Tambayoyi Daga Masu Karatu
A Isra’ila ta dā, menene ma’anar haske na mu’ujiza da ake kira Shechinah da ke bayyana a wuri Mafi Tsarki a mazauni da kuma haikali?
Jehobah, Uba mai ƙauna mai kuma kāre mutanensa, ya sa Isra’ila ta fahimci yana tare da ita. Hanya ɗaya da ya cim ma haka ita ce, ta wajen gajimare da ya danganci wurin bautarsa.
Wannan hasken na wakiltan kasancewar Jehobah marar ganuwa. Hasken ya kasance a wuri Mafi Tsarki na mazauni da haikalin da Sulemanu ya gina. Wannan haske na mu’ujiza ba ya nufin cewa Jehobah ne ke wurin. Allah ba zai iya kasancewa a gidan da mutum ya gina ba. (2 Tarihi 6:18; Ayyukan Manzanni 17:24) Wannan haske da ke cikin wuri mai tsarki na Allah na ba da tabbaci ga babban firist cewa Jehobah na kula da su da kuma bukatunsu, ta wurin firist kuma zuwa ga dukan Isra’ilawa.
A harshen Aramaic na bayan lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, an kira wannan hasken Shekina (shekhi·nahʹ), kalmar da ke nufin “abin da ke zaune” ko kuwa “da zama.” Babu wannan kalmar cikin Littafi Mai Tsarki amma tana cikin fassarar Aramaic na Nassosin Ibrananci wanda ake kira Targums.
Sa’ad da yake ba da umurni game da ginin mazauni, Jehobah ya gaya wa Musa: “Za ku sa murfin bisa akwatin. A cikin akwatin kuwa za ku sa allunan da ke da dokokin da zan ba ka. A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da ke bisa akwatin alkawari.” (Fitowa 25:21, 22) Akwatin da aka ambata akwati ne na gwal da ke cikin wuri Mafi Tsarki. Akwai kerubobi biyu na gwal bisa Akwatin.
Daga ina ne Jehobah zai yi magana? Ya ba da amsar sa’ad da ya ce wa Musa: “Zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.” (Littafin Firistoci 16:2) Wannan girgijen yana kewaye Akwatin mai tsarki da ke tsakanin kerubobi biyun na gwal. Littafi Mai Tsarki bai bayyana tsawon girgijen ba, da kuma tsawonsa bisa kerubobin.
Wannan girgijen yana haskaka wuri Mafi Tsarki. Hakan ita ce kawai hanyar haskaka wannan mazauni. Babban firist zai amfana daga wannan hasken sa’ad da ya shiga cikin ɗakin ciki ciki a Ranar Kafara. Yana tsaye ne a gaban Jehobah.
Wannan haske na mu’ujiza na da muhimmanci ga Kiristoci kuwa? Manzo Yahaya ya ga wani birni a wahayi wanda “ba kuwa za a yi dare a can ba.” Wannan birnin shi ne Sabon Urushalima, wanda ya ƙunshi shafaffun Kiristoci waɗanda aka ta da daga matattu domin su yi mulki tare da Yesu. Wannan hasken birni na alama ba na rana ba ne ko wata. Ɗaukakar Jehobah Allah ce ke haskaka wannan ƙungiyar, kamar yadda girgijen Shekina ke haskaka wuri Mafi Tsarki. Kuma Ɗan Rago, Yesu Kristi, shi ne ‘fitilar’ birnin. Kuma wannan “birnin” yana ba da haske na ruhaniya da kuma tagomashi ga mutanen da aka fanso daga dukan al’ummai don a yi musu ja-gora.—Wahayin Yahaya 21:22-25.
Domin sun sami albarka mai yawa daga sama, masu bauta wa Jehobah sun tabbata cewa shi ne Makiyayi mai kāre su kuma shi ne Ubansu mai ƙauna.