Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 7/1 p. 28-p. 31 par. 10
  • Taƙaici Daga Littafin Firistoci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taƙaici Daga Littafin Firistoci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • BA DA KYAUTA —NA SON RAI DA NA WAJIBI
  • (Littafin Firistoci 1:1–7:38)
  • AN KAFA TSARIN FIRISTOCI MAI TSARKI
  • (Littafin Firistoci 8:1–10:20)
  • BAUTAR ALLAH TANA BUKATAR TSABTA
  • (Littafin Firistoci 11:1–15:33)
  • DOLE A KASANCE DA TSARKI
  • (Littafin Firistoci 16:1–27:34)
  • YADDA LITTAFIN FIRISTOCI YA SHAFI BAUTARMU
  • Hadayu Da Suke Faranta Wa Allah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • “Ku Zama da Tsarki”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Me Ya Sa Ya Wajaba Mu Kasance da Tsarki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Littafin Firistoci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 7/1 p. 28-p. 31 par. 10

Maganar Jehovah Rayayyiya Ce

Taƙaici Daga Littafin Firistoci

BAI kai shekara guda ba tun lokacin da aka ’yantar da Isra’ilawa daga bautar Masar. Yanzu da suka zama sabuwar al’umma, suna kan hanyar zuwa ƙasar Kan’ana. Nufin Jehovah ne al’umma mai tsarki ta zauna a wurin. Amma, salon rayuwar Kan’aniyawa da ayyukansu na addini ta ƙazanta ce. Saboda haka, Allah na gaskiya ya ba ikilisiyar Isra’ila ƙa’idodi da zai sa su kasance dabam don hidimarsa. Suna rubuce a Littafin Firistoci na Littafi Mai Tsarki. Annabi Musa ne ya rubuta shi a dajin Sinai, mai yiwuwa a shekara ta 1512 K.Z., littafin game da tarihin Isra’ila ne na wata guda. (Fitowa 40:17; Littafin Ƙidaya 1:1–3) Jehovah ya aririce masu bauta masa a kai a kai su kasance da tsarki.—Littafin Firistoci 11:44; 19:2; 20:7, 26.

Shaidun Jehovah a yau ba sa bin Dokar da Allah ya ba Musa. Mutuwar Yesu Kristi ta kawar da wannan Dokar. (Romawa 6:14; Afisawa 2:11–16) Amma, farillai da ke cikin Littafin Firistoci za su amfane mu, suna koya mana game da bautar Allahnmu, Jehovah.

BA DA KYAUTA —NA SON RAI DA NA WAJIBI

(Littafin Firistoci 1:1–7:38)

Wasu bayabaye da hadayu na Doka na son rai ne, yayin nan kuma wasu na wajibi ne. Alal misali, hadaya ta ƙonawa na son rai ne. Ana miƙa ta gabaki ɗaya ga Allah, yadda Yesu Kristi da son ransa ya ba da ransa hadayar fansa gabaki ɗaya. Ana rarraba hadaya ta salama da ake yi da yardan rai. Ana miƙa wa Allah ɓari ɗaya a kan bagadi, wani ɓari kuma firist ne yake ci, wani kuma mai bayarwan ne yake ci. Haka nan ma, Tuna mutuwar Kristi jibi na tarayya ne ga Kiristoci shafaffu.—1 Korantiyawa 10:16–22.

Hadayu na zunubi da hadayu na laifi wajibi ne. Hadaya ta zunubi kafarar zunubai ne da aka yi cikin kuskure. Hadaya ta biyun tana gamsar da Allah ne idan mai laifin da ya cuci wani ko kuma idan aka mai da wa mai laifin gatar da aka ɗauke masa don horon da aka yi masa—ko kuma idan yanayi biyun ya auku. Ana hadaya ta gari don a nuna godiya ga tanadin Jehovah mai yawa. Dukan waɗannan batutuwa suna da muhimmanci a gare mu domin hadayu waɗanda Dokar alkawari ta ce a yi su suna nuni ga Yesu Kristi da hadayarsa ko kuma fa’idodi da za a samu a ciki.—Ibraniyawa 8:3–6; 9:9–14; 10:5–10.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

2:11, 12—Me ya sa Jehovah bai amince da “hadayar ƙonawa” na zuma ba? Zuma da ake maganarsa a nan ba na ƙudan zuma ba ne. Ko da ba a yarda a yi “hadayar ƙonawa” da shi ba, yana cikin “nunan fari na . . . amfanin gona.” (2 Tarihi 31:5) Wannan zuma babu shakka, ruwan ’ya’yan itace ne ko maɗi. Da yake zai iya tsami, ba a yarda a miƙa shi a kan bagadi ba.

2:13—Me ya sa za a sa gishiri a “kowace hadaya”? Ba domin a kyautata hadayun ba ne. A gewaye da duniya ana amfani da gishiri a tanada abubuwa. Mai yiwuwa ana sa a hadayu domin kada hadayun su lalace ko kuma su yi tsami.

Darussa da Za Mu Koya:

3:17. Tun da yake ana ɗaukan cewa kitsen ne sashe mafi kyau, domin haka ba za a ci ba, ya nuna wa Isra’ilawa muhimmancin cewa za a ba wa Jehovah sashe mafi kyau. (Farawa 45:18) Wannan yana tuna mana cewa ya kamata mu ba Jehovah abu mafi kyau.—Karin Magana 3:9, 10; Kolosiyawa 3:23, 24.

7:26, 27. Isra’ilawa ba za su ci jini ba. A ra’ayin Allah, jini na wakilta rai. Littafin Firistoci 17:11 ya ce “ran nama yana cikin jinin.” Har ila ana bukatar kada masu bauta ta gaskiya a yau su ci jini.—Ayyukan Manzanni 15:28, 29.

AN KAFA TSARIN FIRISTOCI MAI TSARKI

(Littafin Firistoci 8:1–10:20)

Wanene aka ba wa hakkin kula da ayyuka game da hadayu? An danƙa wa firistoci. Yadda Allah ya ba da umurni, Musa ne ya gudanar da bikin naɗa Haruna, babban firist, da kuma ’ya’yansa maza huɗu da za su zama mataimakan firist. An yi bikin na kwanaki bakwai, kuma bayan haka tsarin firistoci ya soma.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

9:9—Menene ma’anar zuba jini a gindin bagadi da kuma zankayen bagaden? Wannan ya nuna cewa Jehovah ya amince a yi kafara da jini. Dukan shirin kafara ya dangana a kan jini. Manzo Bulus ya rubuta: “Bisa ga Shari’a, kusan kowane abu da jini ake tsarkake shi, in ba game da zubar da jini ba kuwa, ba gafara.”—Ibraniyawa 9:22.

10:1, 2—Menene wataƙila ya sa ’ya’yan Haruna maza, Nadab da Abihu suka yi zunubi? Ba da daɗewa ba bayan Nadab da Abihu suka aikata yadda bai dace ba a ayyukansu na firist, Jehovah ya hana firistoci su sha ruwan inabi ko barasa sa’ad da suke hidima a mazauni. (Littafin Firistoci 10:9) Wannan yana nuna cewa mai yiwuwa ne ’ya’yan Haruna maza biyu sun sha giya a yanayin da aka kwatanta a nan. Amma, miƙa “haramtacciyar wuta . . . ba irin wadda [Jehovah] ya umarta ba” ne ainihin dalilin da ya sa suka mutu.

Darussa da Za Mu Koya:

10:1, 2. Bayin Jehovah masu hakki a yau dole ne su yi biyayya da mizanan Allah. Bugu da ƙari, ba za su yi alfahariya ba yayin da suke kula da hakkinsu.

10:9. Sa’ad da muka sha giya ba zai dace ba mu ce za mu cika wani aiki da Allah ya bayar.

BAUTAR ALLAH TANA BUKATAR TSABTA

(Littafin Firistoci 11:1–15:33)

Dokoki na abinci game da dabbobi masu tsabta da marasa tsabta ta amfani Isra’ilawa a hanyoyi biyu. Waɗannan dokoki sun sa kada abubuwa masu lahani su shafe su kuma su kafa mahani tsakaninsu da mutanen al’ummai da ke gewaye da su. Wasu dokoki game da rashin tsabta da ake samu ne daga gawa, tsabtace mata bayan sun haihu, farillai game da kuturta, da rashin tsabta daga maniyyi da ke fitowa daga namiji da tamace a lokacin jima’i. Firistoci ne za su kula da batutuwa game da mutane marasa tsabta.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

12:2, 5—Me ya sa haihuwa yake sa mace ta zama “marar-tsarki”? An yi al’aura ta fito da kamiltaccen rai. Amma, domin sakamakon zunubi da aka gāda, ’ya’yan da aka haifa suna rayuwa ta ajizanci da kuma na zunubi. Ɗan lokaci na ‘rashin tsabta’ da ke tattare da haihuwa, da wasu batutuwa, kamar su jinin ha’ila, da ɗigar maniyyi sun sa Isra’ilawa su tuna da zunubi da aka gada. (Littafin Firistoci 15:16–24; Zabura 51:5; Romawa 5:12) Farillai na tsarkakewa da ake bukata zai taimaki Isra’ilawa su fahimci bukatar hadayar fansa don a yafe zunubin ’yan Adam kuma a mai da ’yan Adam kamiltattu. Da haka Dokar ta zama ‘uwargijiyarsu da ta kai su ga Almasihu.’—Galatiyawa 3:24.

15:16–18—Menene “maniyyi” da aka ambata a waɗannan ayoyi? Wannan yana nufin maziyyi da ke fitowa daga al’aurar namiji daddare ko kuma wanda ke fitowa lokacin jima’i na mata da miji.

Darrusa da Za Mu Koya:

11:45. Jehovah Allah mai tsarki ne kuma yana bukatar waɗanda suke bauta masa su kasance da tsarki. Dole su yi tsarki kuma su kasance da tsabta ta ruhaniya da ta zahiri.—2 Korantiyawa 7:1; 1 Bitrus 1:15, 16.

12:8. Jehovah ya ƙyale matalauta su ba da tsuntsaye domin hadaya maimakon tunkiya da ta fi tsada. Yana la’akari da matalauta.

DOLE A KASANCE DA TSARKI

(Littafin Firistoci 16:1–27:34)

Ana miƙa hadayu mafi muhimmanci don zunubai a Ranar Kafara kowace shekara. Ana miƙa saniya don firistoci da ƙabilar Lawi. Ana ba da hadayar akuya don ƙabilun Isra’ila da ba firistoci ba. Ana ƙorar wata akuya ta shiga jeji bayan an zuba mata zunuban mutanen. Awakai biyun hadayan zunubi ɗaya ne. Dukan waɗannan suna nuna cewa za a yi hadayar Yesu Kristi kuma zai kawar da zunubai.

Sharuɗa game da cin nama da wasu batutuwa sun nanata mana bukatar kasance da tsarki sa’ad da muke bauta wa Jehovah. Ya dace firistoci su kasance da tsarki. Bukukuwa uku da ake yi kowace shekara, lokaci ne na farin ciki sosai da kuma na yi wa Mahalicci godiya. Jehovah ya kuma ba mutanensa farillai game da ɓata sunansa mai tsarki, kiyaye Asabarci da kuma Shekarar ’Yanci, yadda za a bi da matalauta, da yadda za a bi da bayi. Albarka da za a samu daga biyayya ga Allah dabam take da la’ana da za a fuskanta don rashin biyayya. Da akwai sharuɗa game da yin hadayu na wa’adi da na tamani, ’yan fari na dabbobi, da kuma ba da kowane ushirin ‘tsattsarka ga Ubangiji.’

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

16:29—A wace hanya Isra’ilawa za su “ƙasƙantar da kansu”? Ana yin wannan ne bayan Ranar Kafara, yana da nasaba da neman gafara don zunubai. A wannan lokaci suna azumi domin su tuna su masu zunubi ne. Mai yiwuwa “ƙasƙantar da kansu” ɗin game da batun azumi ne.

19:27—Menene ake nufi da umurni kada a ‘yi wa goshi da gemu kwakkwafa’? An ba Yahudawa wannan dokar don kada su kwakkwafa gemunsu ko gashin kansu a yin kwaikwayon wasu ayyukan arna. (Irmiya 9:25, 26; 25:23; 49:32) Amma, umurnin Allah ba ya nufin cewa kada Yahudawa su kwakkwafa gemunsu ko yi gyaran fuskarsu sam sam ba.—2 Sama’ila 19:24.

25:35–37—Daidai ne Isra’ilawa su biɗi riba kowane lokaci? Idan an ranta kuɗin don kasuwanci ne, wanda ya ba da bashin zai iya biɗan riba. Amma, Dokar ta hana biɗan riba a kan rance da aka yi domin a sauƙaƙa talauci. Biɗan riba daga maƙwabci da ya yi hasara ba daidai ba ne.—Fitowa 22:25.

26:19—Ta yaya ‘sama zai zama kamar ƙarfe, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla’? Domin rashin ruwan sama, sararin sama na ƙasar Kan’ana sun yi tauri kamar ƙarfe. Idan babu ruwan sama, duniya za ta yi ƙarfi kamar tagulla.

26:26—Menene ake nufi da ‘mata goma suna dafa abinci a murhu ɗaya’? Yadda ya dace, kowacce mace za ta bukaci murhu dabam don dukan dahuwa da za ta yi. Waɗannan kalmomi suna nuni ga karancin abinci da za a yi har da murhu ɗaya zai isa a dukan dahuwa da mata goma za su yi. Wannan ɗaya ne cikin sakamako da aka annabta na rashin kasance da tsarki.

Darussa da Za Mu Koya:

20:9. Halin ƙiyayya da zalunci daidai ne da kisa a gaban Jehovah. Saboda haka, zagin iyaye da yake daidai da kashe su ma yana da horo iri ɗaya. Bai kamata wannan ya motsa mu mu ƙaunaci ’yan’uwa masu bi ba?—1 Yahaya 3:14, 15.

22:32; 24:10–16, 23. Ba za a zargi sunan Jehovah ba. Akasin haka, dole mu yabi sunansa kuma mu yi addu’a don tsarkake sunan.—Zabura 7:17; Matiyu 6:9.

YADDA LITTAFIN FIRISTOCI YA SHAFI BAUTARMU

Shaidun Jehovah a yau ba sa bin Dokar. (Galatiyawa 3:23–25) Tun da yake abin da aka faɗa a Littafin Firistoci ya shafe bautarmu zai taimake mu mu san ra’ayin Jehovah a kan batutuwa dabam dabam.

Yayin da kake karatun Littafi Mai Tsarki na mako don shirin Makarantar Hidima ta Allah, babu shakka za ka burge da cewa Allah yana bukatar bayinsa su kasance da tsarki. Wannan littafi na Littafi Mai Tsarki zai motsa ka ka ba Maɗaukaki Duka abu mafi kyau, koyaushe ka kasance da tsarki ga yabonsa.

[Hoto a shafi na 28]

Hadayu da aka miƙa a Dokar suna nuni ga Yesu Kristi da hadayarsa

[Hoto a shafi na 29]

Idin Gurasa Marar-Yisti biki ne na farin ciki sosai

[Hoto a shafi na 30]

Bukukuwa na kowace shekara, kamar su Idin Bukkoki, lokatai ne na yi wa Jehovah godiya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba