Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 11/1 p. 8
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Makamantan Littattafai
  • Elisha Ya Ga Karusai na Wuta​—⁠Kai Kuma Fa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ya Jimre Har Zuwa Karshe
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Dawaki da Karusan Wuta na Jehobah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ya Sami Ƙarfafawa Daga Wajen Allahnsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 11/1 p. 8

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Me ya sa Elisha ya ce Iliya ya ba shi “rabo na ɗan fari” na ruhunsa?

Kafin Iliya ya gama aikinsa na annabi a Isra’ila, ƙaramin annabi Elisha ya roƙe shi: “Ina roƙonka, ka yarda a bar rabo na ɗan fari na ruhunka shi kasance a wurina.” (2 Sarakuna 2:9) A azanci na ruhaniya, Elisha yana son kashi biyu da ake ba wa ɗan fari ne. (Kubawar Shari’a 21:17) Idan muka ɗan bincika labarin zai bayyana sarai kuma ya taimake mu mu koya darussa daga abin da ya faru.

Daidai da umurnin Jehovah, annabi Iliya zai naɗa Elisha ya zama magajinsa. (1 Sarakuna 19:19-21) Shekaru shida, Elisha ya yi hidimar aminci na bawan Iliya kuma ya ci gaba har zuwa ƙarshe. Har a kwanaki na ƙarshe na Iliya na annabi a Isra’ila, Elisha ya manne wa malaminsa. Ko da yake Iliya ya aririci Elisha ya daina binsa, ƙaramin annabin sau uku ya ce: “Bani barinka.” (2 Sarakuna 2:2, 4, 6; 3:11) Hakika, Elisha yana ɗaukan annabin ubansa na ruhaniya.—2 Sarakuna 2:12.

Amma, ba Elisha ne kaɗai ɗa na ruhaniya na Iliya ba. Iliya da Elisha suna tarayya da wasu maza da ake ce da su “ ’ya’yan annabawa.” (2 Sarakuna 2:3) Labarin da ke Sarakuna na Biyu na nuna cewa waɗannan “ ’ya’ya” ma sun yi kusa da Iliya, ubansu na ruhaniya. (2 Sarakuna 2:3, 5, 7, 15-17) Duk da haka, shafaffe magaji Elisha shi ne ya fi cikin ’ya’ya na ruhaniyar—yana kama da ɗan fari. A Isra’ila ta dā, ɗan fari yana samun rabo biyu na gadōn ubansa, sai kuma sauran ’ya’yan su samu kashi ɗaɗɗaya. Shi ya sa Elisha ya ce a ba shi gadō na ruhaniya rabo biyu na Iliya.

Me ya sa Elisha ya yi roƙon nan a lokacin? Domin yana hanyar ɗaukan babban aiki—zai zama magajin Iliya ya zama annabi a Isra’ila. Elisha ya fahimci cewa don a cika hakkin da ke tattare da wannan aiki mai girma, yana bukatar iko na ruhaniya da ya fi nasa iyawa, iko wanda Jehovah ne zai iya bayarwa. Yana bukatar ya zama marar tsoro kamar Iliya. (2 Sarakuna 1:3, 4, 15, 16) Saboda haka, ya roƙi rabon ɗan fari na ruhun Iliya, ruhun gaba gaɗi da kuma “kishi ƙwarai domin Ubangiji”—halaye masu kyau da ruhun Allah ne kawai zai iya bayarwa. (1 Sarakuna 19:10, 14) Me Iliya ya yi?

Iliya ya sani cewa Elisha yana biɗan abin da ba zai iya bayarwa ba sai Allah ne kaɗai zai iya. Saboda haka, cikin filako Iliya ya amsa: “Ka roƙi abu mai-wuya; amma duk da haka, idan ka gan ni sa’anda an fyauce ni daga wurinka, za ya zama maka; amma idan ba haka ba ba za ya zama ba.” (2 Sarakuna 2:10) Haka nan kuma Jehovah ya yarda wa Elisha ya ga sa’ad da Iliya yake hawa cikin guguwa. (2 Sarakuna 2:11, 12) Aka ba wa Elisha abin da ya roƙa. Jehovah ya yi masa tanadin ruhun da yake bukata don ya ɗauki sabon hakki kuma ya iya fuskantar gwaji da ke gaba.

A yau, Kiristoci shafaffu (wani lokaci ana kiransu ajin Elisha) kuma bayin Allah galiba za su iya samun ƙarfafa daga wannan labarin Littafi Mai Tsarki. A wasu lokatai, za mu iya jin wasu sabon hakki sun sha mana kai, ko kuma ba mu da gaba gaɗi da ya dace don mu ci gaba cikin aikin wa’azi na Mulkin, muna fuskantar ƙarin rashin son saƙon ko kuma hamayya a yankunanmu. Amma idan muka roƙi goyon bayan Jehovah, za ya ba mu ruhu mai tsarki nasa yadda muke bukata don mu jure da kaluɓale da kuma yanayi da suke canjawa. (Luka 11:13; 2 Korinthiyawa 4:7; Filibbiyawa 4:13) Hakika kuwa, yadda Jehovah ya ƙarfafa Elisha don hakkinsa mai girma, zai taimake dukanmu, manya da ƙanana, mu cim ma hidimarmu.—2 Timothawus 4:5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba