Ka Yi Tafiya Cikin Aminci
“Gama na yi abin da ke daidai [da aminci”]—ZABURA 26:11.
1, 2. (a) Me ya sa amincin mutum na da muhimmanci a batun ikon mallaka na Allah? (b) Ta yaya ne halittu masu basira za su nuna cewa suna ɗaukaka ikon mallaka na Jehovah?
SA’AD da Shaiɗan ya yi tawaye a lambun Aidan, ya ta da batun dacewar yadda Allah yake mallakar dukan halittunsa. Daga baya kuma ya yi zargin cewa mutane suna bauta wa Allah ne kawai muddin hakan za ta kawo musu moriya. (Ayuba 1:9-11; 2:4) Saboda haka, amincin mutum na da nasaba ta kusa da batun nan na ikon mallaka na Jehovah.
2 Allah zai ci gaba da kasancewa mamallaki ko halittunsa sun riƙe aminci ko ba su riƙe ba, mutane da ’ya’yan Allah na ruhu suna iya nuna matsayinsu a wannan batun. Ta yaya? Ta zaɓen ko za su bi tafarkin aminci ko ba za su bi ba. Saboda haka, amincin kowane mutum shi ne dalili mai ƙarfi da za a yi masa ko mata shari’a.
3. (a) Menene Ayuba da Dauda suke so Jehovah ya duba kuma ya yi shari’a? (b) Waɗanne tambayoyi ne suka taso game da aminci?
3 Da gaba gaɗi Ayuba ya ce: “Bari Allah ya auna ni da ma’aunin da ke daidai [da aminci], zai kuwa san mutuncina.” (Ayuba 31:6) Aminci ne Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya tambayi Jehovah ya duba sa’ad da ya yi addu’a: “Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji, gama na yi abin da ke daidai [da aminci], na dogara gare ka gaba ɗaya.” (Zabura 26:1) Yana da muhimmanci mu yi tafiya cikin aminci! Amma menene aminci, kuma me yake nufi mu yi tafiya cikin aminci? Menene zai taimaka mana mu kasance da aminci?
‘Na yi Abin da Ke Daidai’ da Aminci
4. Menene aminci?
4 Aminci na nufin kasancewa mai adalci, kamili, marar aibi. Amma fa, aminci ya ƙunshi fiye da yin abin da ke daidai. Ma’anarsa ta haɗa da ɗabi’a mai kyau ko cikakkiyar zuciya ta ibada ga Allah. Shaiɗan ya tuhumi dalilin Ayuba sa’ad da ya ce wa Allah: “Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai [Ayuba] ya fito fili ya zage ka.” (Ayuba 2:5) Ban da yin abin da ya dace, kasancewa da aminci na bukatar motsawa ta zuciya tare da yin ayyukan da suka dace.
5. Menene ya nuna cewa riƙe aminci ba ya bukatan sai mun kasance kamiltattu?
5 Riƙe aminci ba ya bukatar kasance kamiltacce. Sarki Dauda ajizi ne kuma ya yi kuskure sau da yawa sa’ad da yake raye. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya kira shi mutumin da ya yi tafiya “da aminci.” (1 Sarakuna 9:4) Me ya sa? Domin Dauda yana ƙaunar Jehovah. Ya ba da zuciyarsa ga Allah. Ya yarda da laifuffukansa, ya ji horo, kuma ya daidaita rayuwarsa. Hakika, mun ga amincin Dauda a ibadarsa da dukan zuciyarsa da ƙauna ga Allahnsa, Jehovah.—Maimaitawar Shari’a 6:5, 6.
6, 7. Menene yin tafiya cikin aminci ya ƙunsa?
6 Aminci bai tsaya a wani ɓangaren halayen mutane ba kawai, kamar ba da kai ga addini. Ya ƙunshi dukan hanyar rayuwarmu. Dauda ya yi “tafiya” cikin aminci. “Sunan nan ‘tafiya’ na nufin ‘tafarkin rayuwa’ ko kuma salon rayuwa,” in ji The New Interpreter’s Bible. Sa’ad da yake magana game da “marasa laifi cikin zamansu,” mai zabura ya rera waƙa: “Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarninsa [Allah], waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya. Hakika ba su yin laifi, sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji.” (Zabura 119:1-3) Aminci na bukatar neman sanin nufin Jehovah koyaushe da yin tafiya a hanyoyinsa.
7 Yin tafiya cikin aminci na bukatar manne wa Allah, har ma a yanayi marar daɗi. Sa’ad da muka jimre wa jarrabobi, muka kasance da ƙarfi duk da wahala, ko muka tsayayya wa jarraba daga duniya marar ibada, amincin mu zai bayyana. Za mu sa Jehovah ‘ya yi farin ciki’ domin zai iya amsa sūkar da wani ke yi masa. (Karin Magana 27:11) Da kyakkyawan dalili kuwa, muna iya yanke shawara kamar yadda Ayuba ya yi: “Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.” (Ayuba 27:5) Zabura ta 26 ta nuna mana abin da zai taimaka mana mu yi tafiya cikin aminci.
“Ka Gwada Muradina da Tunanina”
8. Menene ka koya daga roƙon da Dauda ya yi cewa Jehovah ya auna tunaninsa da muradinsa?
8 Dauda ya yi addu’a: “Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, ka gwada muradina da tunanina.” (Zabura 26:2) Zuciya ta alama ita ce mutum na ciki—motsawarsa, motsin zuciyarsa, da basirarsa. Sa’ad da Dauda ya tambayi Jehovah ya auna shi, yana addu’a ne ya duba tunaninsa mai zurfi da motsin zuciyarsa.
9. A wace hanya ce Jehovah yake auna tunaninmu da muradinmu?
9 Dauda ya yi roƙo cewa a auna muradinsa da tunaninsa. Ta yaya ne Jehovah yake auna mutum na mu na ciki? Dauda ya rera waƙa: “Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni, da dare kuma lamirina yana yi mini faɗaka.” (Zabura 16:7) Menene wannan ke nufi? Hakan na nufin cewa gargaɗi na Allah ya shiga wuri mai zurfi a zuciyar Dauda kuma ya kwanta a wajen, wanda ke daidaita zurfafan tunaninsa da motsin zuciya. Mu ma za mu yi haka idan muka yi tunani da godiya bisa gargaɗin da muke samu daga Kalmar Allah, daga wakilansa, da ƙungiyarsa kuma muka bari su kwanta a zuciyarmu. Yin addu’a ga Jehovah a kowane lokaci ya auna mu zai taimake mu mu yi tafiya cikin aminci.
“Madawwamiyar Ƙaunarka Tana bi da Ni”
10. Menene ya taimaka wa Dauda ya yi tafiya a gaskiyar Allah?
10 Dauda ya ci gaba, “Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni, amincinka ke yi mini jagora kullayaumin.” (Zabura 26:3) Dauda ya san ayyukan madawwamiyar ƙauna da Allah ya yi, kuma cikin godiya ya yi bimbini a kansu. Ya rera, “Ka yabi Ubangiji, ya raina,” “kada ka manta da yawan alherinsa.” Sa’ad da ya tuna da ɗaya daga cikin “alherin” Allah, sai Dauda ya ci gaba: “Ubangiji yakan yi wa waɗanda ake zalunta shari’a ta gaskiya. Yakan ba su hakkinsu. Ya faɗa wa Musa shirye-shiryensa. Ya yardar wa jama’ar Isra’ila su ga manyan ayyukansa.” (Zabura 103:2, 6, 7) Wataƙila Dauda yana tunani ne game da yadda Masarawa suka zalunci Isra’ilawa a lokacin Musa. Idan haka ne, yin tunani a kan yadda Jehovah ya sanar da Musa hanyoyinsa na ceto, ya motsa zuciyar Dauda kuma ya ƙarfafa ƙudurinsa na yin tafiya a cikin gaskiyar Allah.
11. Menene zai taimaka mana mu yi tafiya cikin aminci?
11 Nazarin Kalmar Allah a kowane lokaci da kuma yin bimbini a kan abin da muka koya daga Kalmar zai taimaka mana mu yi tafiya cikin aminci. Alal misali, tuna cewa Yusufu ya gudu sa’ad da matar Fotifar ta so ya yi lalata da ita zai ƙarfafa mu mu gudu daga irin wannan yaudarar a wajen aikinmu, a makaranta, ko a wasu wurare. (Farawa 39:7-12) To, yaya idan aka jarrabe mu da zarafin samun arziki, zama shahararre ko kuma samun iko a wannan duniyar fa? Muna da misalin Musa da ya ƙi ɗaukaka a Masar. (Ibraniyawa 11:24-26) Tunawa da yadda Ayuba ya jure, babu shakka, zai taimaka mana mu ƙarfafa ƙudurinmu na kasancewa amintattu ga Jehovah duk da rashin lafiya da masifu. (Yakubu 5:11) Idan muka fuskanci tsanantawa fa? Tuna abin da ya sami Daniyel a ramin zakoki zai ƙarfafa mu!—Daniyel 6:16-22.
“Ba na Tarayya da Mutanen Banza”
12, 13. Wane irin tarayya ne ya kamata mu kauce wa?
12 Sa’ad da yake nuni ga wani abin da ya ƙara ƙarfafa amincinsa, Dauda ya ce: “Ba na tarayya da mutanen banza, ba abin da ya gama ni da masu riya. Ina ƙin tarayya da masu mugunta, na kan kauce wa mugaye.” (Zabura 26:4, 5) Dauda ba ya zama tare da mugaye. Ya ƙi tarayya da masu mugunta.
13 Mu kuma fa? Muna ƙin tarayya da mutanen banza ta wurin wasannin telibijin, bidiyo, majigi, dandalin Intane, ko ta wasu hanyoyi? Muna kauce wa masu riya kuwa? Wasu a makaranta ko wajen aikinmu suna iya ɓoye halayensu don su ƙulla abota da mu su cuce mu. Muna son mu shaƙu da waɗanda ba sa tafiya a gaskiyar Allah? Ko da yake suna iya nuna cewa su sahihai ne, ’yan ridda suna iya ɓoye muradinsu don su janye mu daga bauta wa Jehovah. Idan kuma akwai waɗanda suke rayuwa iri biyu a cikin ikilisiyar Kirista kuma fa? Su ma suna ɓoye halayensu. Jayson, wanda yanzu bawa mai hidima ne, yana da irin waɗannan abokan sa’ad da yake matashi. Ya ce game da su: “Wata rana ɗaya daga cikinsu ya ce mini: ‘Duk abubuwan da muka yi yanzu, ba abin damuwa ba ne, domin sa’ad da sabuwar duniya ta zo, za mu zama matattu ne kawai. Ba za mu san cewa mun yi asarar kome ba.’ Irin wannan maganar ta sa na farka. Ba na son in mutu sa’ad da sabuwar duniya za ta kasance.” Jayson ya yanke tarayyarsa da irin waɗannan abokai. Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “Kada fa a yaudare ku! Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.” (1 Korantiyawa 15:33) Abu ne mai muhimmanci mu ƙi tarayya da mugaye!
‘Zan Faɗi Dukan Ayyukanka Masu Banmamaki’
14, 15. Ta yaya za mu iya “kewaya bagaden” Jehovah?
14 Dauda ya ci gaba:“Ya Ubangiji, na wanke hannuwana don in nuna ba ni da laifi, da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.” Me ya sa? “Na raira waƙar godiya, na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.” (Zabura 26:6, 7) Dauda yana son ya kasance mai tsabtaccen ɗabi’a domin ya bauta wa Jehovah ya kuma sanar da ibadarsa ga Allah.
15 Duka abubuwa game da ibada ta gaskiya a mazauni da kuma haikali “makamantan abubuwan sama da kuma ishararsu” ce. (Ibraniyawa 8:5; 9:23) Bagadi na nuna nufin Jehovah na karɓan hadayar Yesu Kristi domin fansar mutane. (Ibraniyawa 10:5-10) Mun wanke hannuwanmu don mu nuna cewa ba mu da laifi kuma mun “kewaya bagaden” Jehovah ta ba da gaskiya a wannan hadayar.—Yahaya 3:16-18.
16. Ta yaya ne sanar da mutane game da ayyuka masu ban al’ajabi na Allah za ta taimaka mana?
16 Sa’ad da muka yi tunani a kan abubuwan da wannan fansa ta yi, zuciyar mu ba ta cika da godiya ga Jehovah da kuma Ɗansa makaɗaici ba? Tare da godiya daga zuciyarmu, bari mu sanar da mutane ayyuka masu ban al’ajabi na Allah—tun daga halittar mutum a lambun Aidan zuwa dukan abubuwan da za a maido sabuwar duniya ta Allah. (Farawa 2:7; Ayyukan Manzanni 3:21) Kuma yin wa’azi na Mulki da almajirtarwa—kāriya ce ta ruhaniya! (Matiyu 24:14; 28:19, 20) Shagala cikinta za ta taimaka mana mu riƙe begen mu na gaba mai kyau, bangaskiyarmu a alkawuran Allah za ta ƙarfafa, kuma ƙaunarmu wa Jehovah da mutane za ta kasance a raye.
“Ina Ƙaunar Haikali Inda Zatinka Yake”
17, 18. Yaya ya kamata mu ɗauki taro na Kirista?
17 Mazauni tare da bagade na yin hadaya, sune cibiyar bauta wa Jehovah a Isra’ila. Sa’ad da yake furta marmarinsa ga wannan wurin, Dauda ya yi addu’a: “Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake, inda ɗaukakarka ke zaune.”—Zabura 26:8.
18 Muna ƙaunar haɗuwa a wuraren da muke koyo game da Jehovah? Kowace Majami’ar Mulki da tsarin koyarwarta na ruhaniya a kai a kai, cibiya ce ta ibada ta gaskiya a yanki. Ƙari ga haka, muna da taro na gunduma kowace shekara, taron da’ira, da ranar taro na musamman. Ana tattauna “ka’idodin” Jehovah a irin waɗannan tarurruka. Idan muka ‘ƙaunace su da zuciya ɗaya,’ za mu yi ɗokin halartan waɗannan tarurruka kuma za mu kasa kunne sa’ad da muke wurin. (Zabura 119:167) Abu ne mai wartsakarwa mu kasance tare da ’yan’uwanmu masu bi da suka damu da lafiyarmu kuma suke taimaka mana mu ci gaba da yin tafiya cikin adalci!—Ibraniyawa 10:24, 25.
“Kada Ka Hallaka Ni”
19. Waɗanne irin zunubai ne Dauda ba ya son a same shi da su?
19 Da yake ya sani sarai sakamakon bijire wa yin tafiya cikin gaskiyar Allah, Dauda ya yi roƙo: “Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi, ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai, mutanen da ke aikata mugunta a dukan lokaci, a koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.” (Zabura 26:9, 10) Dauda ba ya son a lissafa shi tare da marasa ibada masu mugunta ko masu karɓan rashawa.
20, 21. Menene zai iya kai mu hanyar waɗanda ba sa ƙaunar Allah?
20 A yau ayyukan lalata sun zama ruwan dare gama duniya. Telibijin, jaridu, da siliman, suna ƙarfafa ƙazaman halaye—“wato fasikanci, da aikin lalata, da fajirci.” (Galatiyawa 5:19) Wasu sun zama bayi ga hotunan batsa, waɗanda ke kai su ga aikata lalata. Matasa musamman sukan faɗa wa rinjaya ta lalata cikin sauƙi. A wasu ƙasashe, fita zance al’adarsu ce, kuma ana sa matasa su yi tunani cewa dole sai sun fita zance. Matasa da yawa suna soma soyayya tun ba su isa yin aure ba. Domin su biya bukatarsu ta sha’awar jima’i da ke tasowa, ba da daɗewa ba sai su faɗa cikin halin lalata ko kuma fasikanci.
21 Manya ma suna iya yin rashin aminci. Sha’anin kasuwanci marar gaskiya da tsai da shawara na son kai alama ne na rashin aminci. Yin tafiya cikin tafarkin duniya za ta nisanta mu ne kawai da Jehovah. Bari mu “ƙi mugunta, [mu] ƙaunaci nagarta” mu kuma ci gaba da yin tafiya cikin aminci.—Amos 5:15.
“Ka yi Mini Jinkai Ka Fanshe Ni”
22-24. (a) Wane ƙarfafa ka samu a kalamai na ƙarshe na Zabura 26? (b) Wane mugun tarko ne za a tattauna a talifinmu na gaba?
22 Dauda ya kammala furcinsa ga Allah, yana cewa: “Amma ni, ina yin abin da ke daidai [da aminci], ka yi mini jinƙai ka fanshe ni! Na kuɓuta daga dukan hatsarori, a taron sujada na yabi Ubangiji!” (Zabura 26:11, 12) Ƙudurin Dauda na riƙe amincinsa na da nasaba ta kusa da roƙonsa na ceto. Wannan abin ƙarfafa ne! Duk da yanayinmu na zunubi, Jehovah zai taimaka mana idan muka ƙudurta yin tafiya cikin aminci.
23 Bari hanyar rayuwarmu ta nuna cewa muna daraja kuma muna godiya ga ikon mallakar Allah a dukan fannonin rayuwarmu. Dukanmu muna iya roƙon Jehovah a cikin addu’a cewa ya auna kuma ya daidaita zurfafan tunani da motsin zuciyarmu. Muna iya tunani a kan gaskiyarsa ta yin nazarin Kalmar Allah sosai. Ta kowace hanya, bari mu kauce wa mugun tarayya amma mu yabi Jehovah a cikin taro na sujada. Bari mu ci gaba da yin aikin wa’azi na Mulki da kuma almajirantarwa, kada mu yarda duniya ta lalata dangantakarmu mai tamani da Allah. Sa’ad da muke iyaka ƙoƙarinmu na yin tafiya cikin aminci, muna da tabbacin cewa Jehovah zai yi mana tagomashi.
24 Tun da yake aminci ya ƙunshi duka fasaloli na rayuwa, muna bukatan mu mai da hankali da wani tarko mai kisa—yin maye. Za a tattauna wannan a talifi na gaba.
Ka Tuna?
• Me ya sa za a iya yi wa halittu masu basira shari’a bisa ga amincinsu?
• Menene aminci, kuma menene yin tafiya cikinsa ya ƙunsa?
• Menene zai taimaka mana mu ci gaba da yin tafiya cikin aminci?
• Domin mu riƙe amincinmu, waɗanne haɗarurruka ne za mu kauce wa?