Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 11/1 pp. 20-25
  • Mata Da Suka Faranta Wa Jehovah Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mata Da Suka Faranta Wa Jehovah Rai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mata da Suka Ƙi Biyayya da Wani Fir’auna
  • Karuwa ta Dā ta Faranta wa Jehovah Rai
  • An Albarkace ta Domin Hikimarta
  • Za Ku Iya Zama Kamar Abigail?
  • Ta Sami ‘Ladar Annabi’
  • Ta Nuna Basira
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ta Yi Amfani da Hankalinta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Abigail Da Dauda
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 11/1 pp. 20-25

Mata Da Suka Faranta Wa Jehovah Rai

“Ubangiji ya sāka miki aikinki, ki karɓi cikakkiyar lada daga wurin Ubangiji.”—Ruth 2:12.

1, 2. Ta yaya za mu iya amfana ta wurin yin tunani a kan misalan mata da suka faranta wa Jehovah rai cikin Littafi Mai Tsarki?

TSORON Allah ya motsa mata biyu su ƙi yin biyayya da wani Fir’auna. Bangaskiya ta motsa wata karuwa ta yi kasadar ranta saboda ta iya kāre Isra’ilawa biyu masu leƙen asiri. Hikima da tawali’u a lokacin wani tarzoma ya taimaki wata mace ta ceci rayuka kuma ta hana wani shafaffe na Jehovah daga ɗaukan alhakin jini. Bangaskiya ga Jehovah Allah tare da halin karimci ya motsa wata gwauruwa kuma uwa ta ba da sauran abincinta wa wani annabin Allah. Waɗannan kalilan ne kawai cikin misalai masu yawa na Nassosi na mata da suka faranta wa Jehovah rai.

2 Halin Jehovah wajen irin waɗannan mata da yadda ya albarkace su ya nuna abin da ya fi faranta masa rai cewa halaye ne na ruhaniya, ba batun ko tamace ce ko namiji ba. A cikin duniya ta yau da ta cika da ganin kyaun jiki, mai da hankali ga halaye na ruhaniya ya zama kaluɓale. Amma za a iya cim ma wannan, tun da yake miliyoyin mata da suke tsoron Allah sun nuna haka, da yake su suka fi yawa tsakanin mutanen Allah a yau. Irin waɗannan mata Kiristoci suna yin koyi da bangaskiya, hikima, karimci, da kuma wasu halayen kirki da mata masu tsoron Allah da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki suka nuna. Babu shakka, maza Kiristoci ma za su so su yi koyi da mata na dā da su misalin kirki ne. Domin mu ga yadda za mu iya yin haka sosai, bari mu bincika ƙarin daki na labaran Littafi Mai Tsarki game da mata da aka ambata a farko.—Romawa 15:4; Yaƙub 4:8.

Mata da Suka Ƙi Biyayya da Wani Fir’auna

3, 4. (a) Me ya sa Shiphrah da Puah suka ƙi su yi biyayya sa’ad da Fir’auna ya umarce su su kashe duk wani jaririn Isra’ilawa da aka haifa? (b) Ta yaya Jehovah ya albarkaci ungozomai biyun domin gaba gaɗinsu da tsoron Allah?

3 A wata ƙara ta shari’a da aka yi a Nuremberg, Jamus, bayan Yaƙin Duniya na II, mutane da yawa da doka ta kama su da laifin kisa suka yi ƙoƙarin hujjar cewa biyayya ce suka yi ga doka. Yanzu ka gwada waɗannan mutane da matan Isra’ilawa biyu da ungozomai ne, Shiphrah da Puah, da suke a Masar ta dā a lokacin sarautar wani Fir’auna mai zalunci da ba a ambata sunansa ba. Domin yana tsoron yadda jama’ar Ibraniyawa suke yawa, Fir’aunar ya umarci ungozomai biyun su tabbata an kashe duk wani jariri na Ibraniyawa. Menene matan suka yi game da wannan mugun umurni? “Ba su kuwa yi yadda sarkin Masar ya faɗa musu ba, amma suka bar ’yan maza da rai.” Me ya sa waɗannan mata suka ƙi jin tsoron mutum? Saboda su “masu-tsoron Allah ne.”—Fitowa 1:15, 17; Farawa 9:6.

4 Hakika, ungozoman sun bukaci gaba gaɗi ga Jehovah, kuma ya zama “garkuwa” gare su, ya tsare su daga fushin Fir’auna. (2 Samu’ila 22:31; Fitowa 1:18-20) Amma ba a wajen kawai albarkar Jehovah ta ƙare ba. Ya ba wa Shiphrah da Puah nasu iyali. Ya daraja waɗannan mata ta saka sunayensu da ayyukansu cikin hurariyar Kalmarsa domin tsararraki na nan gaba su karanta amma da daɗewa an manta da sunan Fir’auna.—Fitowa 1:21; 1 Samu’ila 2:30b; Misalai 10:7.

5. Ta yaya mata Kiristoci da yawa a yau suke nuna hali irin na Shiphrah da Puah, kuma ta yaya Jehovah zai albarkace su?

5 Da akwai mata ne a yau da suke kama da Shiphrah da Puah? Hakika! Kowacce shekara, dubban irin waɗannan mata suna wa’azin saƙon Littafi Mai Tsarki na ceton rai a ƙasashe da “dokar sarki” ta hana, a ta haka suna yin kasadar ’yancinsu ko kuma rayukansu. (Ibraniyawa 11:23; Ayukan Manzanni 5:28, 29) Domin ƙaunar Allah da na maƙwabci ne ta motsa su, irin waɗannan mata masu gaba gaɗi ba su yarda wa wani ya hana su faɗan bisharar Mulkin Allah wa wasu ba. Ban da haka ma, mata Kiristoci da yawa suna jure da hamayya da kuma tsanani. (Markus 12:30, 31; 13:9-13) Yadda ya faru da Shiphrah da Puah, Jehovah ya san ayyuka mafi kyau na mata masu gaba gaɗi, kuma zai nuna ƙaunarsa gare su ta sa sunayensu cikin “littafin rai” nasa, muddin dai sun jimre da aminci zuwa ƙarshe.—Filibbiyawa 4:3; Matta 24:13.

Karuwa ta Dā ta Faranta wa Jehovah Rai

6, 7. (a) Menene Rahab ta sani game da Jehovah da mutanensa, kuma yaya wannan sanin ya taimake ta? (b) Yaya Kalmar Allah ta daraja Rahab?

6 A shekara ta 1473 K.Z., wata karuwa mai suna Rahab ta yi zama a birnin Kan’ana na Jericho. A bayyane yake cewa Rahab ta koyu. Sa’ad da Isra’ilawa biyu ’yan leƙen asiri suka nemi mafaka a gidanta, ta iya gaya musu labarai ainihi game da Fitowa ta mu’ujiza ta Isra’ila daga Masar ko da a lokacin ya faru na shekaru 40! Ta kuma sani game da nasarori da Isra’ilawa suke ci a kan Sarakunan Amoriyawa, su Sihon da Og. Ka lura da yadda sanin nan ya motsa ta. Ta gaya wa ’yan leƙen asirin: “Na sani Ubangiji ya rigaya ba ku ƙasar, . . . gama Ubangiji Allahnku, shi ne Allah cikin sama a bisa, da duniya a ƙasa.” (Joshua 2:1, 9-11) Babu shakka, abin da Rahab ta koya game da Jehovah da ayyukansa domin Isra’ila ya motsa ta kuma sa ta kasance da bangaskiya gare shi.—Romawa 10:10.

7 Bangaskiyar Rahab ta motsa ta ta aikata. Ta karɓi Isra’ilawa masu leƙen asirin “lafiya,” kuma ta bi umurnin da suka ba ta game da cetonta sa’ad da Isra’ilawa za su fāɗa wa Jericho. (Ibraniyawa 11:31; Joshua 2:18-21) A bayyane yake cewa ayyukan bangaskiya ta Rahab sun faranta wa Jehovah rai, domin ya hure Kirista almajiri Yaƙub ya sa sunanta tsakanin na Ibrahim, abokin Allah, misali da Kiristoci za su yi koyi da ita. Yaƙub ya rubuta: “Hakanan kuma Rahab karuwan nan, da shi ke ta karɓi manzannin, ta sallame su kuma ta wata hanya dabam, ba ta wurin ayyuka ta barata ba?”—Yaƙub 2:25.

8. Ta yaya Jehovah ya albarkaci Rahab saboda bangaskiyarta da kuma biyayya?

8 Jehovah ya albarkace Rahab ta hanyoyi da yawa. Na ɗaya, ta mu’ujiza ya ceci ranta da na dukan waɗanda suka nemi ceto cikin gidan—watau, “iyalin ubanta, da dukan abin da ke gareta.” Sai kuma ya yarda wa waɗannan su “zauna a tsakiyar Isra’ila,” da suka zama mutanen ƙasar. (Joshua 2:13; 6:22-25; Leviticus 19:33, 34) Amma ba shi ke nan ba. Jehovah ya sake daraja Rahab ta sa ta zama kakan Yesu Kristi. Lallai alheri ne mai girma ya nuna wa mata Bakan’aniya ta dā mai bautar gunki!a—Zabura 130:3, 4.

9. Ta yaya halin Jehovah wajen Rahab da kuma wasu mata Kiristoci a ƙarni na farko zai iya ƙarfafa wasu mata a yau?

9 Kamar Rahab, wasu mata Kiristoci daga ƙarni na farko zuwa yau, sun yi watsi da hanyar lalaci domin su faranta wa Allah rai. (1 Korinthiyawa 6:9-11) Hakika, wasunsu sun yi girma a irin yanayi da ke kama da Kan’ana ce ta dā, inda lalata ce ta gama gari kuma ana ɗaukan hakan daidai ne. Duk da haka, sun yi canji a rayuwarsu, domin bangaskiya ta motsa su bisa cikakken sani na Nassosi. (Romawa 10:17) Shi ya sa, za a iya cewa irin waɗannan mata “Allah ba ya ji kunya a ce da shi Allahnsu ba.” (Ibraniyawa 11:16) Hakika daraja ce!

An Albarkace ta Domin Hikimarta

10, 11. Wane yanayi ne da ya shafi Nabal da Dauda ya sa Abigail ta aikata?

10 Mata da yawa masu aminci na dā sun nuna halin hikima a hanya ta musamman, da suka zama abin amfani mai tamani ga mutanen Jehovah. Wata cikin irin matan nan Abigail ce, matar wani Ba’isra’ile mawadaci mai gonaki, Nabal. Yadda Abigail ta nuna hikima ta sa aka ceci rayuka kuma ta hana Dauda, sarkin Isra’ila da aka naɗa daga ɗaukan alhakin jini. Za mu iya karanta game da Abigail a 1 Samuila sura ta 25.

11 Labarin ya soma da cewa, Dauda da mabiyansa sansaninsu yana kusa ne da garken Nabal, da suke kula da su dare da rana, saboda su yi alheri ga ɗan’uwansu Ba’isra’ile Nabal. Sa’ad da abincin su Dauda yake ƙarewa, ya aiki matasansa goma zuwa wajen Nabal su karɓo abinci. A wannan lokaci Nabal yana da zarafi ya yi godiya wa Dauda kuma ya daraja shi da yake shafaffe ne na Jehovah. Amma Nabal bai yi haka nan ba. Cikin fushi ya zargi Dauda kuma ya kori matasan suka koma hannu wofi. Sa’ad da Dauda ya ji wannan, ya tara mutanensa masu makamai 400 kuma suka kama hanya zuwa yin ramako. Abigail ta ji yadda mijinta ya aikata da fushi kuma nan da nan ta aikata da basira don ta samu ta roƙi Dauda, ta aika da abinci mai yawa. Sai ita da kanta kuma ta je wajen Dauda.—Ayoyi na 2-20.

12, 13. (a) Ta yaya Abigail ta kasance da hikima kuma da aminci ga Jehovah kuma ga shafaffensa? (b) Menene Abigail ta yi sa’ad da ta dawo gida, kuma yaya al’amura suka kasance gare ta?

12 Sa’ad da Abigail ta sadu da Dauda, yadda ta yi roƙo cikin sauƙin kai a yi musu jinƙai ya nuna yadda take biyayya ƙwarai ga shafaffe na Jehovah. “Hakika Ubangiji za ya tabbatadda gidan ubangijina, gama ubangijina yana yaƙin jihadin Ubangiji,” in ji ta, ta daɗa cewa Jehovah za ya sa Dauda ya zama shugaba kan Isra’ila. (Ayoyi na 28-30) Abigail a nan ta nuna gaba gaɗi, ta wurin gaya wa Dauda cewa ramakon da yake neman yi idan aka ƙyale zai jawo alhakin jini. (Ayoyi na 26, 31) Sai Dauda ya dawo hankalinsa saboda sauƙin kan Abigail, biyayya ta ƙwarai, da kuma tunaninta na kirki. Ya ce: “Mai-albarka ne Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki yau garin ki tarbe ni: mai-albarka ce hikimarki, mai-albarka ce ke kuma da kin hana ni yau daga alhakin jini.”—Ayoyi na 32, 33.

13 Bayan da ta dawo gida, Abigail ta yi ƙarfin zuciya domin ta gaya wa mijinta kyautar da ta yi wa Dauda. Amma, ta same shi “yana maye ƙwarai.” Domin haka, ta jira har ya warware kuma ta gaya masa. Me Nabal ya yi? Ya yi mamaki har ya suma. Bayan kwanaki goma sai Allah ya ƙyale shi ya mutu. Sa’ad da Dauda ya ji game da mutuwar Nabal, ya biɗa ya auri Abigail, wadda alhali ya so ta sosai kuma ya daraja ta. Abigail ta yarda ta auri Dauda.—Ayoyi na 34-42.

Za Ku Iya Zama Kamar Abigail?

14. Waɗanne halayen Abigail ne za mu so mu koya mu bi sosai?

14 Kun ga wasu halaye na Abigail da ku—maza da kuma mata—za ku so ku koya ku bi sosai? Wataƙila kana son ka kasance da basira da kuma hikima sa’ad da matsala ta taso. Ko kuma za ka so ka yi magana da taushi kuma cikin fahimi sa’ad da wasu da kuke tare sun yi fushi. Idan haka ne, ka yi addu’a ga Jehovah game da al’amarin? Ya yi alkawarin zai ba da hikima, fahimi, da kuma basira ga dukan waɗanda suka ‘roƙa da bangaskiya.’—Yaƙub 1:5, 6; Misalai 2:1-6, 10, 11.

15. Cikin wane irin yanayi ne musamman ya kamata mata Kirista su nuna halaye na Abigail?

15 Ana bukatar halayen nan musamman ga macen da mijin ba mai bi ba ne wanda ba ya bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Wataƙila mashayi ne ƙwarai. Da fatan irin mazajen nan za su canja hanyar rayuwarsu. Mutane da yawa sun yi haka—waɗanda yawanci saboda taushin hali ne, biyayya ta ƙwarai, da kuma tsabtar ɗabi’ar matansu.—1 Bitrus 3:1, 2, 4.

16. Ko da wane irin yanayi yake iyalinta, yaya ya kamata ’yar’uwa Kirista za ta nuna cewa tana daraja dangantakarta da Jehovah fiye da kome?

16 Ko da wane irin wahala kike jurewa da ita a gida, ki tuna cewa Jehovah yana tare da ke yana goyon bayanki. (1 Bitrus 3:12) Saboda haka, ki yi ƙoƙari ki yi ƙarfi a ruhaniya. Ki yi addu’a domin hikima da taushin rai. Hakika, ki matso kusa da Jehovah ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, addu’a, yin bimbini, da kuma yin tarayya da ’yan’uwa Kirista. Ƙaunar Abigail ga Allah da kuma halinta game da shafaffen bawansa ba domin mijinta ba shi da ruhaniya ba ne. Ta aikata domin ƙa’idodi na adalci ne. Ko a cikin iyalin da miji bawan Allah ne mai halin kirki, mata Kirista tana bukatar ta yi ƙoƙari ta gina kuma adana ruhaniyarta. Babu shakka, mijinta yana da hakkin ya kula da lafiyarta ta ruhaniya da ta jiki, amma daga bisani, dole ne ta yi ‘aikin cetonta da tsoro da rawan jiki.’—Filibbiyawa 2:12; 1 Timothawus 5:8.

Ta Sami ‘Ladar Annabi’

17, 18. (a) Da wane gwajin bangaskiya aka gwada gwauruwa na Zarephath? (b) Yaya gwauruwar ta aikata ga roƙon da Iliya ya yi, kuma yaya Jehovah ya albarkace ta domin wannan?

17 Yadda Jehovah ya kula da gwauruwa matalauciya a zamanin annabi Iliya ya nuna yadda ya ke son waɗanda suke goyon bayan bauta ta gaskiya ta wurin ba da kansu da kuma abin da suke da shi. Saboda fari na shekaru da yawa da aka yi a zamanin Iliya, mutane da yawa sun yi yunwa, har da gwauruwa da ƙaramin ɗanta da suke zama a Zarephath. Sa’ad da suke da abincinsu na ƙarshe ne, sai ga baƙo ya zo—annabi Iliya. Sai ya biɗi abin da ba a tsammaninsa. Ko da yake ya san damuwar matan, ya ce ta gasa masa “ɗan waina,” ta yi amfani da sauran mai da kuma garin. Amma ya daɗa cewa: “Gama hakanan Ubangiji ya faɗi, Allah na Isra’ila, Tukunyar gāri ba za ta sare ba, kurtun mai kuma ba za ya sare ba, har ran da Ubangiji ya aiko da ruwa bisa ƙasa.”—1 Sarakuna 17:8-14.

18 Da yaya za ka yi game da irin wannan roƙo? Babu shakka gwauruwa ta Zarephath ta fahimci cewa Iliya annabin Jehovah ne, “ta yi bisa ga fāɗin Iliya.” A wace hanya ce Jehovah ya dubi halinta na karimci? Ta hanyar mu’ujiza ya yi tanadin abinci wa matan, ɗanta, da kuma Iliya a duk lokacin farin. (1 Sarakuna 17:15, 16) Hakika kuwa, Jehovah ya ba wa gwauruwar Zarephath “ladar annabi,” ko da yake ita ba Ba’isra’iliya ba ce. (Matta 10:41) Ɗan Allah ma ya daraja wannan gwauruwa da ya ambata ta misali ga mutanen da ba su da bangaskiya a garinsa na Nazarat.—Luka 4:24-26.

19. A waɗanne hanyoyi mata Kiristoci da yawa a yau suke nuna irin halin gwauruwa na Zarephath, kuma yaya Jehovah yake ji game da waɗannan?

19 A yau, Kiristoci mata da yawa suna nuna irin halin gwauruwa na Zarephath. Alal misali, kowane mako ’yan’uwa mata Kiristoci—waɗanda matalauta ne da yawa da suke da iyalai da suke kula da su—suna nuna karimci ga masu kula masu ziyara da matansu. Wasu kuma suna ba da abinci da suke da shi wa masu hidima na cikakken lokaci, suna taimakon mabukata, ko kuma suna ba da kansu da abin da suke da shi don goyon bayan aikin Mulkin a wasu hanyoyi. (Luka 21:4) Jehovah yana ganin irin bayarwar nan kuwa? Babu shakka! “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa, yayinda kuka hidimta ma tsarkaka, kuna kuwa yi har wa yau.”—Ibraniyawa 6:10.

20. Me za a yi la’akari da shi a talifi na gaba?

20 A ƙarni na farko, mata masu tsoron Allah da yawa sun sami gatar yin hidima ga Yesu da manzanninsa. A cikin talifi na gaba, za mu tattauna yadda waɗannan mata suka faranta wa Jehovah rai, kuma za mu yi la’akari da misalan mata na zamani da sun bauta wa Jehovah da zuciya ɗaya, har cikin yanayi masu wuya ma.

[Hasiya]

a Labarin Matta game da zuriyar Yesu ya ambata mata huɗu da suna—Tamar, Rahab, Ruth, da Maryamu. Ana ɗaukan dukansu da daraja cikin Kalmar Allah.—Matta 1:3, 5, 16.

A Maimaitawa

• A wace hanya waɗannan mata suka faranta wa Jehovah rai?

• Shiphrah da Puah

• Rahab

• Abigail

• Gwauruwar Zarephath

• Ta yaya yin bimbini a kan misalan waɗannan mata zai taimake mu? Ka ba da misali.

[Hotuna a shafi na 21]

Mata masu aminci da yawa sun bauta wa Allah duk da ‘umurnin sarki’

[Hoto a shafi na 22]

Me ya sa Rahab misali ne mai kyau na wadda take da bangaskiya?

[Hoto a shafi na 22]

Waɗanne halaye da Abigail ta nuna kake son ka yi koyi da su?

[Hoto a shafi na 24]

Mata Kiristoci da yawa a yau suna da irin halin gwauruwa na Zarephath

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba