Albarkar Jehovah Takan Kawo Mana Wadata
“Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.”—MISALAI 10:22.
1, 2. Me ya sa farin ciki ba shi da mahaɗi da wadata?
BIƊAN abin duniya shi yake ja-gorar rayuwar miliyoyin mutane a yau. Amma abin duniya yana ba da farin ciki ne? “Ban ga lokacin da mutane suke yawan gunaguni ba game da rayuwarsu kamar yanzu,” in ji jaridar The Australian Women’s Weekly. Ta daɗa: Da saɓani. An gaya mana cewa Australiya tana da wadata sosai, rayuwa ta fi ta dā. . . . Duk da haka rashin bege ya cika ko’ina a ƙasar. Maza da mata duka sun fahimci cewa wani abu ya ɓace daga rayuwarsu amma ba su iya faɗin ko menene ba.” Gaskiya ne da Nassosi suka nuna cewa farin ciki ko kuwa rai ba daga yawar dukiya da muke da ita ake samu ba!—Mai-Wa’azi 5:10; Luka 12:15.
2 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa farin ciki na zuwa daga albarkar Allah ce. Game da wannan, Misalai 10:22 ta ce: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.” Tara abin duniya cikin haɗama sau da yawa na kawo baƙin ciki. Daidai kuwa, manzo Bulus ya yi kashedi: “Waɗanda suna so su zama mawadata su kan fāɗa cikin jaraba da tarko da sha’awoyi dayawa na wauta da ɓarna, irin da kan dulmaya mutane cikin hallaka da lalacewa. Gama son kuɗi asalin kowace irin mugunta ne: waɗansu kuwa garin begen samu sun ratse daga imani, sun huda kansu da baƙinciki mai-yawa.”—1 Timothawus 6:9, 10.
3. Me ya sa bayin Allah suke fuskantar gwaji?
3 A wata sassa, albarka da ba ta kawo baƙin ciki tana tarar da duka waɗanda suke “saurara ga muryar Ubangiji.” (Kubawar Shari’a 28:2) Amma, wasu za su yi tambaya, ‘Idan ba a haɗa baƙin ciki da albarkar Jehovah, me ya sa bayin Allah da yawa suke shan wuya?’ Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa Allah yana ƙyale gwajinmu amma asalinsu daga Shaiɗan ne, da mugun tsarinsa, da kuma ajizancinmu. (Farawa 6:5; Kubawar Shari’a 32:4, 5; Yohanna 15:19; Yaƙub 1:14, 15) Jehovah ne tushen “kowacce kyakkyawar baiwa da kowacce cikakkiyar kyauta.” (Yaƙub 1:17) Saboda haka, albarkarsa ba ta kawo baƙin ciki. Bari mu bincika wasu cikakkun kyauta na Allah.
Kalmar Allah—Kyauta Mai Tamani
4. Wace albarka ce da kyauta mai tamani mutanen Jehovah suke morewa a wannan “kwanakin ƙarshe”?
4 Game da “kwanakin ƙarshe,” annabcin Daniel ya ce: “Ilimi kuma za ya ƙaru.” Amma, waɗannan kalmomin sun rage ma’anar cewa: “Miyagu kuma babu mai-fahimtawa; amma waɗanda su ke da hikima za su gane.” (Daniel 12:4, 10) Ka yi tunanin wannan! Kalmar Allah—musamman annabci—an furta ta da hikima ta Allah da miyagu ba za su fahimta ba, amma mutanen Jehovah za su fahimta. Ɗan Allah ya yi addu’a a fili yana cewa: “Ina gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Luka 10:21) Albarka ce mu samu kyauta mai tamani na rubucacciyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, kuma mu kasance tsakanin waɗanda Jehovah ya ba su fahimi na ruhaniya!—1 Korinthiyawa 1:21, 27, 28; 2:14, 15.
5. Mecece hikima, kuma yaya za mu same ta?
5 Da ba za mu samu fahimi na ruhaniya ba in ba domin mun samu “hikima mai-fitowa daga bisa” ba. (Yaƙub 3:17) Hikima yin amfani ne da ilimi da fahimi wajen warware matsaloli, guje wa haɗari, cim ma makasudai, ko kuma ba da gargaɗi mai kyau. Ta yaya za mu samu hikima ta Allah? Misalai 2:6 ta ce: “Ubangiji yana bada hikima: daga cikin bakinsa ilimi da fahimi su ke fitowa.” Hakika, Jehovah zai albarkace mu da hikima idan mun nace da yin addu’a dominta, yadda ya ba Sarki Sulemanu “zuciya mai-hikima, mai-ganewa.” (1 Sarakuna 3:11, 12; Yaƙub 1:5-8) Don mu samu hikima, dole mu ci gaba da saurarar Jehovah ta nazari a kai a kai da yin amfani da Kalmarsa.
6. Me ya sa hikima ce mu yi amfani da dokoki da ƙa’idodin Allah a rayuwarmu?
6 Misalan hikima na Allah na musamman ana samunsu cikin dokoki da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan suna amfanar mu a kowacce hanya—a zahiri, a hankali, a jiye-jiye, kuma a ruhaniya. Mai Zabura ya rera waƙa da ta dace: “Shari’a ta Ubangiji cikakkiya ce, tana mayarda rai: shaidar Ubangiji tabbataciya ce, tana sa mara-sani ya zama mai-hikima. Dokokin Ubangiji madaidaita ne, masu-faranta zuciya: umurnin Ubangiji tsatsarka ne, yana haskaka idanu. Tsoron Ubangiji da tsabta ya ke, matabbaci ne har abada: hukuntai na Ubangiji masu-gaskiya ne, masu-adalci ne dukansu. Abin marmari ne gaba da zinariya, i, gaba da yawan zinariya mai-kyau.”—Zabura 19:7-10; 119:72.
7. Menene sakamakon raina mizanan Allah na adalci?
7 A wata sassa, waɗanda suka raina mizanan Allah na adalci ba sa samun farin ciki da ’yanci da suke nema. Kome daren daɗewa, suna gane cewa ba a yi wa Allah ba’a, gama iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe. (Galatiyawa 6:7) Miliyoyin mutane da suka raina mizanan Littafi Mai Tsarki suna girbe bala’i kamar su cikin shege, cututtuka masu ban ƙyama, ko kuma jarabobbi. Sai dai sun tuba sun canja tafarkin rayuwarsu, al’amuransu babu shakka zai kai su ga mutuwa kuma wataƙila halaka a hannun Allah.—Matta 7:13, 14.
8. Me ya sa masu ƙaunar Kalmar Allah suke farin ciki?
8 Amma, waɗanda suke ƙaunar Kalmar Allah kuma suke yin amfani da ita albarka mai girma za ta tarar da su yanzu da kuma nan gaba. Suna da dalilin jin dokar Allah ta ’yantar da su, suna farin ciki da gaske, kuma suna jiran lokacin da za a ’yantar da su daga zunubi da sakamakonsa na mutuwa. (Romawa 8:20, 21; Yaƙub 1:25) Wannan begen tabbacacce ne domin ya dangana a kan kyautar Allah mafi kyau ga mutane—hadayar fansa ta Ɗansa makaɗaici, Yesu Kristi. (Matta 20:28; Yohanna 3:16; Romawa 6:23) Irin wannan kyauta mafi girma ta nuna zurfin ƙaunar Allah ga ’yan Adam kuma ta tabbatar da albarka mara iyaka ga duk waɗanda suka ci gaba da sauraron Jehovah.—Romawa 8:32.
Muna Godiya don Kyautar Ruhu Mai Tsarki
9, 10. Ta yaya muke amfana daga kyautar Jehovah na ruhu mai tsarki? Ka ba da misali.
9 Wata kyautar Allah mai kyau da ya kamata mu yi godiya a kai shi ne ruhunsa mai tsarki. A ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., manzo Bitrus ya aririci jama’ar da ke wurin a Urushalima: “Ku tuba, a yi ma kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi zuwa gafarar zunubanku; za ku karɓi Ruhu Mai-tsarki kyauta kuma.” (Ayukan Manzanni 2:38) A yau, Jehovah yana ba da ruhu mai tsarki ga bayinsa da suka keɓe kansu da suke addu’a dominsa kuma suna son su yi nufinsa. (Luka 11:9-13) A lokatan dā, wannan iko mai ƙarfi a dukan sararin samaniya—ruhun Allah mai tsarki, ko ikon aiki—ya ba maza da mata masu bangaskiya iko, har da Kiristoci na farko. (Zechariah 4:6; Ayukan Manzanni 4:31) Zai iya yin haka a gare mu, ko da za mu iya fuskantar tangarɗa mai wuya ko kalubale mu mutanen Jehovah.—Joel 2:28, 29.
10 Ka yi la’akari da misalin Laurel, wadda ta yi fama da shan-inna kuma ta zauna cikin na’ura na yin numfashi na shekaru 37.a Duk da yanayinta mai wuya sosai, ta bauta wa Allah da himma har mutuwarta. Cikin shekaru, albarka mai girma na Jehovah ta tarar da Laurel. Alal misali, ta taimaki wasu mutane 17 su kai ga cikakken sani na gaskiyar Littafi Mai Tsarki, ko da tana zama a cikin na’urarta awoyi 24 a rana! Yanayinta ya tuna mana kalmomin manzo Bulus: “Sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi ni ke.” (2 Korinthiyawa 12:10) Hakika, kowacce nasara da za mu yi a aikin wa’azin bishara tana zuwa ne, ba daga iyawa da kuma ƙarfinmu ba, amma daga taimakon Allah ta ruhu mai tsarki, wanda yake ba waɗanda suka ci gaba da saurara muryarsa.—Ishaya 40:29-31.
11. Waɗanne halaye ne ruhun Allah yake fito da shi cikin waɗanda suke yafa “sabon mutum”?
11 Idan mun saurari Allah cikin biyayya, ruhunsa zai fito da halaye na ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, da kuma kamewa cikinmu. (Galatiyawa 5:22, 23) Wannan “ɗiyan ruhu” sashen “sabon mutum” ne da Kiristoci suke yafawa maimakon halaye na zafin rai masu kama da na dabba da suke nunawa a dā. (Afisawa 4:20-24; Ishaya 11:6-9) Wannan ɗiya ta ƙauna tana da muhimmanci ƙwarai, “magamin kamalta.”—Kolossiyawa 3:14.
Ƙauna ta Kirista—Kyauta ce da Za a Daraja
12. Ta yaya Tabita da wasu Kiristoci na ƙarni na farko suka nuna ƙauna?
12 Ƙauna ta Kirista wata kyauta ce daga Jehovah—wadda muke daraja sosai. Ƙa’ida ce take yi mata ja-gora, ƙauna ce sosai da take jawo masu bi kusa kusa da juna fiye da dangantaka ta jini. (Yohanna 15:12, 13; 1 Bitrus 1:22) Alal misali, yi la’akari da Tabita, Kirista ce mai kirki na ƙarni na farko. ‘Cike ta ke da ayyukan nagarta da bayayya,’ musamman ga gwauraye mata cikin ikilisiya. (Ayukan Manzanni 9:36) Waɗannan mata ƙila suna da dangi, amma Tabita tana son ta yi abin da za ta iya ta taimake su kuma ta ƙarfafa su. (1 Yohanna 3:18) Lallai Tabita ta kafa misali mai kyau! Ƙaunar ’yan’uwa ta sa Biriska da Akila su ‘kasai da ransu’ saboda Bulus. Ƙauna kuma ta motsa Abafaras, Luka, Onisifurus, da wasu su taimaki manzon sa’ad da yake fursuna a Roma. (Romawa 16:3, 4; 2 Timothawus 1:16; 4:11; Filimon 23, 24) Hakika, irin wannan Kiristoci a yau suna da ‘ƙauna ga junansu,’ kyauta daga Allah da ke nuna su almajiran Yesu ne na gaskiya.—Yohanna 13:34, 35.
13. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ’yan’uwancinmu ta Kirista sosai?
13 Kana daraja ƙauna da ake nunawa cikin ikilisiya ta Kirista? Kana godiya don ’yan’uwancinmu na ruhaniya, da ya faɗaɗa zuwa dukan duniya? Wannan ma albarka ce da kyauta da ke kawo wadata daga bisa. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja su? Ta bauta wa Allah, ta yin furci a taron Kirista, ta nuna ƙauna da wasu ’ya’yan ruhun Allah.—Filibbiyawa 1:9; Ibraniyawa 10:24, 25.
‘Kyauta a Mutane’
14. Menene ake bukata daga Kirista idan zai yi hidima na dattijo ko kuma bawa mai hidima?
14 Maza Kirista da suke biɗan yi wa ’yan’uwansu masu bi hidima na dattawa ko bayi masu hidima suna da buri mai kyau. (1 Timothawus 3:1, 8) Don a cancanci samun waɗannan gatar, ɗan’uwa dole ya zama mutum mai ruhaniya, ya san Nassosi sosai kuma yana da himma a hidimar fage. (Ayukan Manzanni 18:24; 1 Timothawus 4:15; 2 Timothawus 4:5) Dole ya nuna tawali’u, filako, da haƙuri, domin albarkar Allah ba ta tarar da mutane masu girman kai, fahariya, da masu hassada. (Misalai 11:2; Ibraniyawa 6:15; 3 Yohanna 9, 10) Idan yana da aure, zai kasance shugaba mai kyau na iyali da ya isa ya yi mulkin gidansa da kyau. (1 Timothawus 3:4, 5, 12) Domin yana daraja abubuwa na ruhaniya, irin wannan mutum zai samu albarkar Jehovah.—Matta 6:19-21.
15, 16. Su wanene suka kasance ‘kyauta a mutane’? Ka ba da misalai.
15 Yayin da waɗanda suke hidima na dattawa cikin ikilisiya suka himmantu cikin wa’azin bishara, da kiwo, da kuma koyarwa, suna ba mu ƙaƙƙauran dalili na daraja irin wannan ‘kyauta a mutane.’ (Afisawa 4:8, 11) Waɗanda suka amfana daga hidimarsu ba koyaushe za su furta godiyarsu ba, amma Jehovah yana ganin dukan abin da dattawa masu aminci suke yi. Ba zai manta ƙauna da suka nuna don sunansa ta yi wa mutanensa hidima ba.—1 Timothawus 5:17; Ibraniyawa 6:10.
16 Ka yi la’akari da wani dattijo mai aiki tuƙuru da ya ziyarci wata yarinya Kirista da za a yi mata aiki a ƙwaƙwalwa. Wata abokiyar iyalin ta rubuta, “yana da kirki sosai, yana tallafawa, yana kula sosai.” “Ya nemi izini ya yi addu’a ga Jehovah tare da mu. Yayin da yake addu’a, baban [da ba Mashaidin Jehovah ba ne] ya yi amo, kuma hawaye ya zuba daga idanun duk wanda yake ɗakin asibitin. Addu’ar dattijon ta ƙauna ce, kuma ya yi kyau da Jehovah ya aiko shi a wannan lokacin!” Wata majiyyata Mashaidiya ta ce game da dattawa da suka yi mata ziyara: “Da suka zo wajen gadona a sashen kula da ciwo mai tsanani, na san cewa ko menene ya faru daga wannan lokaci zuwa gaba, zan iya jimrewa. Na kasance da ƙarfi da kuma lumana.” Akwai wanda zai iya sayan irin wannan damuwa na ƙauna? Sam! Kyauta ce daga Allah, da aka yi tanadinta ta ikilisiyar Kirista.—Ishaya 32:1, 2.
Kyautar Hidimar Fage
17, 18. (a) Wace kyautar hidima ce Jehovah ya ba dukan mutanensa? (b) Wane taimako Allah ya yi tanadinsa don mu cika hidimarmu?
17 Ba ɗaukaka da za a ba kowanne ɗan Adam da ta fi bauta wa Jehovah, Maɗaukaki. (Ishaya 43:10; 2 Korinthiyawa 4:7; 1 Bitrus 2:9) Saboda haka an buɗe wa kowa gatar sa hannu cikin hidima ga jama’a—yara da manya, maza da mata—da suke da muradi na gaske na bauta wa Allah. Kana amfani da wannan kyauta mai tamani? Wasu suna ƙin yin wa’azi domin suna ji ba su cancanta ba, amma ka tuna cewa Jehovah yana ba da ruhu mai tsarki ga waɗanda suke bauta masa, zai rufe kowanne kasawa da muke da shi.—Irmiya 1:6-8; 20:11.
18 Jehovah ya danƙa aikin wa’azin Mulki ga bayinsa masu tawali’u, ba ga mutane da suke fahariya da kuma dogara ga nasu iyawa ba. (1 Korinthiyawa 1:20, 26-29) Mutane masu tawali’u, masu filako sun san kasawarsu kuma sun dogara a kan taimakon Allah yayin da suke hidimar fage. Suna godiya kuma ga taimako na ruhaniya da yake tanadi ta “wakili mai-aminci.”—Luka 12:42-44; Misalai 22:4.
Iyali Mai Farin Ciki—Kyauta Mai Kyau
19. Waɗanne abubuwa suke kai wa ga nasara a renon yara?
19 Aure da rayuwar iyali mai farin ciki kyauta ce daga Allah. (Ruth 1:9; Afisawa 3:14, 15) Yara ma ‘gadō ne mai tamani daga wurin Ubangiji,’ suna kawo farin ciki wa iyaye da suka yi nasara wajen koya musu halaye na ibada. (Zabura 127:3) Idan kai mahaifi ne, ka ci gaba da saurarar muryar Jehovah ta koyar da ƙanananka bisa Kalmarsa. Waɗanda suka yi hakan, babu shakka za su samu goyon bayan Jehovah da albarka mai yawa.—Misalai 3:5, 6; 22:6; Afisawa 6:1-4.
20. Menene zai taimaki iyaye da yaransu suka ratse daga bauta ta gaskiya?
20 Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcen iyaye masu ibada, wataƙila wasu cikin yaransu sun zaɓi su ratse daga bauta ta gaskiya sa’ad da suka yi girma. (Farawa 26:34, 35) Wannan zai iya kawo damuwa ƙwarai ga iyaye. (Misalai 17:21, 25) Maimakon fid da rai, zai kasance da taimako su tuna da kwatancin Yesu na ɗa mubazzari. Ko da ɗan ya bar gida kuma ya bi mummunan tafarki, daga baya ya dawo gidan ubansa, wanda ya karɓe shi da farin ciki da ƙauna. (Luka 15:11-32) Ko da me zai faru, iyaye Kirista masu aminci za su tabbata da fahimin Jehovah, kulawarsa, da tokarawarsa.—Zabura 145:14.
21. Wa ya kamata mu saurara, kuma me ya sa?
21 Bari kowannenmu, ya tsai da abin da yake da muhimmanci da gaske a rayuwarsa. Muna biɗan yawan abin duniya, da zai kawo mana baƙin ciki da iyalanmu ne? Ko kuwa muna biɗan ‘kyakkyawar baiwa da cikakkiyar kyauta’ da ke zuwa daga “Uban haskoki.” (Yaƙub 1:17) Shaiɗan, “uban ƙarya,” yana son mu yi aiki tuƙuru don abin duniya kuma mu yi hasarar farin ciki da rai. (Yohanna 8:44; Luka 12:15) Amma Jehovah yana son abin da ya fi kyau dominmu. (Ishaya 48:17, 18) Saboda haka, bari mu ci gaba da saurarar Ubanmu na samaniya mai ƙauna kuma koyaushe mu ‘faranta zuciyarmu’ cikinsa. (Zabura 37:4) Idan mun biɗa irin wannan tafarki, kyautar Jehovah mai tamani da albarkarsa a yalwace za ta sa mu wadata—ba tare da wani baƙin ciki ba.
[Hasiya]
a Duba Awake!, na 22 ga Janairu, 1993 shafuffuka 18-21.
Ka Tuna?
• Ina ne za a samu farin ciki mafi girma?
• Waɗanne kyauta ne Jehovah ya ba mutanensa?
• Me ya sa hidimar fage kyauta ce?
• Menene iyaye za su iya yi don su samu albarkar Allah yayin da suke renon yaransu?
[Hoto a shafi na 14]
Kana nuna godiya don kyautar Allah ta rubucacciyar Kalmarsa?
[Hoto a shafi na 15]
Duk da yanayi mai wuya, Laurel Nisbet ta bauta wa Allah da himma
[Hotuna a shafi na 16]
Kamar Tabita, an san da Kiristoci na zamanin yau don ayyukansu na ƙauna
[Hoto a shafi na 17]
Dattawa Kirista suna damuwa da ’yan’uwa masu bi