“Kowacce Rana Shi Biyo ni”
“Zuwa wannan aka kiraye ku: gama Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar muku gurbi, domin ku bi sawunsa.”—1 BITRUS 2:21.
1, 2. Me ya sa misalin Yesu mafi kyau na malami bai yi girma ainun ba mu yi koyi da shi?
YESU KRISTI ne babban Malami da ya taɓa rayuwa a duniya. Ƙari ga haka, kamiltacce ne, bai yi zunubi ba a duk rayuwarsa na mutum. (1 Bitrus 2:22) Wannan yana nufi ne cewa, misalin Yesu na malami ya yi girma ainu da mu ajizai ba za mu iya kwaikwayon shi ba? Ko kaɗan.
2 Yadda muka gani a talifi da ya gabata, tushen koyarwar Yesu ƙauna ne. Kuma ƙauna aba ce da dukanmu za mu iya koya. Kalmar Allah sau da yawa tana ariritarmu mu yi girma kuma mu yi gyara a ƙaunar juna. (Filibbiyawa 1:9; Kolossiyawa 3:14) Jehovah ba ya bukatar halittunsa su yi abin da ba za su iya ba. Hakika, tun da “Allah ƙauna ne” kuma ya yi mu a surarsa, za a ce ya yi mu don mu nuna ƙauna ne. (1 Yohanna 4:8; Farawa 1:27) Saboda haka, sa’ad da muka karanta kalmomin manzo Bitrus da ke ayar jigonmu, za mu amsa da tabbaci. Za mu iya bin sawun Kristi sosai. Hakika, za mu yi biyayya ga umurnin Yesu: “Kowacce rana, shi biyo ni.” (Luka 9:23) Bari mu yi la’akari da yadda za mu yi koyi da ƙaunar da Kristi ya nuna, na farko ga gaskiya da ya koyar, sa’annan ga mutane da ya koyar.
Gina Ƙauna ga Gaskiya da Muka Koya
3. Me ya sa wasu suke iske shi da wuya su yi nazari, amma wane gargaɗi aka samu a Misalai 2:1-5?
3 Don mu yi ƙaunar gaskiya da muke koya wa wasu, dole ne mu yi ƙaunar koyon gaskiyar mu kanmu. A duniya ta yau, irin wannan ƙaunar ba a koyonta da sauƙi. Abubuwa kamar rashin isashen makarantu da halaye da ba su da kyau da aka koya lokacin ƙuruciya na sa wasu ba sa son nazari. Amma, yana da muhimmanci, mu koya daga Jehovah. Misalai 2:1-5 ta ce: “Ɗana, idan ka karɓi zantattukana, ka ɓoye dokokina a wurinka: Har da za ka karkata kunnenka ga hikima, ka maida zuciyarka ga fahimi: I, idan ka nace bin ganewa, ka tada muryarka garin neman fahimi: Idan ka neme ta kamar azurfa, ka biɗe ta kamar da a ke biɗan ɓoyayyun dukiya: Sa’annan za ka gane tsoron Ubangiji, ka ruski sanin Allah.”
4. Menene yake nufi a “maida” zuciya, wane ra’ayi zai taimake mu yin haka?
4 Ka lura cewa cikin aya ta 1 zuwa ta 4 an aririce mu a kai a kai mu sa ƙoƙari ba kawai mu “karɓi” kuma mu “ɓoye dokoki” ba amma mu “neme ta” kuma mu “biɗe ta.” Menene zai motsa mu mu yi dukan wannan? To, ka lura da furcin nan “ka maida zuciyarka ga fahimi.” Wani aikin bincike ya ce wannan gargaɗin “ba roƙo ba ne kawai don a mai da hankali: bukata ce na wani hali: son koyarwa.” Menene zai sa mu yarda kuma mu yi ɗokin koyon abin da Jehovah yake koya mana? Ra’ayinmu. Muna bukatar mu ɗauki “sanin Allah” kamar “azurfa” da kuma “ɓoyayyun dukiya.”
5, 6. (a) Menene zai iya faruwa da shigewar lokaci, kuma yaya za mu hana wannan? (b) Me ya sa za mu ci gaba da ƙara wa sani da muka samu daga Littafi Mai Tsarki?
5 Ba shi da wuya mu samu irin wannan ra’ayin. Alal misali, “sanin Allah” da ka koya wataƙila ya ƙunshi gaskiya cewa nufin Jehovah ne mutane masu aminci su rayu har abada cikin Aljanna a duniya. (Zabura 37:28, 29) Sa’ad da ka koyi gaskiya da farko, babu shakka ka ɗauke ta dukiya mai tamani, sani da ya cika azancinka da zuciyarka da bege da kuma farin ciki. Yanzu kuma fa? Da shigewar lokaci, godiyarka ga dukiyar ta yi yaushi ne? To, ka yi ƙoƙari ka yi abubuwa biyu. Na farko, ka sabonta godiyarka, watau ka wartsake zuciyarka a kai a kai da dalilin da ya sa ka daraja kowacce gaskiya da Jehovah ya koya maka, har da waɗanda ka koya shekaru da yawa da suka shige.
6 Na biyu, ka ci gaba da ƙara dukiyarka. A ce ka tono wani lu’ulu’u, za ka saka cikin aljihunka ne kawai ka kama hanya kana jin daɗi? Ko kuma za ka ƙara tonowa ne ka gani ko za ka sake samun wasu? Kalmar Allah na cike da lu’ulu’u da bayani mai kyau na gaskiya. Ko nawa ka samu, za ka ƙara samu. (Romawa 11:33) Sa’ad da ka koyi sabon fanni na gaskiya, ka tambayi kanka: ‘Me ya sa ya zama dukiya? Ta sa na san mutuntaka ko nufe-nufen Jehovah sosai? Ta ba ni ja-gora mai kyau da zai taimaka mini na bi sawun Yesu?’ Yin bimbini a kan irin waɗannan tambayoyi zai taimake ka ka gina ƙauna ga gaskiya da Jehovah ya koya maka.
Nuna Ƙauna ga Gaskiya da Muke Koyarwa
7, 8. Waɗanne hanyoyi za mu nuna wa wasu cewa muna ƙaunar gaskiya da muka koya daga Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.
7 Yayin da muke koya wa wasu, ta yaya za mu nuna muna ƙaunar gaskiya da muka koya daga Kalmar Allah? Bin misalin Yesu, za mu dogara ƙwarai da Littafi Mai Tsarki a wa’azi da kuma koyarwa da muke yi. A baya bayan nan, an ƙarfafa mutanen Allah a dukan duniya su yi amfani da Littafi Mai Tsarki a hidimarsu ta fage sosai. Sa’ad da kake amfani da wannan shawara, ka nemi hanyoyi da za ka sa maigidan ya sani cewa kana son abin da kake gaya masa daga Littafi Mai Tsarki.—Matta 13:52.
8 Alal misali, bayan ta’adancin da ’yan ta’ada suka yi a Amirka shekara da ta shige, wata ’yar’uwa Kirista tana karanta wa mutane da ta same su a hidima Zabura 46:1, 11. Da farko tana tambayar mutanen yadda suke ji da haƙuri bayan masifar. Sai ta saurare su sosai, ta yarda da abin da suka ce, sai ta ce: “Bari in karanta muku nassin da ya yi mini jaje a wannan lokaci mai wuya?” Mutane kalilan ne suka ƙi, sakamakon haka shi ne ta tattauna da mutane da yawa. A yin magana da matasa, ’yar’uwar sau da yawa takan ce: “Ina koyar da Littafi Mai Tsarki shekara 50 yanzu, kun sani? Ban taɓa ganin matsala da wannan littafi bai warware ba.” Ta kusantar mutane da marmari da kuma ƙwazo, muna nuna wa mutane cewa muna daraja kuma muna ƙaunar abin da muka koya daga Kalmar Allah.—Zabura 119:97, 105.
9, 10. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke ba da amsa game da imaninmu?
9 Sa’ad da mutane suka yi mana tambaya game da imaninmu, muna da zarafi mai kyau mu nuna cewa muna ƙaunar Kalmar Allah. A bin misalin Yesu, ba ma ba da amsarmu daga namu ra’ayin ba kawai. (Misalai 3:5, 6) Maimakon haka, za mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki mu ba da amsa. Kana jin tsoro ne cewa wani zai yi maka tambayar da ba za ka iya amsawa ba? Yi la’akari da matakai biyu masu kyau da za ka ɗauka.
10 Ka yi abin da za ka iya don ka yi shiri. Manzo Bitrus ya rubuta: “Cikin zukatanku ku tsarkake Kristi kamar Ubangiji: kullum a shirye ku ke ku amsa ma kowane mai-tambayanku dalilin begen da ke cikinku, amma dai da ladabi da tsoro.” (1 Bitrus 3:15) Kana shirye ka ba da amsa game da imaninka? Alal misali, idan wani yana son ya san abin da ya sa ba ka sa hannu cikin wasu al’adu ko ayyuka da ba na nassi ba, kada ka gamsu da cewa kawai, “Addininmu ba ta yinsu.” Irin wannan amsar za ta nuna cewa kana barin wasu su tsai da maka shawara kuma saboda haka, kana cikin wani rukuni ne na asiri. Zai fi kyau ka ce, “Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, ta hana,” ko kuma, “Zai baƙanta wa Allahna rai.” Sai ka ba da bayanin abin da ya kawo haka.—Romawa 12:1.
11. Waɗanne kayan bincike za su taimake mu mu kasance a shirye mu amsa tambayoyi game da gaskiyar Kalmar Allah?
11 Idan ka ga ba ka yi shiri ba, me ya sa ba za ka keɓe lokaci ba ka yi nazarin ƙasidar nan Darussan Littafi Mai-Tsarki Don Mahawwara.a Ka zaɓi wasu darussa da wataƙila mutane za su yi maka tambaya a kai, ka maimaita wasu darussa na nassi. Kana tafiya da naka ƙasidar Darussan Littafi Mai-Tsarki Don Mahawwara da kuma Littafi Mai Tsarki. Kada ka yi jinkirin yin amfani da dukansu biyu, ka gaya wa mai tambayar cewa kana da kayan bincike da za ka yi amfani da su ka samu amsar Littafi Mai Tsarki ga tambayar.
12. Yaya za mu amsa idan ba mu san amsar tambaya ta Littafi Mai Tsarki ba?
12 Kada ka damu ainu. Babu ɗan Adam ajizi da ya san amsar kome. Saboda haka, idan an yi maka tambaya daga Littafi Mai Tsarki da ba za ka iya ba da amsar ba, za ka iya cewa: “Mun gode da irin wannan tambaya mai kyau da ka yi. Da gaske, ban san amsar ba, amma na tabbata cewa Littafi Mai Tsarki zai ba da amsar. Ina son na yi bincike na Littafi Mai Tsarki, zan yi bincike a kan tambayarka na dawo na ba ka amsa.” Irin wannan amsar na gaske da kuma ladabi za ta iya kawo ƙarin tattaunawa.—Misalai 11:2.
Ƙaunar Mutane da Muke Koyar da Su
13. Me ya sa ya kamata mu kasance da ra’ayi mai kyau game da waɗanda muke musu wa’azi?
13 Yesu ya yi ƙaunar mutane da ya koyar da su. Ta yaya za mu yi koyi da shi game da wannan? Bai kamata mu koyi halin ba ruwana ba game da mutane da suka kewaye mu. Hakika, “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka” yana matsowa kurkusa, kuma za a halaka da yawa cikin biliyoyin ’yan Adam. (Ru’ya ta Yohanna 16:14; Irmiya 25:33) Duk da haka, ba mu san wanda zai rayu da kuma wanda zai mutu ba. Za a yi wannan hukunci a nan gaba kuma wanda Jehovah ya naɗa, Yesu Kristi zai yi wannan. Har sai an yi shari’ar, muna ɗaukan kowanne mutum zai zama bawan Jehovah.—Matta 19:24-26; 25:31-33; Ayukan Manzanni 17:31.
14. (a) Yaya za mu bincika kanmu mu san ko muna da juyayi game da mutane? (b) A waɗanne hanyoyi masu kyau za mu nuna juyayi da damuwa ga wasu?
14 Saboda haka, kamar Yesu, muna nema mu yi juyayin mutane. Za mu iya tambayar kanmu: ‘Ina juyayin mutane da aka ruɗe su da ƙarya da ruɗu na addinai, siyasa, da kuma kasuwanci na wannan duniya? Idan ba sa son su ji saƙon da muka kawo musu, na fahimci dalilin da ya sa suke jin haka? Na fahimci cewa ni da wasu da muke bauta wa Jehovah yanzu cikin aminci, dā mun ji haka? Na kyautata yadda nake yin wa’azi domin wannan? Ko kuma ina ƙin waɗannan mutane cewa ba za su taɓa canjawa ba?’ (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Sa’ad da mutane suka ga juyayinmu na gaske, za su fi saurarar saƙonmu. (1 Bitrus 3:8) Juyayi zai sa mu nuna muna son mutane da muka sadu da su a hidima. Muna iya rubuta tambayoyinsu da damuwansu. Idan muka koma, za mu iya nuna musu cewa muna tunani game da abin da suka faɗa sa’ad da muka ziyarce su. Mu sa su sani cewa idan suna da bukata ta gaggawa a lokacin, za mu iya taimaka musu.
15. Me ya sa za mu nemi abu mai kyau cikin mutane, yaya za mu yi haka?
15 Kamar Yesu, muna neman abu mai kyau cikin mutane. Wataƙila uwa gwauruwa tana ƙoƙari ta yi renon yaranta da kyau. Wani yana fama ya tallafa wa iyalinsa. Tsoho yana son abubuwa na ruhaniya. Muna lura da irin waɗannan abubuwa a wajen mutane da muke saduwa da su kuma mu yaba musu? A yin haka, muna nanata abin da muka yarda da shi kuma zai iya buɗe hanyar yin wa’azi game da Mulkin.—Ayukan Manzanni 26:2, 3.
Tawali’u Wajibi ne a Nuna Ƙauna
16. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da taushin hali da ladabi ga waɗanda muke musu wa’azi?
16 Ƙaunar mutane da muke koyar da su za ta motsa mu mu yi biyayya ga gargaɗi na Littafi Mai Tsarki: “Ilimi kuwa ya kan sa kumbura, amma ƙauna ta kan yi gini.” (1 Korinthiyawa 8:1) Yesu yana da ilimi sosai, duk da haka bai da girman kai. Saboda haka, sa’ad da kake bayyana imaninka, ka guje wa yin musu ko nuna ka fi sani. Muradinmu shi ne mu kai zukata kuma mu jawo mutane zuwa gaskiya da muke so sosai. (Kolossiyawa 4:6) Ka tuna, sa’ad da Bitrus ya gargaɗi Kiristoci su kasance a shirye su ba da amsa, ya kuwa tuna musu cewa ya kamata mu yi haka “da ladabi da tsoro.” (1 Bitrus 3:15) Idan muna da taushin hali da ladabi, za mu fi jawo mutane ga Allah da muke bauta wa.
17, 18. (a) Ta yaya ya kamata mu mai da martani ga halaye da ba shi da kyau game da cancantarmu na masu hidima? (b) Me ya sa sanin harsuna na dā na Littafi Mai Tsarki ba shi da muhimmanci ga ɗaliban Littafi Mai Tsarki?
17 Babu amfanin mu burge mutane da iliminmu. Idan wasu a yankinku suna ƙin saurarar wani da ba shi da digiri ko wani matsayi, kada ka yarda wannan hali ya sa ka kasala. Yesu bai saurari maganar cewa bai je babban makarantu na malamai na kwanansa ba; kuma bai faɗā wa wariyar addini ta ƙoƙari ya burge mutane da yawan iliminsa ba.—Yohanna 7:15.
18 Tawali’u da ƙauna sun fi yawan makaranta muhimmanci ga masu hidima ta Kirista. Babban Mai Koyarwa, Jehovah, yana isar da mu don hidima. (2 Korinthiyawa 3:5, 6) Ko da menene wasu limaman Kiristendam suka ce, ba ma bukatar mu koyi harsuna ta dā na Littafi Mai Tsarki don mu zama masu koyar da Kalmar Allah. Jehovah ya hure a rubuta Littafi Mai Tsarki cikin furci da ke a bayyane na ainihi da kusan kowa zai fahimci gaskiyarsa mai tamani. Wannan gaskiyar ba ta canja ba har lokacin da aka fassara zuwa ɗarurruwan harsuna. Saboda haka, sanin harsuna na dā, ko da wani lokaci ana amfani da su, ba su da muhimmanci. Ƙari ga haka, fahariya wajen iya wani yare za ta iya sa mutum ya yi hasarar hali da yake da muhimmanci ga Kiristoci na gaskiya—iya koyarwa.—1 Timothawus 6:4.
19. A wane azanci ne hidimarmu ta Kirista aiki ne na tawali’u?
19 Babu shakka cewa hidimarmu ta Kirista aiki ne da ke bukatar hali na tawali’u. A kai a kai muna fuskantar hamayya, ƙiyayya, da kuma tsanantawa. (Yohanna 15:20) Duk da haka, ta cika hidimarmu cikin aminci, muna aiki da yake da muhimmanci. Idan mun ci gaba da yi wa wasu hidima cikin tawali’u a wannan aikin, muna koyi da ƙauna da Yesu Kristi ya nuna ga mutane. Yi la’akari: Idan ya kamata mu yi wa’azi ga mutane dubbai da ba sa so ko suke hamayya don mu kai mutum guda mai kama da tunkiya, kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba? Babu shakka! Saboda haka, ta nacewa a aikin, ban da fid da rai, muna yi wa mutane masu kama da tumaki da ba mu kai ba tukuna hidima cikin aminci. Babu shakka Jehovah da Yesu za su tabbata cewa irin waɗannan mutane masu tamani za a same su kuma a taimaka musu kafin ƙarshen ya zo.—Haggai 2:7.
20. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya koyar ta misali?
20 Koyarwa da misali wata hanya ce ta nuna cewa muna da yardan rai mu yi wa wasu hidima. Alal misali, muna son mu koya wa mutane cewa bauta wa Jehovah, ‘Allah mai farin ciki,’ hanya ce mafi kyau mai gamsarwa a rayuwa. (1 Timothawus 1:11) Sa’ad da suke lura da halinmu da yadda muke bi da maƙwabtanmu, abokan makaranta, abokan aiki, suna gani cewa muna da farin ciki da gamsuwa? Hakanan ma, muna koya wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki cewa ikilisiyar Kirista ce wurin ƙauna a duniyar da ba ta da juyayi, da ta cika da mugunta. Ɗaliban suna ganin cewa muna ƙaunar duka cikin ikilisiya kuma muna aiki tuƙuru mu kasance da salama da juna?—1 Bitrus 4:8.
21, 22. (a) Bincika kanmu game da hidimarmu zai sa mu yi amfani da waɗanne zarafi? (b) Menene za a tattauna cikin fitar talifan Hasumiyar Tsaro ta gaba?
21 Halin yardan rai game da hidimarmu, wani lokaci zai motsa mu mu sake bincika kanmu. Da suka yi haka da gaske, mutane da yawa sun ga cewa za su iya faɗaɗa hidimarsu ta ɗaukan hidima ta cikakken lokaci ko su ƙaura zuwa inda ake da bukata mafi yawa. Wasu sun koyi wani yare don su koya wa mutane da suke shigowa yankinsu. Idan kana da irin wannan zarafin, ka yi addu’a game da wannan. Rayuwa ta hidima tana kawo farin ciki, gamsuwa, da kwanciyar hankali mai yawa.—Mai-Wa’azi 5:12.
22 A kowacce hanya, bari mu ci gaba da yin koyi da Yesu Kristi ta gina ƙauna don gaskiya da muke koyarwa da mutane da muke koya musu. Gina da kuma nuna ƙauna a waɗannan hanyoyi biyu za su taimaka mana mu kafa tushe mai kyau ta zama masu koyarwa kamar Kristi. Ta yaya, za mu yi gini a kan wannan harsashi? A Hasumiyar Tsaro fita ta gaba, talifai na gaba za su tattauna wasu takamammun hanyoyin koyarwa da Yesu ya yi amfani da su.
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane tabbaci muke da shi cewa misalin Yesu na malami bai yi girma ainun da ba za mu iya koyi da shi ba?
• Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar gaskiya da muka koya daga Littafi Mai Tsarki?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da tawali’u yayin da muke ƙaruwa a ilimi?
• Waɗanne hanyoyi za mu nuna muna ƙaunar mutane da muke koyar da su?
[Hotuna a shafi na 10]
Ka yi abin da za ka iya ka yi shiri
[Hotuna a shafuffuka na 10, 11]
Idan ka ruski “sanin Allah” za ka iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kyau
[Hoto a shafi na 12]
Muna nuna ƙauna ga mutane ta gaya musu bishara