Halin Kirki Yana Kawo Albarka
A WANI ƙaramin tsibiri a kudancin Japan, wata mace da ’ya’yanta uku suka fara nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Da maƙwabtanta suka ga haka sai suka fara yin banza da ita duk lokacin da suka ganta. “Abin da ya fi damu na fiye da yin banza da ni shi ne cewa haka suke yi da maigidana da ’ya’ya na ma,” in ji ta. Duk da haka, ta gaya wa ’ya’yanta: “Dole ne mu ci gaba da gaishe da maƙwabtanmu domin Jehobah.”—Matiyu 5:47, 48.
A gida, ta koya wa ’ya’yanta su kasance da sauƙin hali ko da yake an ƙi su. Da suke kan hanyarsu zuwa rafi mai zafi da suka saba zuwa, yaran suka gwada yadda za su riƙa gaisuwa a cikin mota. Da suka shiga inda rafin yake, yaran suka riƙa cewa wa mutane, “Konnichiwa!” wato, “Barka da rana!” Iyalin suka ci gaba da gai da dukan mutane da suka sadu da su, ko da yake amsar maƙwabtan nasu ba na abokantaka ba ne. Duk da haka, mutane sun lura da halin kirki na yaran.
A ƙarshe, maƙwabtan ɗaɗɗaya suka fara amsa gaisuwar ta su da “Konnichiwa.” Bayan shekara biyu, kusan kowa yana amsa gaisuwarsu. Maƙwabtan suka fara gai da juna kuma suka zama abokan juna. Mataimakin mai gari ya so ya ba wa yaran lambar yabo domin taimako da suka yi wajen kawo wannan canji. Amma mamarsu ta gaya masa cewa suna yin abin da ya kamata Kiristoci su yi ne. Daga baya, a gasar lafazi na tsibirin, ɗaya daga cikin ’ya’yan ya faɗi yadda mamarsu ta koyar da su su gai da mutane ko yaya suka amsa. Lafazinsa ya yi nasara kuma aka buga a jarida. A yau, wannan iyali suna farin ciki ƙwarai da bin mizanai na Kirista da ya kawo irin wannan albarka. Yin aikin wa’azi ya fi sauƙi idan mutane suka kasance masu sauƙin hali.