Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 4/1 pp. 3-4
  • Me Ka Sani Game Da Maita?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ka Sani Game Da Maita?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Makamantan Littattafai
  • Abin Da Ya Kamata Ka Sani Game da Maita
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Gaskiya Game da Sihiri, Bokanci, da Kuma Maita
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
  • Sihiri da Maita Ba Su da Kyau
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 4/1 pp. 3-4

Me Ka Sani Game Da Maita?

MAITA! Menene ya faɗo maka a zuciya?

Ga mutane da yawa, wani camfi ne ko kuma wasiƙar jaki, ba abin da za a ɗauka da muhimmanci ba. Ga mutanen, maita ƙagen zuciya ce—tsohuwar mayya ta ruhu da bargo ta ɓad da kamani, tana daɗa fikafikan jemagu cikin tukunya da take tafasa, take juya mutane su zama kwaɗi, tana tafiya a sama a kan hannun tsintsiya cikin dare tana dariyar mugunta.

Ga wasu kuma, maita ba abin wasa ba ce. Wasu ’yan bincike sun ce, fiye da rabin jama’an duniya sun gaskata cewa da akwai mayu kuma za su iya rinjayar rayukan wasu. Miliyoyi sun gaskata cewa maita mugunta ce, tana da haɗari, kuma abin tsoro ce ƙwarai. Alal misali, wani littafi game da addinin Afirka ya ce: “Gaskatawa da ayyukan mugun sihiri da kuma haɗarinsa, duba da kuma maita, sun yi katutu cikin rayuwar ’yan Afirka sosai . . . Mayu da masu duba aka fi tsana a yankinsu. Har wa yau, akwai wurare da kuma lokutta da mutane suke dūkansu har su kashe su.”

Amma dai, a ƙasashen Yammacin duniya an soma daraja maita. Littattafai, telibijin, da silima sun yi ƙoƙari sosai su rage tsoron maita. David Davis mai nazari game da nishaɗi ya lura: “Farat ɗaya, sai ga mayu suka zamana ƙanana ne kuma kyawawa, kyawawan gaske. Kamfani mai shirya fim Hollywood, yana ɗaukan bukatu da kuma yadda mutane suke ji. . . . Ta wurin mayar da mayu su bayyana kyawawa kuma abin da ake so, yadda mutane da yawa za su so, haɗe da mata da yara.” Hollywood sun san yadda za a mai da kome ya riƙa kawo kuɗi.

Wasu sun ce maita ta zama ɗarika da take ci gaba sosai a United States. A dukan ƙasashe da suka ci gaba, mutane da yawa da adadinsu yake ƙaruwa, da suka gaji da addini suna neman gamsuwa ta ruhaniya ta wurin maita iri dabam dabam. Hakika, maita iri-iri ne barkatai har mutane ba su jitu ba game da ma’anar kalmar da aka juya “mayya.” Duk da haka, waɗanda suke da’awar su mayu ne sau da yawa suna cewa su Wicca suke yi—wani ƙamus ya ba da ma’anar kalmar “addinin arna da ya samo asali daga yammancin Turai kafin zuwan Kiristanci wanda yake farfaɗowa a ƙarni na 20.” Saboda haka, da yawa suna kiran kansu arna ko kuma arnan zamani.

A cikin dukan tarihi, an tsane mayu, an tsananta masu, an gana masu azaba, har ma an kashe su. Abin da ya sa ke nan mayun zamani suna ƙoƙari su gyara sunansu. A wani bincike, an tambayi mayu da yawa wane saƙo suka fi so a gaya wa jama’a. Wata ’yar bincike Margot Adler, ta taƙaita amsarsu da cewa: “Mu ba miyagu ba ne. Ba ma bauta wa Iblis. Ba ma lahani ko kuma yaudarar mutane. Ba mu da ƙeta. Mu mutane ne kamar ku. Muna da iyalai, aiki, bege, da kuma abin da muke so. Mu ba mugun rukuni ba ne. Mu ba bokaye ba ne. . . . Bai kamata ku ji tsoron mu ba. . . . Mu kamar ku ne, fiye da yadda ku ke tunani.”

Mutane da yawa sun yarda da saƙon nan. Amma wannan yana nufin cewa babu dalilin damuwa ke nan ne game da aikin maita? Bari mu bincika wannan tambaya a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba