kana cikin aljanna ta ruhaniya! Amma, wannan yana nufin cewa za a kāre ka daga dukan wahala ne? Da kyar! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masifu na mai-adalci dayawa su ke.” (Zabura 34:19) Wannan ba abin mamaki ba ne, domin “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Muna fuskantar sakamakon ikonsa a dukan duniya.—Afisawa 6:12.

Sakamakon Wahala

3. Ka ba da misalan bayin Allah a cikin Littafi Mai Tsarki da suka fuskanci baƙin ciki mai tsanani.

3 Baƙin ciki na dogon lokaci zai iya ɓata siffarmu. (Misalai 15:15) Ka yi la’akari da Ayuba mai adalci. Lokacin da yake cikin matsala mai tsanani, Ayuba ya ce: “Mutum, haihuwar mace kwanakinsa kaɗanna ne, cike da wahala kuma.” (Ayuba 14:1) Ayuba ya daina farin ciki. Akwai lokacin da ma yi tunani cewa Jehobah ya yashe shi. (Ayuba 29:1-5) Ba Ayuba kaɗai ba ne bawan Allah da ya fuskanci wahala mai tsanani. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Hannatu ta yi “ɓacin rai” domin ba ta haihu ba. (1 Samuila 1:9-11) Da take baƙin ciki game da wata damuwa cikin iyali, Rifkatu ta ce: “Na gaji da raina.” (Farawa 27:46) Sa’ad da yake tunani game da kurakuransa, Dauda ya ce: “Muddar yini ina tafiya ina makoki.” (Zabura 38:6) Waɗannan ’yan misalai sun nuna sarai cewa kafin lokacin Kiristoci maza da mata masu jin tsoron Allah sun jimre wa baƙin ciki mai tsanani.

4. Me ya sa ba abin mamaki ba ne Kiristoci a yau suna “rarraunar zuciya”?

4 Kiristoci fa? Manzo Bulus ya ga ya dace ya gaya wa Tassalunikawa su “ƙarfafa masu rarraunar zuciya.” (1 Tassalunikawa 5:14) Wata majiya ta ce kalmar Helenanci da aka fassara “rarraunar zuciya” tana nufin waɗanda “wahalar rayuwa ta sha kansu na ɗan lokaci.” Kalmomin Bulus sun nuna cewa wasu da aka shafa da ruhu a ikilisiyar Tassalunika sun karai. A yau akwai waɗanda suka karai tsakanin Kiristoci. Amma me ya sa suka karai? Bari mu yi la’akari da dalilai uku.

Ajizancinmu Zai Iya Jawo Mana Wahala

5, 6. Wane ƙarfafa ne za a samu a Romawa 7:22-25?

5 Ba kamar lalatattun mutane da “sun wuce gaban su ji,” Kiristoci na gaskiya suna wahala don ajizancinsu. (Afisawa 4:19) Suna iya jin yadda Bulus ya ji, kuma ya rubuta: “Ina murna da shari’ar Allah bisa ga mutum na ciki: amma ina ganin wata shari’a dabam a cikin gaɓaɓuwana, tana yaƙi da shari’ar hankalina, tana saka ni bauta ƙarƙashin shari’ar zunubin nan da ke cikin gaɓaɓuwana.” Sai Bulus ya furta: “Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi!”—Romawa 7:22-24.

6 Ka taɓa jin yadda Bulus ya ji? Ba laifi ba ne ka san kai ajizi ne, domin wannan zai sa ka san tsananin zunubi kuma ya ƙarfafa ƙudurinka ka ƙi mugunta. Amma bai kamata ka ci gaba da baƙin ciki domin kasawarka ba. Kalmomin baƙin ciki na Bulus da aka yi ƙaulinsu ɗazu, ya daɗa: “Na gode ma Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Romawa 7:25) Hakika, Bulus yana da tabbaci cewa jinin da Yesu ya zubar zai fanshe shi daga zunubi da ya gada.—Romawa 5:18.

7. Menene zai taimaki mutum kada ya yi baƙin ciki ainun don muradinsa na yin zunubi?

7 Idan kana jin ajizancinka ya sha kanka, kalmomin manzo Yohanna za su ƙarfafa ka, ya rubuta: “Idan kowa ya yi zunubi, muna da Mai-taimako wurin Uba, Yesu Kristi mai-adalci: shi ne kuwa fansar zunubanmu; ba kuwa ta namu kaɗai ba, amma ta duniya duka kuma.” (1 Yohanna 2:1, 2) Idan ka damu don muradinka na yin zunubi, ka riƙa tuna cewa Yesu ya mutu don masu zunubi, ba don kamiltattu ba. Hakika, ‘dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.’—Romawa 3:23.

8, 9. Me ya sa za mu ƙi tunanin cewa ba mu da amfani?

8 Amma, a ce dā ka yi zunubi mai tsanani. Babu shakka, ka yi wa Jehobah addu’a game da batun, wataƙila sau da yawa. Ka sami taimako na ruhaniya daga dattawa. (Yaƙub 5:14, 15) Ka tuba da gaske kuma kana cikin ikilisiya. Ko kuma wataƙila ka bar ƙungiyar Allah na ɗan lokaci, amma daga baya ka tuɓa kuma ka kasance da matsayi mai tsabta. A kowane yanayi, za ka riƙa tuna zunubinka na dā kuma zai sa ka baƙin ciki. Idan hakan ya faru, ka tuna cewa Jehobah yana gafarta wa waɗanda suka tuɓa da gaske “a yalwace.” (Ishaya 55:7) Ƙari ga haka, ba ya son ka ji ba ka da amfani. Shaiɗan ne yake so ka ji hakan. (2 Korinthiyawa 2:7, 10, 11) Za a halaka Iblis domin ya cancanci hakan, amma zai so ka ji cewa ka cancanci a yi maka hakan. (Ru’ya ta Yohanna 20:10) Kada ka bar Shaiɗan ya yi nasara a wannan ƙulli don ya hallaka bangaskiyarka. (Afisawa 6:11) Maimakon haka, ‘ka tsaya masa fa’ game da wannan, yadda ka yi a wasu hanyoyi.—1 Bitrus 5:9.

9 A Ru’ya ta Yohanna 12:10, an kira Shaiɗan “mai-saran ’yan’uwanmu,” wato, shafaffu Kiristoci. Yana “sarassu dare da rana” a gaban Allah. Bimbini a kan wannan ayar zai taimake ka ka ga cewa Shaiɗan mai zargin ƙarya zai yi farin ciki idan ka sari kuma ka hukunta kanka, ko da Jehobah ba ya yin hakan. (1 Yohanna 3:19-22) Me ya sa za ka ci gaba da baƙin ciki game da kasawarka har da za ka ji kamar ka daina bauta wa Allah? Kada ka bar Shaiɗan ya halaka dangantakarka da Allah. Kada ka bar Iblis ya sa ka mance cewa Jehobah mai “juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai” ne.—Fitowa 34:6.

Kasawarmu Zai Iya Sa Mu Sanyin Gwiwa

10. A waɗanne hanyoyi ne kasawarmu za ta iya sa mu sanyin gwiwa?

10 Wasu Kiristoci sun yi sanyin gwiwa domin yadda kasawarsu take shafan hidimarsu ga Allah. Haka kake ji ne? Mai yiwuwa ciwo mai tsanani, tsufa, ko kuma wasu yanayi suna hana ka ba da lokaci a hidima yadda kake yi a dā. Hakika, an ƙarfafa Kiristoci su rifta zarafi don hidimar Allah. (Afisawa 5:15, 16) Amma idan kasawa da gaske tana hana ka ƙara ƙwazo a hidima kuma wannan na sa ka sanyin gwiwa fa?

11. Ta yaya gargaɗin Bulus da ke rubuce a Galatiyawa 6:4 zai amfane mu?

11 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu kada mu yi nauyin jiki amma mu “zama masu-koyi da waɗanda ke gāda alkawura ta wurin bangaskiya da haƙuri.” (Ibraniyawa 6:12) Za mu iya yin haka idan muka bincika misalinsu mai kyau kuma muka yi koyi da bangaskiyarsu. Amma ba za mu amfana ba idan muka gwada kanmu da wasu yadda bai dace ba kuma muka kammala cewa ba abin da muke yi da yake da kyau. Saboda haka, yana da kyau mu yi biyayya da gargaɗin Bulus: “Bari kowane mutum shi auna nasa aiki, sa’annan za ya sami fahariyarsa bisa ga zancen kansa kaɗai, ba ga zancen wani ba.”—Galatiyawa 6:4.

12. Me ya sa za mu yi farin ciki a hidimar da muke yi wa Jehobah?

12 Kiristoci suna da dalili mai kyau na yin farin ciki, ko da rashin lafiya mai tsanani ya rage abin da suke yi. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana: “Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi.” (Ibraniyawa 6:10) Mai yiwuwa yanayi da ya sha kanka ya sa yana maka wuya ka yi abubuwa da kake jin daɗin yi a dā. Da taimakon Jehobah, za ka iya yin wasu fannonin hidimar Kirista, kamar yin wa’azi ta tarho da kuma rubuta wasiƙa. Ka tabbata cewa Jehobah Allah zai albarkace ka don hidima da dukan zuciyarka da ƙauna da kake nuna masa da ’yan’uwa masu bi.—Matta 22:36-40.

“Miyagun Zamanu” na Iya Sa Mu Sanyin Gwiwa

13, 14. (a) A waɗanne hanyoyi ne waɗannan “miyagun zamanu” za su jawo mana wahala? (b) Ta yaya ake ganin rashin ƙauna a yau?

13 Ko da muna sauraron rayuwa a sabuwar duniya mai adalci ta Allah, a yanzu muna zama a “miyagun zamanu.” (2 Timothawus 3:1) Za mu ƙarfafa ta sanin cewa wahala ta nuna cewa cetonmu ya kusa. Duk da haka, yanayi da ya kewaye mu yana shafanmu. Alal misali, idan ba ka da aiki fa? Aiki yana iya kasancewa da wuyan samu, kuma da shigewar watanni za ka yi mamaki ko Jehobah yana ganin yanayinka ko kuma yana jin addu’arka. Ko kuma ka zama wanda aka yi wa wariya ko wani rashin adalci. Idan ka karanta jigon jarida za ka iya jin yadda Lutu mutum mai adalci ya ji, wanda “ransa ya ɓaci ƙwarai” don masu mugunta da suka kewaye shi.—2 Bitrus 2:7.

14 Da akwai wani fanni na musamman na kwanaki na ƙarshe da ba za mu yi banza da shi ba. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutane da yawa za su zama “marasa-ƙauna irin na tabi’a.” (2 Timothawus 3:3) Babu ƙauna cikin iyalai da yawa. Hakika, “tabbaci ya nuna cewa waɗanda suke cikin iyali ne suka fi kashe mutanen da ke cikin iyalinsu, kuma su yi musu duka, ko kuma su nemi su yi iskanci da su,” in ji littafin Family Violence. “Wurin da ya kamata a ƙaunaci mutane kuma su sami kwanciyar rai ne ya fi haɗari ga wasu yara da manya.” Waɗanda suke cikin yanayin iyali da ba shi da kyau a shekaru ta nan gaba za su fuskanci alhini da baƙin ciki. Idan hakan ya same ka fa?

15. Ta yaya ƙaunar Jehobah ta fi na kowane ɗan adam kyau?

15 Mai zabura Dauda ya rera waƙa: “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni.” (Zabura 27:10) Abin ƙarfafa ne mu sani cewa ƙaunar Jehobah ta fi ta dukan iyaye ’yan adam! Ko da ƙi, zalunci, ko kuma yasarwa na iyaye zai iya sa ka baƙin ciki, amma hakan ba ya shafan yawan yadda Jehobah yake kula da kai. (Romawa 8:38, 39) Ka tuna cewa Allah yana jawo waɗanda suke ƙaunarsa. (Yohanna 3:16; 6:44) Ko yaya ’yan adam suka bi da kai, Ubanka na samaniya yana ƙaunarka!

Matakai Masu Kyau na Sauƙaƙa Baƙin Ciki

16, 17. Sa’ad da mutum yake baƙin ciki, menene zai yi don ya ci gaba cikin ƙarfinsa na ruhaniya?

16 Za ka ɗauki matakai masu kyau don ka jimre da baƙin ciki. Alal misali, ka bi tsarin ayyukan Kirista mai kyau. Ka yi bimbini a kan Kalmar Allah, musamman sa’ad da sanyin gwiwa ya nemi ya sha kanka. Mai zabura ya rera waƙa yana cewa: “Sa’anda na ce, Ƙafata tana talalabiya, jinƙansa ya tagaje ni, ya Ubangiji. A cikin yawan wusuwasi da ke cikina ta’aziyyanka suna ji ma raina daɗi.” (Zabura 94:18, 19) Karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai zai cika zuciyarka da kalmomi na ta’aziyya da na ƙarfafa.

17 Addu’a ma tana da muhimmanci. Ko idan ma ba za ka iya furta ainihin yadda kake ji ba, Jehobah ya san abin da kake son ka faɗa. (Romawa 8:26, 27) Mai zabura ya ba da wannan tabbacin: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya agaje ka: Ba za ya yarda a jijjiga masu-adalci ba daɗai.”—Zabura 55:22.

18. Waɗanne abubuwa ne mai baƙin ciki zai yi?

18 Baƙin cikin wasu mutane ciwo ne.b Idan wannan ne matsalarka, ka yi ƙoƙari ka mai da hankali ga sabuwar duniya ta Allah da kuma lokacin da “wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) Idan kana baƙin ciki a kai a kai, zai fi kyau ka nemi taimako wurin likita. (Matta 9:12) Yana da muhimmanci ka kula da lafiyar jikinka. Abinci mai gina jiki da kuma motsa jiki zai ƙara mana lafiya. Ka tabbata kana samun isashen hutu. Kada ka cika yin dare kana kallon talabijin, ka guji nishaɗi da zai gajiyar da kai ainun. Mafi muhimmanci, ka ci gaba da yin ayyuka na ibada! Ko da lokaci bai kai ba da Jehobah zai “share dukan hawaye” zai taimake ka ka jimre.—Ru’ya ta Yohanna 21:4; 1 Korinthiyawa 10:13.

Kasancewa a “Ƙarƙashin Hannu Mai-Iko na Allah”

19. Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa waɗanda suke wahala?

19 Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa ko da masifu na adali suna da yawa, “Ubangiji ya kan tsamarda shi daga cikinsu duka.” (Zabura 34:19) Ta yaya Allah yake yin haka? Sa’ad da manzo Bulus ya yi addu’a a kai a kai a cire masa “masuki cikin jiki” Jehobah ya gaya masa: “Cikin kumamanci ikona ya ke cika.” (2 Korinthiyawa 12:7-9) Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa Bulus, alkawarin menene ya yi maka? Ba warkarwa na zamani ba ne, amma ƙarfin jimrewa.

20. Duk da gwajinmu, menene 1 Bitrus 5:6, 7 suka tabbatar mana?

20 Manzo Bitrus ya rubuta: “Ku ƙasƙantarda kanku . . . ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah, domin shi ɗaukaka ku loton da ya zama daidai; kuna zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:6, 7) Domin Jehobah yana kula da kai, ba zai yasar da kai ba. Zai tallafa maka duk da gwaji da kake fuskanta. Ka tuna cewa Kiristoci masu aminci suna “ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah.” Yayin da muke bauta wa Jehobah, yana ba mu ƙarfin jimrewa. Idan mun kasance da aminci a gare shi, ba abin da zai mana lahani na dindindin a ruhaniya. Saboda haka, bari mu kasance da aminci ga Jehobah domin mu more rai madawwami a cikin sabuwar duniya da aka yi alkawarinta kuma mu ga ranar da zai ceci wanda yake wahala na dindindin!

[Hasiya]

a An canja sunan.

b Irin wannan baƙin cikin ba sanyin gwiwa ba ne kawai, amma ciwo ne mai tsanani. Don ƙarin bayani, ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Oktoba, 1988, shafuffuka na 25-29; 15 ga Nuwamba, 1988, shafuffuka na 21-24; da kuma 1 ga Satumba, 1996, shafuffuka na 30-31 duka a Turanci.

Ka Tuna?

• Me ya sa wahala ke shafan bayin Jehobah?

• Waɗanne abubuwa ne za su sa wasu cikin mutanen Allah su yi baƙin ciki?

• Ta yaya Jehobah yake taimakonmu mu jimre da alhini?

• Ta yaya muke cikin “ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah”?

[Hotuna a shafi na 12]

Ko da suna fuskantar gwaji, mutanen Jehobah suna da dalilin farin ciki

[Hoto a shafi na 15]

Wa’azi ta tarho, hanya ɗaya ce da za ka yi wa Jehobah hidima da dukan zuciyarka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba