Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 10/1 pp. 4-9
  • “Lokacinsa Bai Yi Ba Tukuna”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Lokacinsa Bai Yi Ba Tukuna”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Ƙuduri Aniya Ya Yi Nufin Allah
  • Himma don Gidan Jehovah
  • Koyarwa Mai Girma a Galili
  • Yin Wa’azi da Gaba Gaɗi a Yahudiya da Perea
  • Mu’ujiza da Babu Wanda Zai Iya Ƙaryatawa
  • “Lokaci Ya Yi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Dalilin da Ya Sa Yesu Bai Hanzarta Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yesu Ya Tayar da Li’azaru Daga Matattu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 10/1 pp. 4-9

“Lokacinsa Bai Yi Ba Tukuna”

“Ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.”—YAHAYA 7:30.

1. Waɗanne abubuwa biyu suka ja-goranci abubuwan da Yesu ya yi?

“YESU Kristi ya gaya wa manzanninsa, “Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi ya yi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.” (Matiyu 20:28) Ya gaya wa Bilatus Babunti gwamnar Roma: “Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya.” (Yahaya 18:37) Yesu ya san dalilin da ya sa zai mutu da kuma aikin da ya kamata ya yi kafin ya mutu. Ya kuma san iyakar lokaci da yake da shi ya yi aikinsa. Hidimarsa ta Almasihu a duniya za ta kasance shekara uku da rabi kawai. Ya soma lokacin da ya yi baftisma cikin Kogin Urdun (a shekara ta 29 A.Z.) farkon mako na 70 na alama da aka annabta, kuma ya ƙare da mutuwarsa a kan gungume da ya sha azaba a tsakiyar wannan makon (a shekara ta 33 A.Z.). (Daniyel 9:24-27; Matiyu 3:16, 17; 20:17-19) Saboda haka, abubuwa biyu ne na musamman suka ja-goranci abubuwan da Yesu ya yi lokacin da yake duniya: abin da ya sa ya zo duniya da kuma don kiyaye lokaci.

2. Yaya aka nuna Yesu Kristi cikin Lingila, kuma ta yaya ya nuna cewa ya san lokaci a aikinsa?

2 Labaran Lingila sun yi maganar Yesu Kristi cewa mutum ne da ya zagaya duk faɗin ƙasar Palasɗinu, ya yi bisharar Mulkin Allah ya yi ayyuka masu iko da yawa. Lokacin ayyukan Yesu na ƙwazo na hidima, an ce game da shi: “Lokacinsa bai yi ba tukuna.” Yesu kansa ya ce: “Lokacina bai yi sosai ba tukuna.” Kusan ƙarshen hidimarsa, ya yi amfani da furcin nan “lokaci ya yi.” (Yahaya 7:8, 30; 12:23) Da ya ke Yesu ya san sa’ar, ko kuma lokaci da aka ba shi na aiki, har da na mutuwarsa ta hadaya, lalle ya shafi abubuwan da ya faɗa da kuma waɗanda ya yi. Fahimta wannan zai sa mu gane mutumtakarsa da yadda yake tunani, ya taimake mu mu “bi hanyarsa” sosai.—1 Bitrus 2:21.

Ya Ƙuduri Aniya Ya Yi Nufin Allah

3, 4. (a) Menene ya faru a bikin aure a Kana? (b) Me ya sa Ɗan Allah ya ƙi shawarar Maryamu na cewa ya kamata ya yi wani abu game da ruwan anab da ya gaza, kuma me za mu iya koya daga wannan?

3 Shekara ta 29 A.Z. ce. Kwanaki kaɗan bayan Yesu ya zaɓi almajiransa na farko. Dukansu sun zo ƙauyen Kana a gunduman Galili don bikin aure. Uwar Yesu, Maryamu tana wajen ita ma. Ruwan anab ya gaza. A nuna masa cewa ya kamata ya yi wani abu, Maryamu ta gaya wa ɗanta: “Ba su da sauran ruwan inabi.” Amma Yesu ya amsa: “Mace, ina ruwana da ke? Sa’ata ba ta zo ba tukuna.”—Yahaya 1:35-51; Yohanna 2:1-4, Litafi Mai-Tsarki.

4 Amsar da Yesu ya bayar, “Mace, ina ruwana da ke?” tambaya ce ta dā da ke nuna ƙin shawara ko abin da aka faɗa. Me ya sa Yesu ya ƙi maganar Maryamu? To dai, shekararsa yanzu 30 ne. Makonni kaɗan da suka shige ne ya yi baftisma, aka shafa shi da ruhu mai tsarki, kuma Yahaya Mai Baftisma ya gabatar da shi, “Ɗan Rago na Allah, mai ɗauke zunubin duniya.” (Yahaya 1:29-34; Luka 3:21-23) Yanzu ja-gorarsa dole ta zo daga Maɗaukakin Iko wanda ya aike shi. (1 Korantiyawa 11:3) Ba wanda za a bari, ko ma wanda yake kusa da shi cikin iyali ya sa baki a aikin da Yesu ya zo ya yi a duniya. Lalle amsa da Yesu ya ba Maryamu ya nuna ƙudurinsa ya yi nufin Ubansa! Bari mu ma mu ƙuduri aniyar cika ‘wajibinmu’ ga Allah.—Mai Hadishi 12:13.

5. Wace mu’ujiza ce Yesu Kristi ya yi a Kana, menene sakamakon wannan a kan wasu?

5 Fahimtar abin da ɗanta yake nufi, Maryamu nan da nan ta koma gefe ta gaya wa barori: “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.” Yesu kuwa ya warware matsalar. Ya sa barorin su cika tulunan da ruwa, ya juya ruwan zuwa ruwan anab mafi kyau. Wannan ya zama farkon mu’ujiza ta Yesu, ta ba da alamar cewa ruhun Allah yana kansa. Lokacin da almajiransa sababbi suka ga wannan mu’ujiza, bangaskiyarsu ta ƙarfafa.—Yahaya 2:5-11.

Himma don Gidan Jehovah

6. Me ya sa Yesu ya yi fushi game da abin da ya gani a haikali a Urushalima, kuma menene ya yi?

6 Ba da daɗewa ba rani na shekara ta 30 A.Z. ya yi, Yesu da abokansa suna kan hanya zuwa Urushalima su yi Idin Ƙetarewa. Da suka isa wajen, almajiransa suka ga Shugabansu yana yin abin da wataƙila ba su taɓa ganinsa ya yi dā ba. Yahudawa ’yan kasuwa masu haɗama suna sayar da dabbobi da tsuntsaye don hadayu a haikalin. Suna sayarwa da tsada sosai wa Yahudawa masu aminci da suke bauta. Cike da fushi Yesu ya aikata. Ya tuka igiya ya yi bulala da ita ya kori masu sayar da dabbobin. Ya zubar da kwabbai na ’yan canjin kuɗi, ya kuma birkice teburansu. “Ku kwashe waɗannan daga nan!” ya gaya wa masu sayar da tantabarun. Da almajiran Yesu suka gan shi ya yi haka da himma, suka tuna da annabci game da Ɗan Allah: “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.” (Yahaya 2:13-17; Zabura 69:9) Mu ma dole mu tsare kanmu da himma kada sha’awa ta duniya ta lalata mana bauta.

7. (a) Menene ya motsa Nikodimu ya ziyarci Almasihu? (b) Me muka koya daga Yesu da ya yi wa wata Basamariya wa’azi?

7 Da yake Urushalima, Yesu ya yi mu’ujizoji na musamman, mutane da yawa sun ba da gaskiya gare shi. Har Nikodimu, wanda yake ɗan Majalisa ko kuma babban kotun Yahudawa, Yesu ya burge shi sai ya zo wajensa da dare ya ƙara koyo. Sa’an nan, Yesu da almajiransa sun zauna a “ƙasar Yahudiya” na misalin wata takwas, suna yin wa’azi da almajirantarwa. Amma da aka tsare Yahaya Mai Baftisma a fursuna suka bar Yahudiya suka koma Galili. Yayin da suke tafiya a ƙasar Samariya, Yesu ya yi amfani da zarafin, ya yi wa wata Basamariya wa’azi. Wannan ya sa ’yan Samariya da yawa suka zama masu bi. Bari mu ma mu kasance a shirye mu yi amfani da zarafi da muka samu mu yi magana game da Mulkin.—Yahaya 2:23; 3:1-22; 4:1-42; Markus 1:14.

Koyarwa Mai Girma a Galili

8. Wane aiki Yesu ya soma yi a Galili?

8 Kafin “lokaci” na mutuwar Yesu, yana da abubuwa da yawa da zai yi a hidimar Ubansa na samaniya. A Galili, Yesu ya soma hidima mai girma fiye da na Yahudiya da Urushalima. Ya zagaya “duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami’unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.” (Matiyu 4:23) Maganarsa da ke motsawa ita ce: “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato,” ya cika duk ƙasar da wa’azi. (Matiyu 4:17) Watanni kaɗan bayan haka, lokacin da almajiran Yahaya Mai Baftisma biyu suka zo su ji labari game da Yesu, ya gaya musu: “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara. Albarka ta tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”—Luka 7:22, 23.

9. Me ya sa taron suka zo wajen Kristi Yesu, kuma wane darasi za mu iya koya daga wannan?

9 ‘Labari mai kyau game da Yesu ya bazu a dukan kewayen ƙasar,’ taro masu girma suna zuwan wajensa—daga Galili, Dikafolis, Urushalima, Yahudiya, da kuma ƙetaren Kogin Urdun. (Luka 4:14, 15; Matiyu 4:24, 25) Sun zo wajensa ba domin warkarwarsa na mu’ujiza kawai ba amma domin koyarwarsa na ban mamaki. Saƙonsa yana da daɗi da ban ƙarfafa. (Matiyu 5:1–7:27) Kalmomin Yesu suna da daɗi da kuma ban murna. (Luka 4:22) Taron suka yi “mamakin koyarwa tasa,” gama yana magana daga Nassosi da hakikanci. (Matiyu 7:28, 29; Luka 4:32) Waye ne ba zai je wurin irin wannan mutumin ba? Bari mu ma mu koyi fasahar koyarwa domin mutane masu zukatan kirki su san gaskiya.

10. Me ya sa mutanen garin Nazarat suka yi ƙoƙari su kashe Yesu, amma me ya sa suka kasa?

10 Amma, ba duka da suka ji maganar Yesu ne suka amince da shi ba. Lokacin da ya soma hidimarsa, da yake koyarwa cikin majami’a na garinsu a Nazarat, an yi ƙoƙari a kashe shi. Ko da mutanen garinsu sun yi mamakin “maganarsa ta alheri,” suna so su ga mu’ujizoji. Amma maimakon ya yi ayyuka masu al’ajabi a wurin, Yesu ya fallasa son kai da rashin bangaskiyarsu. Cike da fushi, waɗanda suke cikin majami’a suka tashi, suka kama Yesu, suka kai shi goshin dutse don su jefo da shi ƙasa. Amma ya ratsa daga hannunsu kuma ya yi tafiyarsa. “Lokaci” na mutuwarsa bai yi ba tukuna.—Luka 4:16-30.

11. (a) Me ya sa wasu shugabanan addinai suka zo su saurari Yesu? (b) Me ya sa aka zargi Yesu da karya dokar Asabaci?

11 Shugabanan addinai—marubuta, Farisawa, Sadukiyawa da wasu—sau da yawa suna inda Yesu yake wa’azi. Yawancinsu suna wajen ba don su saurara su koya ba, amma don su nemi laifi kuma su kama shi. (Matiyu 12:38; 16:1; Luka 5:17; 6:1, 2) Alal misali, da ya ziyarci Urushalima don Idin Ƙetarewa na shekara ta 31 A.Z., Yesu ya warkar da mutum da yake ciwo shekara 38. Shugabanan addinan Yahudawa sun zargi Yesu cewa yana karya dokar Asabaci. Ya amsa: “Ubana na aiki har yanzu, ni ma ina yi.” Yanzu Yahudawa sun kama shi da alhakin saɓo don ya yi da’awar shi Ɗan Allah ne da ya kira Allah Uba. Suka nemi su kashe Yesu, amma shi da almajiransa suka bar Urushalima suka koma Galili. Hakanan ma, yana da kyau mu guje fuskantar ’yan hamayya yayin da muke ba da kuzarinmu a wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa.—Yahaya 5:1-18; 6:1.

12. Yaya yawan tafiye-tafiyen Yesu a ƙasar Galili?

12 Shekara guda da rabi na gaba ko fiye da haka, Yesu ya yi yawancin hidimarsa a Galili, yana zuwa Urushalima kaɗai don ya halarci idodi uku na Yahudawa da ake yi kowace shekara. Duka duka, ya yi tafiye-tafiye na wa’azi sau uku a Galili: na farkon da almajirai 4 sababbi, na biyu da manzanni 12, da kuma wanda ya faɗaɗa da ya aika da manzanni da ya koyar. Lalle an ba da shaida na ƙwarai ga gaskiya a Galili!—Matiyu 4:18-25; Luka 8:1-3; 9:1-6.

Yin Wa’azi da Gaba Gaɗi a Yahudiya da Perea

13, 14. (a) A wane lokaci ne Yahudawa suke nema su kama Yesu? (b) Me ya sa dogaran suka kasa kama Yesu?

13 Lokacin kaka ne na shekara ta 32 A.Z., “lokaci” na Yesu na gaba tukuna. Idin Bukkoki ya kusa. ’Yan’uwan Yesu suka aririce shi: “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya.” Suna so Yesu ya nuna ikonsa na mu’ujiza ga dukan waɗanda suka taru a wajen idin a Urushalima. Amma Yesu ya san haɗari ne. Sai ya gaya wa ’yan’uwansa: “Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.”—Yahaya 7:1-8.

14 Da ya ɗan yi jinkiri a Galili, Yesu ya tafi Urushalima “a ɓoye, ba a fili ba.” Hakika Yahudawan suna nemansa a idin, suna cewa: “Ina yake ne?” Wajen tsakiyar idin, Yesu ya shiga haikali kuma ya soma koyarwa da gaba gaɗi. Sun nemi su riƙe shi, wataƙila su sa shi a fursuna ko su kashe shi. Har ila, ba su yi nasara ba domin ‘lokacinsa bai yi ba tukuna.’ Mutane da yawa suka ba da gaskiya ga Yesu. Har ma dogarai da Farisawa suka aika su kama shi, sun dawo hannu banza, suna cewa: “Ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan.”—Yahaya 7:9-14, 30-46.

15. Me ya sa Yahudawa suka ɗebi duwatsu su jajjefe Yesu, amma wane aikin wa’azi ya soma?

15 Jayayya tsakanin Yesu da ’yan hamayya na Yahudiya ta ci gaba a lokacin idin, yayin da yake koyarwa game da Ubansa a haikali. A rana ta ƙarshe ta idin, da suka yi fushi don Yesu ya ce ya wanzu kafin ya zama mutum, Yahudawan suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Amma ya ɓuya, ya fita ba abin da ya same shi. (Yahaya 8:12-59) Da yake waje da Urushalima, Yesu ya soma aikin wa’azi sosai a Yahudiya. Ya zaɓi almajirai 70, bayan ya umarce su, ya aike su bibbiyu su yi aiki a ƙasar. Suna zuwa kowane wuri da birni inda Yesu da manzanninsa suke shirin zuwa.—Luka 10:1-24.

16. Daga wane haɗari Yesu ya tsere a lokacin Idin Buɗewa, wane aiki ya shagala ciki kuma?

16 A lokacin damina ta shekara ta 32 A.Z., “lokaci” na Yesu yana matsowa kurkusa. Ya zo Urushalima don Idin Buɗewa. Har ila,Yahudawa suna nema su kashe shi. Yayin da Yesu yake tafiya cikin ginshiƙan haikalin, suka gewaye shi. Suna zarginsa suna cewa ya yi saɓo, suka ɗebi duwatsu su kashe shi. Amma kamar yadda ya yi dā, Yesu ya tsere. Ba da daɗewa ba yana kan hanya yana koyarwa, yanzu daga birni zuwa birni da ƙauye zuwa ƙauye a ƙasar Perea, a hayin Urdun daga Yahudiya. Mutane da yawa suka ba da gaskiya a gare shi. Amma saƙo game da abokinsa Li’azaru ƙaunatacce ya sa ya koma Yahudiya.—Luka 13:33; Yahaya 10:20-42.

17. (a) Wane saƙo na gaggawa ne Yesu ya samu yayin da yake wa’azi a Perea? (b) Menene ya nuna cewa Yesu ya san dalilin ayyuka da dole zai yi da kuma lokacin abubuwa?

17 Saƙon gaggawan daga Marta da Maryamu ne ’yan’uwan Li’azaru, waɗanda suke da zama a Bait’anya na Yahudiya. “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya,” in ji ɗan saƙon. “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne,” Yesu ya amsa, amma “domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.” Don a cim ma wannan nufi, Yesu ya sake yin kwanaki biyu da gangan a inda yake. Sa’an nan ya ce wa almajiransa: “Mu koma ƙasar Yahudiya.” Don ba su da niyyar komawa, suka ce: “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa ke neman jifanka, za ka sake komawa can?” Amma Yesu ya san cewa sauran “yini,” ko kuma lokaci da Allah ya bayar don hidimarsa na duniya, gajere ne. Ya san daidai abin da dole zai yi da kuma dalilin haka.—Yahaya 11:1-10.

Mu’ujiza da Babu Wanda Zai Iya Ƙaryatawa

18. Lokacin da Yesu ya isa Bait’anya, menene yanayin wurin, kuma menene ya faru bayan ya isa?

18 A Bait’anya, Marta ce ta farko da ta sadu da Yesu, tana cewa: “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.” Maryamu da waɗanda suka zo gidansu suka biyo baya. Duka suna kuka. “Ina kuka sa shi?” Yesu ya tambaya. Suka amsa: “Ya Ubangiji, zo ka gani.” Lokacin da suka kai kabarin—kogo ne da wani dutse da aka rufe bakin da shi—Yesu ya ce: “Ku kawar da dutsen.” Ba ta gane abin da Yesu yake so ya yi ba, Marta ta ƙi: “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.” Amma Yesu ya tambaya: “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?”—Yahaya 11:17-40.

19. Me ya sa Yesu ya yi addu’a a fili kafin ya tashe Li’azaru?

19 Da aka cire dutsen da ya rufe bakin kabarin Li’azaru, Yesu ya ɗaga murya ya yi addu’a don mutanen don su sani cewa abin da yake son ya yi ta ikon Allah ne. Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce: “Li’azaru, fito!” Li’azaru ya fito da ƙafa da hannaye a ɗaure da likkafani, fuskarsa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce: “Ku kwance masa, ya tafi.”—Yahaya 11:41-44.

20. Yaya waɗanda suka ga Yesu ya ta da Li’azaru suka yi?

20 Da ganin wannan mu’ujizar, Yahudawa da yawa waɗanda suka zo su yi wa Marta da Maryamu ta’aziyya suka ba da gaskiya ga Yesu. Wasu suka tafi su gaya wa Farisawa abin da ya faru. Yaya suka yi? Nan da nan, da su da manyan firistoci suka yi taro na gaggawa na ’yan Majalisa. Da tsoro, suka ce: “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu’ujizai da yawa haka? In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama’armu.” Amma Babban Firist Kayafa ya ce musu: “Ku dai ba ku san kome ba. Ba kuwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama’a, da duk jama’a ta halaka.” Saboda haka, daga ranan sai suka ƙulla su kashe Yesu.—Yahaya 11:45-53.

21. Mu’ujizar ta da Li’azaru daga matattu farkon menene?

21 Don Yesu bai isa Bait’anya da sauri ba ne ya samu yin mu’ujiza da babu wanda zai iya ƙaryatawa. Da ikon Allah Yesu ya ta da mutum da ya mutu kwana huɗu. Har aka tilasta ’yan Majalisa masu girma su lura kuma su yi wa Mai Yin Mu’ujiza hukuncin kisa! Da haka mu’ujizar ta zama farkon lokacin da ke da muhimmanci a hidimar Yesu—canji daga sa’anda “lokacinsa bai yi ba tukuna” zuwa sa’anda “lokacinsa ya yi.”

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya Yesu ya nuna cewa ya san lokacin aikin da Allah ya ba shi?

• Me ya sa Yesu ya ƙi shawara da uwarsa ta bayar game da ruwan anab?

• Menene za mu iya koya daga yadda Yesu sau da yawa ya bi da ’yan hamayya?

• Me ya sa Yesu ya yi jinkiri game da rashin lafiyar Li’azaru?

[Hotuna a shafi na 6]

Yesu ya ba da kuzarinsa ga hakki da Allah ya ba shi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba