Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 7/1 pp. 8-13
  • Ka Bi Ja-gorar Allah Rayayye

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bi Ja-gorar Allah Rayayye
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yin Amfani da Jini a Matsayin Magani
  • Matsayin Lamirinka
  • Ra’ayin Allah Game da Jini
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Abubuwan da Suka Zama Jini da Kuma Hanyoyin Fida
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Rai Yana da Muhimmanci a Gare Ka Kamar Yadda Yake ga Allah?
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Kana Daraja Rai Yadda Allah Yake Yi Kuwa?
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 7/1 pp. 8-13

Ka Bi Ja-gorar Allah Rayayye

“Ku juyo ga Allah rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da ke cikinsu.”—AYYUKAN MANZANNI 14:15.

1, 2. Me ya sa ya dace mu sani cewa Jehovah “Allah mai rai ne”?

BAYAN manzo Bulus da Barnaba sun warkar da wani mutum, Bulus ya tabbatar wa masu kallo a Listira: “Mu ma ’yan adam ne kamar ku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da ke cikinsu.”—Ayyukan Manzanni 14:15.

2 Hakika, Jehovah ba gunki ba ne marar rai, amma “Allah mai rai ne”! (Irmiya 10:10; 1 Tasalonikawa 1:9, 10) Ban da cewa mai rai ne, Jehovah shi ne Maɓulɓular ranmu. “Shi kansa ne ke ba dukkan mutane rai, da numfashi, da dukkan abubuwa.” (Ayyukan Manzanni 17:25) Yana son mu ji daɗin rayuwa, a yanzu da kuma nan gaba. Bulus ya ƙara cewa Allah “bai taɓa barin kansa ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci yana kuma faranta muku rai.”—Ayyukan Manzanni 14:17.

3. Me ya sa ya kamata mu amince da ja-gorar da Allah yake bayarwa?

3 Yadda Allah yake son ranmu ya ba mu dalilin da zai sa mu dogara ga ja-gorarsa. (Zabura 147:8; Matiyu 5:45) Wasu suna iya ƙin ja-gorancinsa idan suka ga wata doka a cikin Littafi Mai Tsarki wadda ba su gane ta ba ko wadda take kamar tana matsa musu. Duk da haka, hikima ce a amince da ja-gorar Jehovah. Alal misali: A ce Ba’isra’ile bai fahimci dokar da ta hana a taɓa gawa ba, zai amfana idan ya bi dokar. Da farko, biyayya za ta jawo shi kusa da Allah mai rai; na biyu, za ta taimake shi ya kauce wa cuta.—Littafin Firistoci 5:2; 11:24.

4, 5. (a) Kafin lokacin Kiristanci, wace ja-gora Jehovah ya bayar game da jini? (b) Ta yaya ne muka sani cewa ja-gorar Allah game da jini ta shafi Kiristoci?

4 Yana kama da ja-gorar da Allah ya bayar game da jini. Ya gaya wa Nuhu cewa kada mutane su yi amfani da jini. Bayan haka, Allah ya nuna a cikin Doka cewa za a iya yin amfani da jini a kan bagade kaɗai—domin gafarar zunubi. Ta wurin waɗannan ja-gorar, Allah yana shirin yin amfani da jini sosai—wato domin ceton rayuka ta wurin fansar Yesu. (Ibraniyawa 9:14) Hakika, ja-gorar Allah ya nuna cewa yana damuwa da ranmu da kuma lafiyarmu. Sa’ad da yake tattauna Farawa 9:4, wani manazarcin Littafi Mai Tsarki na ƙarni na 19 Adam Clarke ya rubuta: “Wannan doka [da aka ba Nuhu] har yanzu Kiristoci na Gabas suna bin ta sosai . . . Babu jinin da ake ci a ƙarƙashin doka, domin yana nuni ne da jinin da za a zubar domin zunubin duniya; kuma a ƙarƙashin bishara ba a yarda a ci jini ba, domin za a ci gaba da ɗaukan shi a matsayin jinin da ake zubarwa domin gafarar zunubai.”

5 Wataƙila wannan masanin yana nuni ne da bishara game da Yesu. Wannan ya haɗa da yadda Allah ya aiko mana da Ɗansa ya mutu dominmu, ya zubar da jininsa domin mu sami rai madawwami. (Matiyu 20:28; Yahaya 3:16; Romawa 5:8, 9) Kuma kalamin wannan masani ya yi nuni da wata doka da ta ce mabiyan Kristi su ƙi jini.

6. Wace ja-gora ce aka ba Kiristoci game da jini, kuma me ya sa?

6 Ka sani cewa Allah ya ba Isra’ilawa ɗarurruwan farillai. Bayan mutuwar Yesu, almajiransa ba sa bukatar su bi duka waɗannan dokoki. (Romawa 7:4, 6; Kolosiyawa 2:13, 14, 17; Ibraniyawa 8:6, 13) Amma dai, bayan wani lokaci wata matsala ta taso game da wani abu da yake wajibi—yin kaciya. Ya kamata waɗanda ba Yahudawa ba da suke son su amfana daga jinin Kristi su yi kaciya, da za ta nuna cewa suna ƙarƙashin Doka? A shekara ta 49 A.Z., hukumar mulki ta Kiristoci sun tattauna wannan mahawwara. (Ayyukan Manzanni, sura 15) Da taimakon ruhun Allah, manzanni da dattawa sun warware wannan mahawara da suka ce Doka ta kawo ƙarshen wannan wajibi na yin kaciya. Duk da haka, akwai wasu hurarren farillai da ke nan da Kiristoci suke bi. A cikin wata wasiƙa zuwa ga ikilisiyoyi, hukumar mulki ta rubuta: “Ruhu Mai Tsarki ya ga ya kyautu, mu ma mun gani, kada a ɗora muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwa da ke wajibi, wato ku guji abin da aka yanka wa gunki, da cin nama tare da jini, da cin abin da aka maƙure, da kuma fasikanci. In kun tsare kanku daga waɗannan, za ku zauna lafiya.”—Ayyukan Manzanni 15:28, 29.

7. Me ya sa yake da muhimmanci ‘Kiristoci su ƙi jini’?

7 A bayyane kuwa, hukumar mulki ta ɗauki ƙin jini daidai da ƙin lalatar jima’i ko kuwa bautar gunki. Wannan ya nuna cewa wannan hani game da jini yana da tsanani. Kirista wanda ya bauta wa gunki ko kuwa ya yi lalatar jima’i kuma ya ƙi ya tuba ba zai “sami gado a cikin Mulkin Allah” ba; “rabonsu . . . shi ne mutuwa ta biyu.” (1 Korantiyawa 6:9, 10; Wahayin Yahaya 21:8; 22:15) Ka lura da bambancin: Rena ja-gorar Allah game da tsarkakar jini tana iya jawo mutuwa ta har abada. Daraja hadayar Yesu tana iya kai ga rai madawwami.

8. Menene ya nuna cewa Kiristoci na farko sun ɗauki ja-gorar Allah game da jini da muhimmanci?

8 Ta yaya ne Kiristoci na farko suka fahimci kuma suka bi ja-gorar Allah game da jini? Ka tuna da maganar Clarke: “A ƙarƙashin bishara ba a yarda a ci jini ba, domin za a ci gaba da ɗaukan shi a matsayin jinin da aka zubar domin gafarar zunubai.” Tarihi ya nuna cewa Kiristoci na farko sun ɗauki batun da muhimmanci. Tertullian ya rubuta: “Ka yi la’akari da waɗanda suke haɗama, a wani wasa, suka ɗebi jinin mugaye masu laifi . . . suka tafi da shi domin su warkar da farfaɗiyarsu.” Ko da yake arna suna cin jini, Tertullian ya ce “ko jinin dabba ma ba shi cikin abincin [Kiristoci] . . . A lokacin gwaji idan ka ba Kirista nama da aka dafa da jini. Ka sani cewa haramu ne a gare su.” Hakika, duk da burgar mutuwa, Kiristoci ba za su ci jini ba. Ja-gorar Allah tana da muhimmanci sosai a gare su.

9. Ban da cin jini menene ƙin jini ya ƙunsa?

9 Wasu suna iya zaton cewa hukumar mulki ba ta nufin cewa kada Kiristoci su ci ko su sha jini kai tsaye ba, ko cin nama da ba a yanka ba, ko kuwa abinci da aka haɗa da jini ba. Hakika, wannan ita ce ma’anar dokar da Allah ya ba Nuhu. Kuma dokar manzanni ta gaya wa Kiristoci ‘su ƙi abin da aka maƙure,’ naman da ba a yanka ba. (Farawa 9:3, 4; Ayyukan Manzanni 21:25) Amma, Kiristoci na farko sun san cewa wannan tana da wata manufa. A wasu lokaci an sha jini domin magani. Tertullian ya lura cewa a ƙoƙarin warkar da farfaɗiya, wasu arna sun sha jini. Kuma wataƙila an yi amfani da jini don a warkar da cuta ko kuwa don kyautata lafiya. Saboda haka, ƙin yin amfani da jini da aka ce Kiristoci su yi ya haɗa da ƙin amfani da shi a matsayin “magani.” Suna riƙe wannan mataki ko idan hakan zai sa rayuwarsu cikin matsala.

Yin Amfani da Jini a Matsayin Magani

10. A waɗanne hanyoyi ne ake amfani da jini a matsayin magani, kuma wannan ya ta da wace tambaya?

10 Yin amfani da jini a matsayin magani a yau ya zama ruwan dare. Ƙarin jini na dā ilahirinsa ne—wanda aka cire daga jikin wani, a ajiye, kuma a ƙara wa marar lafiya, wataƙila wanda aka ji masa rauni a wajen yaƙi. A kwana a tashi, masu bincike suka koyi yadda ake rarraba jini zuwa ainihin abubuwan da ke ƙunsa cikin jini. Ta yin amfani da abubuwan da aka samo daga cikin jini wajen ƙarin jini, likitoci suna iya raba jinin da ake ba majiyyata, ƙila ruwan jini ga wanda ya ji rauni, jajayen ƙwayoyin jini kuma ga wani. Ƙarin bincike ya nuna cewa abubuwan da aka samo daga cikin jini, kamar ruwan jini, ana iya sarrafa shi don a cire wasu gutsurori, da za a iya ba wa wasu majiyyata. Ƙoƙarin cire wasu gutsurori da aka samo daga cikin jini yana ci gaba, kuma ana samun rahoto cewa an fara amfani da sababbin gutsurorin. Menene Kirista zai yi game da wannan? Ya riga ya yanke shawarar cewa ba zai taɓa amsar ƙarin jini ba, amma likitansa ya ce ya karɓi ɗaya daga cikin gutsurori da aka samo daga cikin jini, wataƙila jajayen ruwan jini. Ko kuwa yana iya kasance cewa maganin yana ɗauke da ƙananan gutsuri da aka ciro daga cikin ainihin abubuwan da aka samo daga cikin jini. Ta yaya ne bawan Allah zai iya yanke shawara game da waɗannan tambayoyi, da sanin cewa jini yana da tsarki kuma a azanci mai girma, jinin Yesu yana ceton rai?

11. Wane amintaccen matsayi ne Shaidu suke da shi da daɗewa game da jini?

11 Shekaru da yawa da suka wuce Shaidun Jehovah sun bayyana matsayinsu. Alal misali, sun rubuta a wani talifi wanda aka buga a cikin The Journal of the American Medical Association (27 ga Nuwamba, 1981; an sake buga shi a cikin How Can Blood Save Your Life?,a shafi na 27–29). Wannan talifin ya yi ƙauli daga Farawa, Littafin Firistoci, da kuma Ayyukan Manzanni. Ya ce: “Ko da yake waɗannan ayoyi ba a faɗe su ba a harshen magunguna, Shaidu sun ɗauki ayoyin a matsayin sun hana ƙarin jini, ilahirin jini, jajayen ƙwayoyin jini, da ruwan jini, da ƙwayoyin rai na farin jini da kuma kamewar jini.” Littafin shekara ta 2001 na Emergency Care [Taimako na Gaggawa] a ƙarƙashin “Composition of the Blood,” ya ce: “Jini ya ƙunshi abubuwa da yawa: ruwan jini, jajaye da fararen ƙwayoyin jini da kuma kamewar jini.” Domin abubuwan da masu magani suka faɗa, Shaidu sun ƙi ƙarin jini na ilahirin jini ko kuwa na sauran abubuwan da aka samo daga cikin jini iri huɗu.

12. (a) Wane matsayi ne aka gabatar game da gutsurori da aka cire daga abubuwan da aka samo daga cikin jini? (b) A ina ne za a iya samun ƙarin bayani game da wannan?

12 Wannan talifi na magani ya ci gaba: “Addinin Shaidun bai fito sarai sarai ya hana yin amfani da [gutsuri] ba irin su wani furotin da ake samu a cikin jini, furotin mai garkuwa, da kuma abubuwan da ke tsare zuban jini ba; kowane Mashaidi zai yanke shawara da kansa idan zai karɓi waɗannan.” Tun shekara ta 1981, an daina yin amfani da ɗaya cikin gutsurori masu yawa (na ainihin abubuwa huɗu da aka samo daga cikin jini). Domin haka, Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 2004, ta ba da taimako a kan wannan batu a cikin talifin nan “Tambayoyi Daga Masu Karatu.” Wannan ya ba da daki-daki da kuma bayani game da batun, duk da haka za ka ga cewa abin da ya ce ya yi daidai da muhimman ra’ayoyi da aka bayyana a shekara ta 1981.

Matsayin Lamirinka

13, 14. (a) Menene lamiri, kuma ta yaya ya shafi batun jini? (b) Wace ja-gora Allah ya ba Isra’ilawa game da cin nama, amma waɗanne tambayoyi ne suka taso?

13 Irin waɗannan bayani suna bukatar yin amfani da lamiri sa’ad da za a tsai da shawara. Me ya sa? Kiristoci sun amince da bukatar su bi ja-gorar Allah, duk da haka a wasu yanayi mutum zai yi amfani da lamirinsa sa’ad da yake son ya tsai da shawara. Lamiri shi ne iya gwada wani abu da kuma tsai da shawara, wanda ya shafi batu na ɗabi’a. (Romawa 2:14, 15) Amma dai, ka sani cewa, lamiri sun bambanta.b Littafi Mai Tsarki ya ce wasu suna da ‘rarraunan lamiri,’ wannan ya nuna cewa wasu suna da lamiri mai ƙarfi. (1 Korantiyawa 8:12) Kiristoci sun bambanta a yadda suka sami ci gaba wajen sanin abubuwan da Allah ya faɗi, sun kuma san tunaninsa kuma suna amfani da wannan sa’ad da suke tsai da shawara. Muna iya misalta wannan da Yahudawa da kuma cin nama.

14 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutumin da yake biyayya ga Allah ba zai ci naman da ba a yanka ba. Wannan yana da muhimmanci sosai har ma a lokacin gaggawa sa’ad da sojojin Isra’ila suka ci naman da ba a yanka ba, sun yi zunubi mai tsanani. (Maimaitawar Shari’a 12:15, 16; 1 Sama’ila 14:31–35) Duk da haka, ƙila tambaya ta taso. Sa’ad da Ba’isra’ile ya kashe tunkiya, ta yaya ne zai zubar da jinin da wuri? Ya dace ya yanke maƙogwaron dabbar domin ya zubar da jinin? Ana bukatar a rataye tunkiyar ta ƙafafun baya ne? Har yaushe? Ta yaya ne zai zubar da jinin babban saniya? Bayan ya zubar da jinin, jinin na iya ragewa a cikin naman. Zai iya cin irin wannan naman kuwa? Wa zai tsai da shawarar?

15. Menene wasu Yahudawa suka yi game da cin nama, amma wane ja-gora ne Allah ya bayar?

15 A ce wani Bayahude mai ƙwazo yana fuskantar irin wannan tambayar. Yana iya tunanin cewa zai dace ya ƙi naman da ake sayarwa a kasuwa, yadda wani kuma zai ƙi cin naman da aka yi wa gunki hadayarsa. Wasu Yahudawan suna iya cin nama bayan sun bi al’ada domin su cire jinin.c (Matiyu 23:23, 24) Menene ka ce game da irin waɗannan halaye da suka bambanta? Bugu da ƙari, tun da Allah bai bukaci irin waɗannan ayyuka ba, ya dace Yahudawa su aika tambayoyi masu yawa ga majalisar malamai domin su sami shawara game da kowace tambaya? Ko da yake irin wannan al’ada ta taso ne cikin addinin Yahudawa, muna farin ciki cewa Jehovah ba ya ja-gorar masu ibada ta gaskiya su bi irin wannan shawarar ba game da jini. Allah ya ba da muhimmiyar ja-gora game da yanka dabbobi masu tsabta da kuma zubar da jininsu, amma bai ba da wani ƙarin bayani fiye da haka ba.—Yahaya 8:32.

16. Me ya sa Kiristoci suke da ra’ayi da ya bambanta game da amsar allura na ƙananan gutsuri na abubuwan da aka samo cikin jini?

16 Yadda aka ambata a sakin layi na 11 da na 12, Shaidun Jehovah ba sa amsar ƙarin jini na ilahirin jini ko na abubuwan da aka samo daga cikin jini iri huɗu—ruwan jini, jajayen ƙwayoyin jini, ƙwayoyin rai na farin jini, da kuma kamewar jini. Gutsurori da aka cire daga cikin ainihin ƙananan abubuwa da jini ya ƙunsa kuma fa, kamar jini mai ruwan ɗorawa wanda zai iya yaƙi cuta ko kuwa ya yaƙi dafin maciji? Wasu sun yanke shawarar cewa irin waɗannan gutsurin a yanzu ba jini ba ne kuma saboda haka ba sa ƙarƙashin doka da ta ce ‘a ƙi jini’ ba. (Ayyukan Manzanni 15:29; 21:25) Wannan hakkinsu ne. Lamirin wasu yana sa su ƙi ko dukan abin da aka samo daga jinin (dabba ko na mutum), ko ɗan gutsuri guda ɗaya ne cikin abubuwan da aka samo daga cikin jini.d Duk da haka wasu suna iya karɓan allura na furotin ɗin ruwan jini domin yaƙe cuta ko dafin maciji kuma suna iya ƙin sauran ƙananan ainihin abubuwan da aka samo daga cikin jini. Bugu da ƙari, wasu kayayyaki da ake samu daga cikin ainihin abubuwa huɗu da jini ya ƙunsa na iya zama daidai da ilahirin jini kuma yana iya ɗaukan matsayin kiyaye rai a cikin jiki wanda zai zama abin tuhuma ga yawancin Kirista.

17. (a) Ta yaya ne lamirinmu zai iya zama kāriya sa’ad da muke fuskantar tambayoyi game da gutsurin abubuwan da aka samo daga cikin jini? (b) Me ya sa yin shawara game da wannan batu yake da muhimmanci sosai?

17 Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da lamiri yana taimakawa sa’ad da muke yanke irin wannan shawarar. Mataki na farko shi ne koyon abin da Kalmar Allah ta ce kuma ka yi ƙoƙari ka gyara lamirinka da ita. Wannan zai taimake ka ka yanke shawara cikin jituwa da ja-gorancin Allah maimakon ka tambayi wani ya tsai da maka shawara. (Zabura 25:4, 5) Game da karɓan gutsurin abubuwan da aka samo daga cikin jini, wasu suna tunani cewa, ‘Wannan batu ne na lamiri, saboda haka, bai da muhimmanci.’ Wannan tunanin bai yi daidai ba. Gaskiyar cewa wannan bayani na lamiri ne ba ya nufin cewa ba shi da muhimmanci. Shawararmu na iya zama mai tsanani. Dalili na farko shi ne yana iya shafar wasu da lamirinsu ya bambanta da namu. Muna iya tunanin haka daga shawarar da Bulus ya ba da game da nama da wataƙila an yi wa gunki hadaya da shi kuma bayan haka an zo an sayar da shi a kasuwa. Ya kamata Kirista ya lura kada ya ‘rushe rarraunan lamirin.’ Idan ya sa wasu tuntuɓe, yana iya ‘rushe ɗan’uwansa wanda Almasihu ya mutu dominsa’ kuma ya yi zunubi ga Kristi. Saboda haka, ko da yake batun da gutsurin abubuwan da aka samo daga cikin jini tana bukatar ka tsai da shawararka ne, ya kamata a ɗauki shawarar da muhimmanci.—1 Korantiyawa 8:8, 11–13; 10:25–31.

18. Ta yaya ne Kirista zai kauce wa ƙyale lamirinsa sa’ad da yake tsai da shawara game da jini?

18 Wani darasi da za mu bincika ya nanata muhimmancin shawara game da jini. Haka ne wannan shawarar zai iya shafan ka. Idan yin amfani da ɗan gutsurin abubuwan da aka samo daga cikin jini zai dami lamirinka da aka koyar da Littafi Mai Tsarki, kada ka ƙi lamirinka. Kuma kada ka ƙi abin da lamirinka ya gaya maka domin wani ya gaya maka cewa, “yana da kyau ka karɓi gutsurin abubuwan da aka samo daga cikin jini; mutane da yawa sun karɓa.” Ka tuna cewa, miliyoyin mutane a yau suna banza da lamirinsu, kuma ya zama matacce, wannan ya sa suna yin ƙarya ko wasu abubuwa marasa kyau ba sa damuwa. Kiristoci ba sa son su zama haka.—2 Sama’ila 24:10; 1 Timoti 4:1, 2.

19. Sa’ad da muke tsai da shawara a batun magani da ya ƙunshi jini, menene za mu fi tunawa da shi?

19 Kusan ƙarshensa, amsar da aka buga a fitar Hasumiyar Tsaro na 15 ga Yuni 2004, ta ce: “Gaskiyar cewa ra’ayi da kuma shawarar da ta dace tana iya bambantawa, wannan na nufin cewa batun bai da muhimmanci ne? A’a. Yana da muhimmanci.” Wannan yana da muhimmanci domin ya shafi dangantakarka da “Allah mai rai.” Wannan dangantakar ita ce kaɗai za ta iya sa ka sami rai madawwami, bisa ikon ceto na jinin da Yesu ya zubar. Ka daɗa daraja jini sosai domin abin da Allah yake yi ta wurinsa—ceton rayuka. Bulus ya rubuta daidai da wannan: ‘Marasa sa zuciya, marasa Allah kuma a duniya. Amma yanzu, cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu.’—Afisawa 2:12, 13.

[Hasiya]

a Shaidun Jehovah ne suka buga.

b A wani lokaci, Bulus da wasu Kiristoci guda huɗu, suka tafi haikali domin su tsarkaka kansu. Ko da yake ba a amfani da Dokar kuma, Bulus ya bi shawarar dattawa a Urushalima. (Ayyukan Manzanni 21:23–25) Duk da haka, wasu Kiristoci suna iya jin cewa su ba za su shiga cikin haikali ko kuwa su bi wannan tsarin ba. Lamiri sun bambanta a can dā, kuma sun bambanta a yau.

c Littafin nan Encyclopaedia Judaica ya ba da “cikakken bayani kuma mai sauƙi” game da yadda ake “yanka” nama. Ya kuma faɗi minti nawa nama zai yi a cikin ruwa, yadda za a shanya shi a kan katako, ainihin irin gishirin da za a yayyafa a kan shi, da kuma sau nawa za a wanke shi a cikin ruwan sanyi.

d Yawancin fasali na wasu allurai da suke ƙara ƙarfin ƙwayoyin jini, ba da jini aka yi su ba. Amma a wasu yanayin ana iya ƙara ɗan gutsurin abubuwan da aka samo daga cikin jini, kamar wani irin furotin da ake samu a cikin jini.—Duba “Tambayoyi Daga Masu Karatu” a cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Oktoba, 1994 na Turanci.

Za Ka Iya Tunawa?

• Wane ja-gora ce game da jini Allah ya ba wa Nuhu, Isra’ilawa, da kuma Kiristoci?

• Game da jini, menene Shaidun Jehovah suka ƙi?

• A wane azanci ne karɓan ɗan gutsuri na ainihin abubuwan da aka samo daga cikin jini ya zama batun lamiri, amma menene hakan ba ya nufi?

• Sa’ad da muke tsai da shawara, me ya sa ya kamata mu sa dangantakarmu da Allah ta zama aba ta farko a zuciyarmu?

[Taswira a shafi na 11]

MATSAYI NA MUSAMMAN GAME DA JINI

ILAHIRIN JINI

▾ ▾ ▾ ▾

WAƊANDA BA Jajayen Ƙwayoyin rai Kamewar Ruwan

A KARƁA ƙwayoyi na farin jini jini jini

▾ ▾ ▾ ▾

KIRISTA ZAI TSAI DA SHAWARARSA

Gutsurori daga jajayen ƙwayoyi

Gutsurori daga fararen ƙwayoyi

Gutsurori daga kamewar jini

Gutsurori daga ruwan jini

[Hoto a shafi na 9]

Hukumar mulki ta yanke shawarar cewa Kiristoci su ‘ƙi jini’

[Hoto a shafi na 12]

Kada ka yi watsi da lamirinka sa’ad da ka fuskanci shawara game da gutsurin abubuwan da aka samo daga cikin jini

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba