Ƙauna da Take Ja-Gora
A YAWANCIN wurare cikin Nassosin Helenanci na Kirista, ko kuma Sabon Alkawari, an fassara kalmar Helenancin nan a·gaʹpe da “ƙauna.”
Wajen bayyana ma’anar furcin, wata majiya a kan Insight on the Scripturesa ta ce: “[A·gaʹpe] ba tsotsuwar zuciya ba ne, da ke bisa son wane yadda mutane ke tunaninsa, amma ƙauna ce ta ɗabi’a na jama’a da ke bisa batu na ƙa’ida, aiki, abin da ya dace, biɗan abin da yake nagari domin wani. Ƙauna ta a·gaʹpe ba ta sanin magabtaka, ba ta yarda wa waɗannan su sa ta yasar da nagargarun ƙa’idodi kuma ta yi ramako ba.”
A·gaʹpe ma zai iya haɗa da jiye-jiye mai zurfi. “Ku zama da ƙauna [a·gaʹpe] mai-huruwa zuwa ga junanku,” in ji manzo Bitrus. (Tafiyar tsutsa tamu ce; 1 Bitrus 4:8.) Saboda haka, za a iya ce a·gaʹpe ya shafi zuciya ba azanci kawai ba. Me ya sa ba za ka bincika wasu nassosi da ke nuna iko da girman ƙauna mai ja-gora ba? Ƙila waɗannan nassosi za su iya taimakawa: Matta 5:43-47; Yohanna 15:12, 13; Romawa 13:8-10; Afisawa 5:2, 25, 28; 1 Yohanna 3:15-18; 4:16-21.
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga.